*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 18
Wattpad @afreey101*************
"A can cikin gida kuwa, gimbiya kilishi taji shiru shiru babu yarima bai dawo ba gashi har an kusan gama sa lallen..
Fulani diyya ce ta kalli laure tace, jeki ki saka turaki ya fita ya nemo jalal,laure tace toh ranki ya dade sannan ta mike ta tafi.Surayya kam tana can gefe da wasu matan cousins dinsu yarima,sai wani murmushin farin ciki takeyi ganin yarda yarima ya tashi yayi tafiyarsa gashi kuma har yanzu bai dawo ba..
Asiya ce ta kalleta,lallai kuwa surayya na yarda kin gama sace zuciyar yarima..
Karima ta saka dariya,gaskiya ne wannan,tun fa dazu daya fita har yanzu shiru bai dawo ba.
baiwar surayya ce tazo tayi mata rada a kunne,surayya ta kallesu kafin nan tace,ni zan tafi yanzu tunda dai dare ya soma yi kuma banga amfanin zaman mu a nan ba tunda har shima angon ya sallame kanshi ,gaba daya suka saka dariya.."Turaki ne ya fito waje dan neman sa,sai hango sa yayi ya tunkaro gidan yana ta sakar da wani irin murmushi mai kayatarwa..
Mamaki ne ya kashe shi dan ya dade bai ga yarima yana irin wannan murmushin haka ba..Bai gama mamakinsa ba ya hango juwairiya ta bullo daga wajen itama,kuma ga babban mamakinsa itama din silent smile take fitarwa..
Girgiza kai kawai yayi,dan yasan waye yarima yasan kuma halinsa dan haka bazai zarge komai ba.
Karasawa yayi ya taro sa,yarima na ganinsa ya hade rai,ya akayi?
Turaki yace,haba yaya tun fa dazu kayi ficewarka gashi har an gama taron ma kai kawai ake jira a tashi.
Yarima yadan ja tsaki,kafin yayi gaba..***********
Washe gari........"A yau ne ake bikin daurin auren yarima jalal da kuma khadija,sannan kuma a yau din ne jama'ar dake kasar daura zasu halarci na'din sarautar sabon sarkin su wato JALALLUDEEN...
"Tun safe masarautar take a cike tab da mutane daga kowane yanki na nigeria dama tsallake, makida sun zo daga kasar nijar sannan mahauta ma sun zo ana ta yankar shanu ana ban'karesu ana ta gashe su..
RUMFAR BAYI kanta a cike take,dan kamar yarda al'adar take,duk lkcn da ake wani na'din sarautar sabon sarki toh sarakuna da masu kudi da shuni suna bada kyautar bayi ga masarautar dake bikin, kamar wata kyauta ce ko wani abun bajinta ne hakan.
******************
"UMAYMA"
Surayya ta fada cike da murnar ganin baiwar ta dake mata hidima tun a can gidansu.
budurwa ce yar kimanin shekaru ashirin da haihuwa,bakace sosai amma fa akwai kyawu babu laifi..Umayma tayi murmushin murnar ganin uwar dakinta bayan rabuwarsu tun lkcn aurenta..
Ranki shi dade nayi farin cikin sake ganin ki..Surayya tayi dariya nayi kewar ki a kusa dani umayma,dole ne nayi wa yakumbo godiya sosai data turo min dake nan .
Umayma tayi wani irin shu'umin murmushi, sannan ta kalli sauran bayin dake wajen tace,ku bamu waje!Duk suka fice suna mamakin iko irin umayma sai kace itama din ba baiwar bace kamar su..
Surayya ta gyara zaman ta tace,da magana a bakin nan naki umaymah,kwararo min su naji...
Umayma ta matso sosai gaban surayya, ta fito da wani kulli acikin rigarta,ta kwance shi ta fito da wani garin magani..Ungo wannan gimbiyata ,surayya ta amsa tana juya kullin maganin,menene shi din?
Umayma ta gyara zama tace,yakumbo ta aike ni wajen malam jatau dake can yobe,ya bani wannan maganin na daukar cikine da wuri..
Surayya dadi ya mamaye zuciyarta,tace,da kyau umayma..amma kinsan fa shi yarima ba kullum yake son yin abun ba,gashi har ma yau amaryar sa zata tare kinga idan har ya kwana da ita tana iya samun ciki a daren farkonta..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid