15

11K 1K 50
                                    

          *RUMFAR BAYI*
       (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 15
Wattpad @afreey101

                     ************

".....Bayan sati biyu...."

    "Juwairiya na zaune a cikin RUMFAR BAYI, lkcn karfe goma na dare ne amma a cikin rumfar se ka rantse da Allah ko shidda ta yamma  batayi ba.
dan kuwa sai a lkcn ne suke samun yin duk wata hidimar kan su,irin su wanki,kitso da sauran su...

    " Rabi ce ta kalleta tana jefa gyadar dake hannunta cikin bakinta..
Ya dai juwairiya kinyi shiru sai mgn nakeyi kin wani share ni...

Juwairiya tayi dan firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data tafi..
Kai Ina fa kinji rabi,kikace mai ma?
Rabi takai mata dukan wasa,ai dama nasan uwar shegu kikayi dani..

Laure ce ta karaso wajensu da yan kayanta a hannu..
   Juwairiya ta kalla tana narke murya,diyata ga ka'ron wankina..
Juwairiya ta zunboro baki,goggo laure duka duka fa sati biyu kenan danayi miki wanki..

Laure tace,ke yar gari yo ni wanki har nawa nayi miki da kina yar jaririyarki uhm!
Juwairiya ta juyar da kai,laure takai mata duka tace,ni kike juyawa ke'ya?yar fama kawai..

Hansai ce ta karaso wajen nasu, ta kamo hannun juwairiya, sannan ta kalli laure,babu ruwanki da diyarta ,wanki kuma bazatai ba,ai ba ajiyeta kikayi ba,muje ya'ta,laure ta rike baki,ni hansai?ni hansai?lallai ina nan zamana zaku dawo ai,kici gaba da shagwaba ta kema sai tace baki isa ba... ta ja tsaki ta juya tayi gaba..
Juwairiya da hansai suka shige daki suna mata dariya..

**************
"Da sassafe ranar alhamis juwairiya tayi shirin ta tsab sannan ta wuce wajen uwar dakin ta..

Tana shiga sashen zainaba ta same ta a zaune..
Ta gaishe ta tana kokarin shigewa ban dakine zainaba tayi saurin kiranta..
Juwairiya zo kiji..

Tazo ta duka har kasa tace gani..
Zainaba tace so nake kije min gidan waziri ki amso min wasikar da Mustapha ya aiko min da ita jiya,juwairiya tayi murmushi wato baki manta da ranar ta yau ba kenan?

Zainaba ta murmusa tana gyara zaman ta,ni kaina mamaki nakeyi wlh,kullum cikin addu'ar Allah ya kawo min wannan ranar nake,tunda yace min ze aiko min da lambar wayar su ta landline  gaba daya na zaku dana kira naji muryar sa..

Juwairiya ta saki baki cike da mamakin kalaman zainaba..
Zainaba ta taso ta rufe mata bakin tana dariya..
Juwairiya tayi murmushi sannan ta mike tace toh bara naje na dawo, da sauri ta juya ta fice.....

**************
"A nutse take tafiyar ta har ta fito babbar kofar masarautar,can ta hango su a tsaye tare da wani bawa (wato yarima da magaji kenan)
Da sauri ta dauke kanta sannan ta karawa tafiyar tata sauri...

   Magaji ne ya fara hango ta,ya kalli yarima yana sosa kashin kansa yace,ni fa wancan yarinyar se na riga gani kamar na santa a wani waje..

  Yarima ya kalli gefen da magaji ke nuna masa...
Can ya hango ta sai buga sauri takeyi kamar zata tashi sama..
"Ina zataje?"
Ya fada acikin zuciyasa...

Magaji ne ya dafa sa ganin hankalin sa baya tare dashi..
Muje mana kasan fa yau inna ta hada abinci damu kuma tace dole na taho dakai,rannan haka kayi min wayo naje nasha fada na..
Yarima yayi murmushi dan kuwa yana jin dadin abincin innar sosai,kai fa ka cika korafi dayawa,ko ranar ma ai umma ce ta tsare ni a sashen ta,magaji yace,naji din muje dai kada muyi rana....
  
"Juwairiya har tayi musu nisa sai ji tayi kawai  ta taka wani abu a kafarta..
da sauri ta dage kafar tana sakin ihun azabar da taji..
Waje ta samu ta zauna tana dago da kafar ta duba me ya tsake ta haka..
    Wata kwalba ce kuma ba kadan ba ta fasa mata kafar se jini ke fita..
Kuka sosai juwairiya keyi tana rike da kafarta ta...

Rumfar bayi Where stories live. Discover now