6

10.6K 788 26
                                    

    *RUMFAR BAYI*
   (A historical fiction )

NA Afrah bhai
Page 6
Wattpad @afreey101

*******************

**bayan shudewar shekaru bakwai**

'Gaba daya masarautar a war'gitse take.
A sanadiyyar bakin dauren auren YARIMA JALAL da diyar sarkin adamawa wato gimbiya SURAYYA da akeyi a ranar ta yau, wato shidda ga watan sa'tumba.

     'Mutane ne tan'kam cikin masarautar ko ina ka kai idonka bayi ne keta hidima ana ta shirye shiryen amsar dan'gin amarya dake tafe daga kasar adamawa...

   "Can na hango yan wasan doki suna ta kokarin shirya KILISA(wasan doki),A gefe kuwa yan busan algaita ne ke tayi masu kanguna ma nata bugawa take masarautar ta dau sautin ki'da me kayatarwa,yan wasan wuka da yan farauta ma nata nuna tasu bajintar..

*************
'Tun asubahi duk baiwar dake cikin Rumfar bayi bata zauna ba,rabinsu duk suna cikin madafa ne ana ta hada'hadar dahuwar abinci na gani na fada.
dan shanaye sun fi dari da mai martaba yasa aka yanka su banda kuma kaji da wasu kananan dabbobin.

"Hansai ce na hango duk  hidima  tayi mata yawa.
can sai ga wasu kuyangi sun shigo,wajenta naga sun nufa cikin saurinsu daya daga cikinsu tace,hansai wai ina JUWAIRIYA ne gimbiya zainaba na can nata faman nemanta.. tace idan mun ganta mu sanar mata da cewa su hadu da ita a can sashen gimbiya kilishi...

'Hansai ta girgiza kai...
lallai wannan yarinyar wato bata tashi ba kenan duk dukan da nayi mata da asubahin nan..
Laure ta kwashe da dariya,ai ni kam gara da Allah yasa zainaba ce uwar dakin juwairiya da ina fada miki tuni yarinyar nan zata jawo mana musiba sbd shegen son jikinta..

  Jakadiya tace,haba kun manta aikin data sha ne jiya daddare duk fa itace ta ba're wancan danyen waken.
jakadiya ta sake kallon laure dake faman  wanke wanke tace,ke laure tashi kije ki sanar mata sakon uwar dakin tata ..

'Lkcn da laure ta shiga dakin juwairiya ta hango kwance akan taburmar ka'ba tayi dai'dai tana ta kwasar barcinta hankali kwance dan shaf ta manta da wani daurin aure da akeyi a cikin masarautar..

Laure ta shiga tashin ta..juwairiya maza ki tashi...!
A firgice ta farka tana gogar idanunta dake cike da barci..
Ni kuwa afrah na saki baki ina kallon kyakkyawar fuskarta,laure tace,se ki tashi dan yanzun nan uwar dakin ki tayi aiko a sanar miki daki same ta a sashen gimbiya kilishi...

Ai tun kafin laure ta rufe baki juwairiya ta mike da sauri ta zari gyelen ta tayi waje da gudu duk kiran da laure keyi mata bai sa ta tsaya ba .....

Gudu takeyi sosai dan shaf ta manta da maganar da sukayi jiya ita da zainaba..

Yau ta shiga uku!
Me ya same ni haka ne?
Wane irin bacci ne nayi haka!oh Allah!

'Abun mamaki tana zuwa sashen gimbiya kilishi ta tarar da sashen wayam babu kowa a wajen duk kuwa da  cikar da masarautar tayi a yau..
Ta karasa ciki tana kalle'kalle ko zata ga zainaba tunda tace kayan biki zasu zo amsa a wajen gimbiya kilishin...

    'tana faman leke'leke kawai taJi kamar wani ana kokarin  shigowa..
Tsoro ne ya kama ta sosai dan kuwa tasan idan har aka kamata a ciki ba tare da zainaba ba kuma babu kowa acikin sashen toh kashin ta ya bushe...

   Bayan wani lalube ta boye jikinta na tsananin rawa..se addu'a takeyi Allah yasa ba gimbiya kilishi bace ta shigo ita tsoron matar takeyi..

   bata ankara ba sai Jin takon mutum tayi kawai..

Bugun zuciyarta ne ya linku...
Ta dafe kirjinta...ganin inuwar mutum a gabanta yasa ta runtse idonta gam dan ta sadakar da an gama kama ta....

  Shi kuwa yarima jalal mamaki ne yakeyi ganin inuwar mutum a cikin labule dan kuwa ummansa ta shaida masa data kori kowa daga sashen na ta dan kawai yaje yayi shirin sa tunda nashi sashen  cike yake da ya'yan sarakuna abokansa da sukazo dan daurin aure...
    
Bai bata lkc ba ya yaye labulen cikin zafin nama....

Rumfar bayi Donde viven las historias. Descúbrelo ahora