*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 19
Wattpad @afreey101**********
"An sha shagali sosai har kusan tara na dare kafin taron ya watse..
Sarki jalal ne ya shiga babban turakar sa (sashen sa) inda aka canzawa tsari daga tsarin na mahaifinsa wato tsohon sarki kenan.." Jakadiya ce ta shigo da kuyangi har cikin makeken dakinsa,ta fada musu yarda zasu hada mishi ruwan wanka da sauran hidimarsa,kuyangi biyu ne suka shige cikin dakin suka gyara shi tsab dan kwanar amarya..
A can wajen khadija amarya kuwa,bayan ta dawo daga taro a gajiyenta, gimbiya kilishi ce ta aika mata da hansai da kuma sabowar baiwarta wato rabi, nan hansai ta shiga nunawa rabi yarda zata kula da uwar dakin nata,rabi sai washe baki akeyi tana murnar samun karin girman da tayi..
An gama shirya khadija tsab cikin kaya na gani na fada.
suna shirin fitane dan zuwa kai ta can turakar sarki jalal sai ga surayya tare da umayma sun shigo cikin sashen..Wajen zama rabi ta nuna musu,sannan ta dawo kusa da khadija dake ta jin haushin tsaida su da akayi ta zauna..
Surayya ce tace, su amarya an sha kamshi,dama nazo ne dan nima na bada tawa gudunmawar tunda dai ban samu lokacin bayar wa ba ko..Umayma ce ta ajiye tiren dake hannunta wanda dashi ne suka shigo.
surayya tadan yi murmushi kafin nan ta sake cewa,
wani tsumi ne dama da aka kawo min shi daga kasar Cameroon, nayi amfani dashi kuma na yaba sosai,tunda dai ba karamin rikita sarkina yayi ba a lkcn,ta karashe mgnr cike da kissa..Khadija taji wani abu ya tsaya mata a wuya,sarkinta?ya rikice?lallai ma wannan matar..
Tadan dago kai tana murmushin yake kafin nan tace a takaice ,toh nagode..ta shiga kokarin mikewa..Umayma ce tayi saurin fadin,ah ah gimbiya khadija ai kamata yayi ki dan nuna karamci,ta shiga zuba tsumin a kofi..
Surayya ta amsa kofin ta mikawa khadija,kidan sha ko kadan ne na tabbatar miki gobe se kin gode mini..
Khadija tadan kalli rabi,rabi tayi mana alama da kada tasha,khadija tadan tabe baki..Jakadiya ce ta rangwada sallama tana sake nanata musu sarki jalal na jiran amaryar sa..
Khadija data ka'gu sosai data tafi wajen rabin ranta...
cikin sauri da jawar jiki ta amsa kofin ta kafa kai ta shanye shi tass tana nunawa su surayya cikin kofin (irin am done zaku iya tafiya).Surayya tayi murmushin murna,yauwa ko kefa kinga nima se naji dadi ai,rabi ce ta kamo hannun khadija sukayi gaba abunsu..
Umayma da surayya suka kalli juna suna murmushin mugunta cike da gamsuwa..**************
"A wajen Jalal kuwa yayi wankansa ya saka kaya masu saukin gaske,se kamshi yakeyi ..Yana zaune a saman darduma ta alfarma yaji sallamar khadija daga can falo..
Bai motsa daga inda yake ba har ta shigo dakin cike da yangarta ta sauke idanunta akan sa..
Wani irin kyau da kwarjini yayi mata har bata san lkcn da ta saki murmushi ba tana wani kafe shi da ido..'Idan kin gama karemin kallon se kije ki kwanta"
Khadija tadan waro ido kunya duk ta lullube ta.
Jalal ya mike cike da kasaitarsa ya juya mata baya..sai ji kawai yayi an rungumo shi ta bayan..Khadija ta kwantar da kanta a bayansa tana fadin..
"Haba ya jalal meyasa kake bawa zuciyata wahala ne?kasan fa yarda na damu dakai tun muna yara...amma se ka ringa wani share ni..ta karashe mgnr a shagwabe..Yarima yaji jikinsa yayi sanyi,idan har yace bai san khadija ta mutu a kansa ba toh karya yakeyi wa kansa..
Lumfashi yaja sannan ya kamo hannunta ya maido da ita gabansa yana kallon fuskarta har kwalla sun fara cikowa a cikin idanunta..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid