*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 35
Wattpad @afreey101*sabowar rayuwa*
*******************
"Sarki abu-turab ne da kanshi ya tara dukkan bayin dake cikin masarautar sa..
Gimbiya amina ya saka ta zabarwa juwairiya sababbin bayin da zasuyi mata hidima daga wannan ranar ta yau..Cike da kwarewa amina ta shiga zabar mata su..
Abu-turab ya jinjina kai yana yabawa zabin matar tasa dan kuwa duk yan matane ta zabo kusam sa'annin juwairiya din..yasan diyarsa zataji dadin zama dasu..Ya kalli wani dogari yace dashi,ka dauki bayi kuje can sabon sashen dake kusa dana amina a gyarawa juwairiya shi ta zauna a ciki..
Amina ta karaso wajen mijinta tana mai farin cikin ganin sa a cikin wannan yanayin..
Abu-turab ya kamo hannunta suka shige cikin sashen sa..
Ya kalleta yace..
Na gode sosai da taya ni farin cikin da kikeyi inaso ki tayani rikon juwairiya..
Amina ta girgiza kai..
Ka manta diyar zarah'u kamar a matsayin diyata take nima?
Gashi kafi kowa sanin yarda yake kwadayin samun diya mace nima ko?Abu-turab yayi dariya..hakane gimbiyata..gashi kuma kin samu..
Sannan Idan su yarimaADO da Abdullahi sun dawo gobe inaso ki hada su yar uwar su..Amina tace,ai wannan ya zama dole..mai martaba
Abu-turab yace,yauwa inaso kuma ki saka jakadiya ta zauna ta koyar da juwairiya Al'adu da halayen zama a gidan sarauta,tunda dai kin ga a inda tayi rayuwar ta a baya..Amina ta jinjinar dakai,hakane kada ka damu inshaAllah zakayi mamakin juwairiya,abu-turab yace nagode sosai gimbiyata...
"Amina na fita daga sashen abu-turab ta kira jakadiya da hanne (sabowar baiwar juwairiya)ta basu umarni akan su fara koyar da juwairiya da'bi'u da halayen jinin sarauta..
Jakadiya tace,kada ki damu ranki ya dade kamar anyi an gama ne wannan..Juwairiya na zaune a cikin dakin amina,hanne ta shigo cike da girgimawa tace..
Sannu da hutawa uwar dakina..
Juwairiya taji abun wani banbara kwai..
Hanne ta sake fadin..
Ki fito gimbiya amina nason mgn dake..
Juwairiya ta mike ta filo falon..
Amina ta kalleta cike da kulawa..tace
Juwairiya zo nan kiji..ta nuna mata kusa da kilisar da take zaune..
Juwairiya tayi yarda tace..wato ta zauna a kusa da ita..
Amina tace,inaso yanzu ki bi su jakadiya zuwa sabon sashen ki dan su koyar dake da'bi'u da al'adun mu na gidan sarauta kinji?
Juwairiya tayi murmushi ta gyada kai..
Amina tace yauwa diyata tashi kuje.."Ba karamin haduwa sashen na juwairiya yayi ba,dan a ganin tama yafi sashen zainaba nesa ba kusa ba..
Komai yaji zam zam..Jakadiya da hanne ne suka shiga koyar da ita duk abunda suka san zai amfane rayuwarta a cikin masarautar dama waje... a matsayinta ta sarauniya juwairiyya kuma diyar sarki abu-turab..
Tunda ga yarda ake zaman kilisa..
Yarda ake tafiya..
Yarda ake cin abinci..
Yarda yake amsa gaisuwar bayi..
Yarda yake bada umarni..
Yarda ake jan aji..
Yarda ake kasaita..
Da dai sauran su.........
Juwairiya ta cika da mamaki,wato komai zakayi a gidan sarauta sai an koyardake kenan?Sai ta tuna da halayen YARIMA kau sarki jalal..
A take ta saki murmushi mai kayatarwa..
Hanne ce tace da ita..
Kinfi kyau idan kina murmushi haka uwar dakina..
Juwairiya ta kalleta,itama fa a baya tayi irin wannan rayuwar..
A sanyeye tace da ita Nagode hanne.."Acikin kwana biyu kacal sai da jakadiya ta tabbatar da juwairiya duk ta koyi abunda suka koyar da ita..
Tabbas kuma an samu canji nesa ba kusa ba,dan kuwa ita kanta juwairiya har mamakin kanta takeyi..
Komai nata ya canza a cikin dan kankanin lkc...
Gashi sarki abu-turab na mutukar kula da ita duk da baya samun zuwa wajenta sosai amma yana aiko mata da sakwanni sosai..hakama gimbiya amina duk suna nuna mata soyayya..
![](https://img.wattpad.com/cover/192065469-288-k379718.jpg)
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid