*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 13
Wattpad @afreey101********************
'kallon ta yayi Ya dan saki murmushi, kafin nan ya daure fuska yace,ke!...
Ta dago da kanta a tsorace amma bata kalli in da yake ba..'Yarima ya shafi sumar kansa Yace,ki biyoni.....sannan yayi cikin dakinsa..
A sanyeye jikinta na rawa ta bi bayansa a tsorace...Tana shiga dakin ta iske shi a tsaye yana goge jikinsa cike da nutsuwa..
Tayi kasa da kanta da sauri..
Yarima yace,har yanzu baki san aikin ki ba ne?A cikin sarkewar murya tace na sani?
Ya karasa gabanta ya mika mata dan karamin kyallen dake hannunsa..
Jiki na rawa ta amsa..Ya koma ya zauna yana juya mata bayansa,kawai be ce da ita komi ba..
'Juwairiya ta karasa ta tsaya a bayansa da kyallen a hannunta..
Se data ja lumfashi sannan ta runtse ido ta shiga goge masa jikinsa..
Tana gamawa taja gefe da saurinta..ta runtse idonta kirjinta na bugawa..'Yarima ya saki murmushi sannan ya mike ya karasa wajen kayansa ya dauki man shafawar sa .
yana shafa man yana kallon juwairiya dake rakube a gefe idanuwanta a kulle gam! haka kawai sai ya tsinci kansa a cikin wani irin nishadi.."Zo ki taimaka min ya fada kai tsaye yana mika mata alkyabbar dake hannunsa..
Ta bude ido taga ya gama shirin sa tsaf cikin wani farin yadi mai sauki ,ta karasa ta amsa alkyabbar sannan ta taimaka masa ya saka..
Maganar wani bawa sukaji daga can cikin falon...Yarima ya fito tana biye a bayansa..
Abincine kala kala aka kawo masa..
Bawan ya du'ka har kasa yace,ranka shi dade sun ce na baka hakuri akan kayi hakuri da wannan ya nuna abincin daya shigo dashi,saboda dare yayi ne basu samu damar gaba tar maka da abinci masu yawa ba..Yarima yace banu komi zaka iya tafiya..
Juwairiya ta dan tabe baki duk wannan kayan dadin shine harda wani bashi hakuri..tab lallai ta yarda yarima babban mutum ne..'Yarima ya kalleta yaga idanuwanta kyam akan abincin..
Zama yayi kawai yana lankwashe kafafunsa..
Juwairiya ta dan hada karfin da gareta tace..
Ranka shi dade zan iya tafiya?Yarima ya girgiza kai...
Juwairiya tace na shiga uku wai meke damun mutumin nan ne?(a cikin zuciyarta)..Yarima ya lumshe ido ya bude,kafin yace,zo ki bani abincin..
Juwairiya a sanyaye ta duka ta zuba masa abincin a cikin plate sannan ta ajiye a gabansa tana kokarin mikewa yace..A ba'ki zaki bani...dan na gaji dayawa..
Juwairiya gabanta ya fadi,...
'A baki'?ta fada a tunaninta cikin zuciyarta tayi mgnr se ji tayi yace..
Da a hanci zaki bani?
Ta girgiza kai,ai ko zainaba bata zama a bata abinci a baki..
Tsokali ta dauka ta debo abincin kadan a ciki sannan ta mika masa..Yarima na kallon fuskarta ya bude baki ta saka masa abincin aciki..
Cike da takura take basa abincin har yayi mata nuni da ya koshi..
Dadi taji sosai dan ta san yanzu dolene ya sallameta tunda dai ba ita zatayi masa barcin ba..Ji tayi kawai yace..
'Saura ke ki ci'
Ta dago da mamaki tace,Ni?
Yarima fuska ya daure yace ban sani ba..Juwairiya ta rasa yarda zatayi wai "saura ke ki ci"kodai kunnenta ne yaji mata badai dai ba..?
Yarima ya mike kawai yace,idan kin gama zaki iya tafiya...
Yana shiga daki juwairiya ta sake kallon delicacies din dake wajen ko kwatan abincin yarima bai ci ba..
Gyara zamanta tayi a wajen tana fadin..'Gwara naci dan kada ma ayi asarar abincin nan da mutane dayawa basu da halin kamar shi...
Cin'yar kaza ta dauka tana yashe lebenta,se yau Allah yayi zata dandana irin wadan nan abincin oh"dama su ummanta na nan suci tare..

YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid