*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 39
Wattpad @afreey101**********************
""Bayan an gama daura aure sai kuma aka fara shirin daukar amarya zuwa can masarautar daura ..
Gimbiya amina ce ta kai juwairiya har sashen sarki abu-turab abbanta yayi mata nasiha mai ratsa jiki sosai..
Duk da ba wani shakuwa ce mai karfi ta shiga tsakanin su ba amma sai da juwairiya ta zubar da kwalla sbd tasan sai tayi kewar mahaifin nata sosai..Daga wajen sarki sai kuma akayi da ita akayi sashen gimbiya jamila itama tayi mata nata fadan sannan ta bata kyautuka masu yawa.. daga nan gimbiya amina ta maida ita sashen ta don shirya ta kafin tafiyarsu..
Su zainaba ne akan gaba wajen zolayar ta..
Sun saka ta a gaba suna ta gulmar sarki jalal wai ance tunda aka daura aure bakinsa yaki rufuwa..Ita dai amarya tunanin irin rayuwar da zatayi a can masarautar daura kawai takeyi...ya zasu dauke ta?bare surayya data nuna tsanarta karara..kila gara ma khadija,ooh ita dai ta shige su,wata zuciyar tace,kema fa idan kin koma a matsayin matar mijinsu kike ba baiwarsu ba...
"An shiryata tsab a cikin leshi me shegen tsada kalar light blue da peach,sannan aka rufa mata alkyabba ta ga'do wacce ake kai duk amaryar data fito daga cikin tsatson masarautar kano..
"Wayyo Zanso kuga gogan naku,wato sarki jalal..kenan..
Gaba daya murna da farin ciki sunyi masa yawa..
Yau dai Allah ya mallaka rabin ransa,ya basa farin cikin rayuwar sa...Baki yaki rufuwa magaji na gefen sa sai zuba masa ruwan zolaya yakeyi amma ko a jikinsa..
Shidai hamdala kawai yakeyi wa Allah.."An kawo motocin daukar amarya a nan sarki abu-turab ya zabi mutanen da zasu tafi kai ta..
G-amina ce tare da jakadiya,se hanne baiwarta da kuma AMMI,da yan uwa da suka zo daga kasar zazzau..
Dan shi kam Baya son yawan jama'a kada ace can a samu wata matsalar."""""Kuka sosai juwairiya tasha ganin an fito da ita daga cikin masarautar su ga bayi nan a bayansu sai wakar al'ada sukeyi na daukar amarya..(suna mata bankwana kenan)
Hanne kuwa murna kashe ta zata bi uwar dakin ta..
Zainaba dasu samira kuwa sunyi murna juwairiya zata koma garesu.."Lkcn da suka fito dangin jalal na waje harma da abbansa..
A nan aka shiga motoci liman yayi musu addu'a aka dau hanyar DAURA...**************
Lkcn da suka isa masarautar daura yamma tayi sosai..Hamza da nafisa tare dasu fulani da gimbiya kilishi ne suka tare su cikin girgimawa..
Juwairiya babu abunda gabanta yakeyi sai faduwa,tana kunshe acikin alkyabba gimbiya amina da ammi na rike da ita..Nan aka hau gaishe gaishe gimbiya kilishi ta hada su da jakadiya tace ba sai an kai amarya sashen ta ba,kawai su huce can sashen amaryar dan su samu hutawa sosai kafin anjima..
"Kilishi na barin wajen ta jawo hansai dake ta leken ko zata ga fuskar diyarta..
Sashen khadija sukaje dan kuwa kilishi ta fara jin haushin rainin hankalin da suke son suyi musu..A hakimce ta tarar da ita tiren kayan kwalam a gabanta..
Rabi na gefe tana ji kamar tayi tsuntsuwa taje wajen tarar su amaryar da akeyi,dan tasan zata kwashi kallo bare ance diyar sarkin kano ce...wai!yanzu se de taji lbr a RUMFAR BAYI kenan?Kilishi ta kalli khadija rai a bace..
Khadija ta mike da sauri tana fadin..
Umma sannu da shigowa..
Kilishi tace,rike sannunki..haka ake rashin lfyr dama?ni dama na zargi wani abu wlh..Khadija tayi saurin sadda kai kasa tace,sauki na samu ne yau umma..
Kilishi tace,shine baki fito tarar bakin ba?
Ko duk haukan kishin naku ne haka?
Kuke son ku jawo mana wani sabon raini daga wajen mutanen nan..
Khadija tace,kiyi hakuri umma zanje yanzu nayi musu sannu..
Kilishi taja tsaki tayi gaba a fusace...
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid