*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 26
Wattpad @afreey101******************
"Juwairiya na kallonshi har ya karaso zuwa gabanta ya tsaya..
"Kin hada min kayan?
Juwairiya tace,
yanzu na gama ranka shi dade..
Ya lumshe ido,
toh shiga ki hada min ruwa nayi wanka..
Juwairiya tace toh sannan tayi hanyar toilet da saurinta..
"Ta fito ta sanar masa ta gama,bai ce mata komai ba ya shige toilet din..
Yana shigane ta samu damar gyara masa dakin tsab..Ta kalli kofar toilet din,ta kammala komai na aikinta amma sai ta samu kanta da rashin fita son daga cikin dakin..yau zayyi tafiya ko ba komai tana so suyi sallama..
Matse baki tayi sannan ta fita ta dawo falon ta zauna akasa dan jiransa..Jalal na fitowa ya tarar babu ita a dakin,bai ji dadi ba kodan dan yaso ace yayi sallama da ita...
Sai daya dauki awa daya yana shiri kafin ya fito cikin shiga ta alfarma..Caraf ya ganta a zaune ta rakube a waje daya..
Murmushi ya saki ya karasa wajen yana fadin..
"Ya baki tafi ba?
Juwairiya tayi saurin mikewa..
Uhm dama dama uhm yauwa jakadiya ce tace na jira ta a nan..
Ya jinjina kai dan zuciyarsa ta gama basa shi take jira...
Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya nufi wajen shakatawar sa da ita..Ya sake hannun nata sannan ya rufo kofar wajen.
Juwairiya gabanta ne ya shiga faduwa..
Jalal yace..
Yau zanyi tafiya...ya karashe mgnr cike da wani irin yanayi..
juwairiya ita kanta se dataji wani iri.. da murya me cike da sanyi ta samu kanta da fadin..
'Yaushe zaka dawo?Ya kurawa kwayar idonta kallo..
Kwana biyune..
Juwairiya tayi murmushin yake tace..
Allah ya dawo dakai lfy ranka shi dade..
Jalal ya gyada kai..
Nagode..
Hayaniyar su shamaki ya jiyo daga waje..
Yaja lumfashi ni zan tafi..
Ta jinjina kai ta kasa furta komai..
Ya juya har ya kai bakin kofa ya sake juyowa..
Bai bata wani lkc ba ya janyo ta jikinsa..dan gaba daya kasa controlling zuciyarsa yayi..Juwairiya taji gaba daya duniyar ta tsaya mata tsak...
Sai da suka shafe seconds talatin kafin yayi karfin halin sakinta ya juya da sauri ya fice........*************
"Yana fitowa waje ya tarar da fadawa sun cika wajen gasu magaji da turaki suna ta jiransa suma..
Ya karasa wajen su cikin takon girma kafin suka nufi sashen gimbiya kilishi ga baki dayansu..A nan suka tarar dasu surayya da khadija kowacce najin da kanta..
Sallama sukayi musu...sannan suka sake zuwa sashen mahaifinsu anan suka iske fulani sukayi musu sallamar suma kafin suka dau hanya.."Sun isa kasar zazzau da yamma sosai..
Sarki ya saka aka kaisu masaukin su..
Abinci kala kala aka kawo musu suka ci sosai kafin duk suka bi lafiyar gado sbd sauke gajiya..***************
Yau kwanan jalal daya da tafiya amma juwairiya duk ta rasa me ke mata dadi,
har fada take wa zuciyarta,ke wacece a wajensa da zaki damu dashi haka uhm?
Ta girgiza kai,yarima ka barni na huta!
Ta kalli zobensa data amso dazun wajen me siyar da kifi..ya zanyi da kai yarima?Zabba'u ce ta shigo dakin ta sanar mata da sakon zainaba na son ganinta a sashen ta..
Tana fitowa daga rumfar bayi suka hade da umayma..
Umayma tace,sai ina haka juwairiya, ko saurayin naki zakije gani ne?
Gaban juwairiya ya fadi,ta ware ido tana dafe kirjinta..
Saurayi kuma?ta fada cike da faduwar gaba..
Umayma tayi dariya ke wasa fa nakeyi miki..
Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya,kee kuwa kin cika uwar zolaya..
Umayma ta jinjina kai sukayi sallama kowaccen su ta kama gabanta.."A can kasar zazzau kuwa,sarki da kansa ne ya bukaci ganinsu da safe,suka shirya suka same sa a palace dinsa..
Sun fara mgnr yarda auren zai kasance sarki ya saka a kirawo masa dansa na fari wato mahaifin yarinyar da ake son hadawa da turaki..
yana shigowa fa'da ya kwashi gaisuwa wajen mahaifinsa sannan aka saka ranar biki..
Turaki dai kallonsu kawai yakeyi dan shikam dan dole ne zai yi wannan auren.
jalal ne ya sanar dashi sakon mai martaba dayaje yaga yarinyar can a gidansu aka hada shi da wani bawa..ba da son ranshi ba ya tafi..
![](https://img.wattpad.com/cover/192065469-288-k379718.jpg)
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid