12

10.1K 948 29
                                    

         *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 12
Wattpad @afreey101

*****************

"Sunyi tafiya mai nesan gaske kafin suka iso Daular borno..
   "Yarima dake zaune a bayan mota yace wa bawan dake tu'ka su,idan muka shiga  borno sai mu a tsaya a  masarautar su mu kwana zuwa gobe sai mu karasa chadin..

'Magaji ne ya gyara zamansa yace,ai mun shigo Daular borno tun dazu yarima tunanin me kake ne haka?ba dai har ka fara kewar surayyar taka ba..yayi mgnr cike da zolaya..
Yarima yaja tsaki kawai yana kallon window..

'A can cikin bus kuwa su juwairiya ne,tunda aka shigo kasar borno ta maida hankalinta akan kallon window tana karewa tsarin garin kallo...har taga sun shiga wata katowar kofa sai gasu acikin masarautar ta borno..

'Ido ta ware tana kallon mutane dake ta zurga'zurgar su duk da dare ne amma harkar gabansu kawai sukeyi..
Rabi ce ta dan tabo ta ganin motar su ta tsaya,muje juwairiya....

'A sanyaye ta fito daga motar jikinta duk a gajiye tana rungume da kullin kayanta..
Daidai lkcn ne shima yarima ya fito yana wani shan kamshin sa.
  
Har fadar mai martaba aka kai su suka kwashi gaisuwa sannan aka saka wasu matah su kaisu masaukin da zasu kwana zuwa goben..

Masaukinsu ya hadu sosai dan komai an wadata su,tunda Takawa (mahaifin jalal)ya riga ya turawa sarkin borkon sakon zuwan su.
daki daya aka ware wa su juwairiya ,sai daki daya na yarima, daya kuma na mazan bayi sai dakin magaji...

Suna shiga kowaccen su ta kwanta cike da gajiya,basu dade da shigowa ba sai ga sakon magaji ya iso musu daga wajen wani bawa,wai a cikin su ukun wata taje ta hadawa yarima ruwan wankan sa..

    'Rabi ta marairaice ta kalli juwairiya,waye zai je a cikin ku dan ni kam wlh bazan iya zuwa ba jikina ciwo yakeyi sosai..

"Zabba'u itace karama a cikinsu,dan haka tace,ni wlh tsoro nakeji kuma ni ban ma iya hada ruwan wankan ba  tunda ni a madafa nake dama..

  "Juwairiya tadan hararesu,kawai ku fito fili kuce ni naje mana..
Dariya sukayi sannan a tare sukace..
Dan Allah juwairiya ke kije..

"Juwairiya zatayi mgn bawan dake waje ya sake cewa, baku ji bane? !ba a barin yarima yana jira,juwairiya ta zunboru baki sannan ta mike tana sake gyara kayan dake jikinta kafin ta fito..

   Bawan na gaba tana binsa a baya har suka shiga bangaren su yarima..
  Magaji ne kawai a falon zaune..
Yabi juwairiya da kallo, shiga ga dakin can ya nuna mata wata kofa..
Toh tace kawai jiki a sanyaye ta shiga kofar..

   Yarima ta hango a zaune kan dago ya jingina bayansa a kan gadon ya lumshe idonsa..
Ta rasa me zatace masa, wace irin gaisuwa zatayi masa..

Dan haka se ta lallaba zata shige kofar data ke tunanin ta ban dakin ce..

     'Haka aka koyar dake!!!?

Muryar yarima ta da'ki dodon kunnenta..
Da sauri ta juyo ta hango shi yana kallonta fuska a daure..

Dawowa tayi baya tace,afuwa zanka shi dade na dauka barci kake ne...

Ya yamutse fuska yayi sannan ya maida idonsa ya lumshe..
  Juwairiya ta shiga toilet din ta hada ruwan wankan sannan ta fito ta tarar dashi a tsaye..tace..

Na gama...ta sunkuyar dakai..
Tsaki ya danyi haushin kansa kawai yakeji daya za'bi ta a tafiyar....ya kasa gane meyasa wannan yarinyar take shiga rayuwar sa..

    tsaki ya dan'yi kafin yace,Zaki iya tafiya,ya mike a natse yana cire alkyabbar dake jikinsa..
Toh tace kawai ta fice..

Tana fitowa falon ta sauke wata ajiyar zuciya mai nauyi..

Rumfar bayi Where stories live. Discover now