*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 42
Wattpad @afreey101_"Fans please ina neman addu'ar ku,October dinnan zan fara exams dina inshaAllah,shi yasa zaku ga ina yanke lbrn dan na gama muku shi a cikin lkc na fara karatun jarabawata.._
_Thanks for all your love.._
_Ina Yin'ku sosai😘_********************
"Surayya abun duniya ya taro ya fara yi mata yawa..
Girman kai gaba daya ya hana ta zuwa neman gafara a wajen juwairiya..Gashi kuma yanzu jalal ya dauke mata kafa daga dukkan al'amuran ta ko sashen sa ya daina gayyatar ta..
tun ranar dayayi kiranta tayi masa alkawarin zata je ta nemi gafarar ta har yanzu bai waiwaye ta ba
Sai dai taji yaje wajen khadija da amaryarsa..Yau dai fada tayi wa zuciyarta sosai ganin bata da wata mafita..
ga kuma wannan ciwon cikin daya dawo mata kullum dare sai tayi fama dashi tun lkcn da tasha maganin malamin nan a kwanakin baya ta kasa ganewa jikinta gaba daya..
Ga mafarkai barkatai da takeyi,duniya dai tayi mata zafi sosai,taja lumfashi..
Gara naje na nemi gafarar ta wata kila na samu sausaucin abunda nake ji..***************
"Abun mamaki juwairiya na zaune a sashenta dasu hansai sai ga surayya ta shigo da sabowar baiwar ta...
Ga babban mamakin su juwairiya sai gani sukayi surayya ta dage sosai wajen neman gafarar ta..Tayu mamaki sosai amma sai Tace.. babu komai ita ta yafe mata,Allah kansa ma muna masa laifi ya yafe mana balle kuma dan adam?..
Ita dama bata rike ta ba....
Surayya taji dadi sosai,dan gaba daya ma sai ji tayi juwairiyar ta burge ta bata dauki duniyar a bakin komai ba ita kuwa sbd shaidan ya tafi da tunaninta tayi ta wulakanta ta a baya oh?duniya kenan!..
Ai kuwa tun daga ranar sai surayya taji nauyin dake zuciyarta ya ragu sosai,sai dai wannan ciwon ciki da zame mata tilas kullum dare da kyal take samun barci...
Ta rasa mafita gashi yakumbo kanta bata kasar balle ta saka ta ta nemo mata magani..Bayan wata uku..
******************
A cikin watannin nan da suka gabata ba karami shakuwa da zaman lafiya bane ya shiga a tsakanin matan sarki jalal ba..Abun mamaki Yanzu kam surayya sai shige wa juwairiya takeyi dan kafin kaganta a sashen khadija toh zaka kanta a sashen juwairiya sau ba adadi duk wani shawara wajenta take zuwa..
sai dai har lkcn ta kasa fadawa kowa abunda take ciki..
duk ta rame ko jalal ya tambaye ta sai tace masa kawai babu komai..kada ya damu..
shi kam ma abun har ya fara basa tsoro dan yanzu ya lura gaba daya surayya bata yarda ta kwana a sashen sa..
Ba kamar da ba da take matsawa sosai sai ya kwana da ita..."Khadija kam ta maida juwairiya tamkar kawarta dan har dakinta inna (mahaifiyarta)tazo tayi mata kaca kaca akan ta samu lbr a gidansu wai goggo na kawo wa diyarta magunguna....
ba karamin tashin hankali ta shiga ba shine tazo da kanta tayi mata fada mai ratsa jiki..
Sannan ta bata shawarwari wadan da zasu amfane ta a zaman auren ta..Tun daga lkcn khadija ta saduda sosai ta mayar da juwairiya kawarta..
sai su ringa hadewa a can sashen fulani suna shan firar su dasu zainaba..."Kamar kullum magaji ne ya shigo cikin masarautar dan amsa kiran sarki jalal...
yana tafe ne yana mamakin neman gaggawar da Amale keyi masa..
Caraf ya hango ta tana tafiya da baiwarta a baya amma da gani hankalin ta gaba daya baya jikin ta..
ganin yarda tazo har ta wuce sa bata ko ma lura dashi ba..Juyawa yayi yabi bayanta da sauri yasha gabanta..
Duk da haka ko ganinsa ma batayi ba har sai data ci karo da shi..Bum!A tsorace sosai tayi baya zata fadi kasa..
Yayi saurin taro ta ya rike ta gam yana karewa kwayar idonta kallo..
Wani irin abune yaji yana yawo a cikin cikin sa..

YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid