*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 17
Wattpad @afreey101***************
"Gidan waziri suka shiga,mutane har sun fara tarowa kasancewar yau ne sa lallen khadija..
A dakinta suka tarar da ita tasha gyaran jiki se fitar da kamshi takeyi...Tana ganin zainaba ta fada jikinta tana murna sosai..
Zainaba tace,kai duk murnar auren ya yariman ne haka?Khadija ta dago tana murmush sosai, kema ai kin sani,mafarkin da na dade inayi gashi har ya kusa zamowa gsky.
na kusa mallakar rabin raina,ta kamo hannun zainaba, zainaba gobe yarima zai zama mijina,ina tunani a duk duniyar nan babu wanda tafi ni farin ciki...Surutai kawai khadija ke sakar musu cike da tsantsar murnar ta.
juwairiya kam gaba daya taji jikinta yayi sanyi,ta rasa dalilin da yasa duk lkcn da khadija zata ambaci sunan yarima toh sai zuciyarta ta buga..Ganin zaman na neman gagararta ne sai ta mike kawai ta fito waje..
Mata ta iske cike da tsakar gidan ana ta faman girke girke..
Ji tayi kamar lumfashin ta baya fita sosai..Da gudu ta bar cikin gidan ta karasa can bayan gidan kusa da ra'fi mai gudana da ruwa...
Sauke ajiyar zuciya takeyi sosai,wai meke faruwa da ita ne,me yasa take mafarkin yarima? Meye hadinta dashi?yafi karfin ta me yasa zuciyarta bazata bar tunaninsa ba..!
Zama tayi a wajen saman grass, jin iska na kadata sai lumshe ido takeyi...***************
"Ango kasha kamshi!Magaji ya fada yana washe baki..
Hamza yace,ai yaya kai kam dan gata ne wlh mata biyu cikin wata biyu kacal..Turaki yayi dariya,yarima ya banka musu harara,sannan ya amshe alkyabbar sa dake hannun magaji yana tayashi shiryawa..
Hamza yace,gsky wannan sa lallen ya kamata mai martaba ya bari mu dan cashe ko ya kuka gani?..Turaki ya kai masa duka,kai fa hamza dan duniya ne wlh,a ina ka taba ganin maza sunyi rawa a sa lallen?
Hamza ya mike yana fadin,ba sai a fara a kan mu ba,ni dai Allah ya gani gobe A na'din sarautar ya yarima se na cashe abuna,kasan fa har wannan mawakin na dauko dake can kasar nijar..Magaji yace,kai hamza akwai son bidi'a,duk suka saka dariya..
Daga waje ne aka shiga sanar da shigowar da surayya..Duk suka kalli juna suna murmushi, kafin nan suka mike,magaji yace,a lallaba mata ita don Allah...
Yarima ya tabe baki yana basarwa..
Suna fita ta shigo cikin adonta sai baza kamshi takeyi...
Kallon juna sukayi,yarima ne ya fara dauke idonsa yana kokarin saka hular sa..Da sauri taje ta amshe hular sannan tayi murmushin yake tace..
Wannan aikina ne ...
Yarima yace,sai yau kika sani kenan?
Surayya ta turo baki,toh kana kiran na ne na saka maka?Ya wani basar yana fadin,naga kinsha shiri sai ina?
Surayya ta dan harara shi,ina fa?gidan amaryar zamuje dasu umma..
Yarima ya jinjinawa makircin surayya,sannan yayi murmushi ya fice abunsa ya bar nan cike da takaici..Surayya ta jefar da yar jakar dake hannunta, cike da fusata tace, dole ne nasan abunyi,ya za'ayi ace kamar ni yarima yake wulakantawa son ransa,sannan hakan bai isa ba ma ko shekara banyi da aurensa ba zasu sake aura masa wata?
Ta tuna zancensu da yakumbo,lkcn data fada mata mgnr juwairiya..
_ ''Miye abun tashin hankalinki akan wata banzar baiwa can ke da za'ayiwa kishiya cikin kwanan nan,idan har kinaso ki siye zuciyar yarima toh ki tabbatar kece kika fara haifa masa Da wanda ze ga'je shi a mulki"_"Surayya ta ciji lebenta na kasa,taya zata samu damar wani haihuwa bacin sai yarima yaga dama yake kwana da ita,dole ne ta san abunyi,dan ta lura gimbiya kilishi ma zata iya juya mata baya indai har wannan yarinyar ta shigo kuma ta rika ta haihuwar...
**************
"An gama dukkan shirye shirye na sa lallen khadija..Surayya , Fulani diyya ,gimbiya kilishi tare da sauran matar sarki ne suka zo gidan, tare da su jakadiya,du'bu da kuma sauran bayi dayawa dan kawo musu lallen amarya..
"Bayan an zauna ne sai ga tawagar su yarima tare da abokansa da kuma yan uwa..
Nan aka tanadar wa amarya da ango wajen zamansu kamar yadda al'adar tasu take,sannan aka fara gudanar da event din,su jakadiya ansha gu'da,hansai sai raba idanu take ko zata dan hango diyarta amma bata ganta ba. ko ina ta shige oho?.Zainaba dake rike da hannun khadija ta shiga neman juwairiya dan ta dauko mata wani sako a dakin khadija data manta.
"A tsakiyar su khadija da yarima dake zaune taje tace a hankali, khadija kinga bari naje na dan duba juwairiya tun fa dazun ban sa ta a idona ba ko gida ta koma oho?amma nasan ma da kyal ne ta koma can bata nemi izini na ba..
Khadija tadan tabe baki,toh shikenan amma kada ki dade dan Allah,zainaba tayi murmushi kada ki damu yanzu zan dubo ta na dawo...
Duk wannan zancen nasu yarima yanaji..
Ina take?ya tambaya a cikin zuciyarsa sai lkcn ne ya lura da bata a wajen,hakanan yaji yana son yasan ko tana lafiya,zuciyarsa ke ta azazzalar sa...Kallon turaki yayi dake kusa dashi..
"ina zuwa"
bai bari ya amsa masa ba kawai yayi gaba abunsa...Gimbiya kilishi na lura da tashin da yayi daga wajen,ina zai je?ta tamabayi hansai dake gefenta,hansai tace,gimbiyata wata kila ban daki zai shiga,kilishi ta jinjina kai cike da gamsuwa..
Shi kam yarima fita yayi yana ta dube dube,lkcn har duhun yamma ya farayi...
**************
Juwairiya kuwa barci ne ya dauke ta a wajen dan dama bata samu barcin kirki ba a daren jiya...Yarima na zagayawa bayan gidan ya karasa gaban rafin yana sauke lumfashi....
me yasa zai damu kansa sabida wata baiwa can?Yaja tsaki yana shirin juyawa sai kawai can ya hango ta...ta jingina a jikin wani bishiya tana ta sharar barci a takure..
Karasawa yayi wajen ya kura mata ido,zuciyarshi yaji wasai ganin tana lfy,amma wannan barcin fa?Bakinta yaga yana motsi...
Ya duko sosai ahankali kusa da fuskarta dan son jin me take fada...Ya..ri...ma.....!
Yaji ta furta....
Ware ido yayi cike da mamakin jin sunansa a bakinta..Murmushi ya saki yana kare mata kallo,tabon fuskarta ya kalla yana son yaji dalilin da yasa take yin sa?
Bai ankara ba sai gani yayi ta bude idonta tangaram a kansa..A tsorace take kallon sa...
Shi din ma yadan tsorata da ganin ta bude idonta,yana kokarin gyara tsayuwarsa kawai yayi loosing balance dinsa sai tim!
Ya fadowa juwairiya ajiki suka zube a kasa su duka..Wani irin kamshi ne ya mamaye hancin ta,taja lumfashi mai karfi,nauyin yarima ne yasa tayi saurin dago da idonta.
Hada ido sukayi,ta hada duka karfinta ta sa hannu ta ture shi gefe...
Yarima ya lumshe ido yana jin wani irin yanayi yana ratsa shi..
Juwairiya tayi saurin mikewa tana kallonsa..
Sai kuma Da sauri koma ta zube a kasa tunawa da tayi waye ta ture yanzun nan,yarima jalal ne fa....Allah ya huci zuciyar ka,kayi min afuwa...
Yarima ya mike yana kakkabe kayan dake jikinsa...
"Ni kika ture a kasa?
Juwairiya a tsorace tace,kayi hakuri ranka shi dade, kayi min rai...Yarima yadan murmusa,
me kikeyi a nan?
Juwairiya a zuciyarta tace,kai ya kamata na tambaya ai,me kakeyi a nan bayan ana can ana sa lallen amaryar ka....!kallon da yake yi mata ne yasa ta fuskanci katobarar da tayi,wato mgnr zucin da takeyi ta fito fili kenan?wayyo Allah ta shiga uku..
Da sauri tasa hannu ta rufe bakinta,gani tayi ya tako zuwa gabanta,kirjinta na ta bugawa ...jitai yace,
"Kina son sanin meyasa na baro amarya ta nazo nan?
Juwairiya ta waro ido tana girgiza kai..
Murmushi yayi,juwairiya ta kura masa ido kyaun sa na kashe ta..
Bai sake cewa komai ba yabi ta gefen ta ya wuce abunsa......"Thanks fans,i can see that some of you r doing well with the GIVE AWAY"
Please
Vote
And
Share

VOCÊ ESTÁ LENDO
Rumfar bayi
Ficção HistóricaA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid