8

10.4K 903 30
                                    

         *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
NA Afrah bhai
Page 8
Wattpad @Afreey101

*************************

            'Tana shiga sashen zainaba ta tarar da ita a tsaye sai safa da marwa takeyi.
Juwairiya ta mi'ka mata furen dake hannunta, ta amsa tana sakin murmushi me kayatarwa,gaskiya furen nan yayi min kyau sosai,se de akwai wata matsalar kuma juwairiya.. ta karashe mgnr kamar zatayi kuka..

     Juwairiya tace,matsalar me kuma ranki ya dade ba dai har sun tafi din ba?

'Zainaba ta girgiza kai,dazun ne fulani ta aiko min da sakon cewa kada na fita ko ina  zata aiko min da wata mai magani ta dubani akan yawan ciwon cikin nan da nake fama  dashi ,kin kuma san halin fulani, har fa wani bawa ta ajiye a kofata wai dan kada na gudu sbd bana son magani..yanzu ya za'ayi na fita kenan?

         'Juwairiya tadanyi tunani kadan sannan tace inda ranki ya dade ba zata damu ba ina da shawara..
Zainaba tace da gaske?
Juwairiya ta gyada kai ..
Zainaba tace fadi muji..
Juwairiya tace ko naje na sanar dashi bazaki iya fitowa se shi din yazo nan..

Zainaba ta ware ido...
Ah ah bana so yazo nan juwairiya..ta karashe mgnr a shagwabe tana kallon juwairiyar..
Can kuma tace,yauwa! Tasa hannu taja juwairiya zuwa dakinta...

'Cire.....ta fada kai tsaye..
Ciki da mamaki juwairiya ke kallonta..me zan cire ranki shi dade ?
Zainaba ta nuna kayan dake jikin juwairiya..cire kayanki ki bani..
A tsorace juwairiya tace,kiyi hakuri ranki ya dade amma.....

Zainaba tayi dariya,ba ina nufin ki tu'be min ba dan naga jikin ki ba..
Ah ah ina so ne muyi canjen kayane kawai kin ga babu wanda zai san ni ce na fita bake ba ko?

    Juwairiya ta gyada kai,wato wayo zakiyi wa fulani ko?amma idan aka kama mu fa?ni gsky tsoro nakeji..
Zainaba ta murmusa kada ki damu bazan jima ba zan dawo,kedai kawai cire kayan ki bani..

Juwairiya a sanyaye ta cire kayanta,zainaba ma ta cire nata ta bata..
Juwairiya tabi kayan da kallo,ina zata iya saka wadan nan kayan?
Ta girgiza kanta,ranki shi dade bani da matsayin da san saka wadan nan kayan..
Zainaba ta harare ta,amsa!
Kuma umurni nake baki daki saka su yanzun nan!
Juwairiya ta amsa a tsorace..
Tana kallon zainaba bata nuna wani kyama ba ta saka nata kayan tana dariya tace,lallai ke kam wannan kayan naki ashe walawa kike yi sosai..(ta fada tana jujjuyawa cikin katoton rigar juwairiya )

Juwairiya dai da kallo kawai take bin ta,a sanyeye ta saka kayan itama atamfa ce riga da zani sai wata alkyabba ja da ruwan madara,ita kanta tayi mamakin yarda kayan suka amshe ta....
Zainaba tabi ta da kallo,lallai juwairiya Allah yayi mata baiwa dayawa,se de kawai yanayin data tsinci rayuwarta ne...
     Zainaba tace,toh ni na tafi,ta dauki furen ta tana sake fadin,babu wanda zai gane ni ce,ta saki murmushi tayi gaba..

juwairiya ta zauna a takure tana tunanin idan wani ya shigo fa yanzu tasan tabbas kashin seya bushe..
    Motsin dataji ne a waje ana sanar da shigowar turaki yasa ta saurin komawa shinfidar zainaba ta kwanta hade da juya bayanta ta rufe rabin fuskarta..

   A tsanake ya shigo falon cike da takonsa yana mamakin rashin ganin juwairiya da bayyi ba..
    Yan matan fulani naji mun kusa hutawa da jinyar ciki ko?dazu fulani ke sanar min an kawo me magani daga cikin katsina..

     Juwairiya tayi wiki wiki da ido,bata so ko kwakwaran motsi tayi turaki ya gano ita ce..
Turaki ya zauna yana mamakin shirun da zainaba tayi masa..
To wai ko barci take ne ?
Yana wannan tunanin ya mike har ya kai bakin kofa yace, ko ina kawarta ta tayi yau oho..

   Juwairiya najin fitar sa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike zaune,se a lkcn ta nuna da inda take zaune(wato akan kilisar zainaba ),ta mike da sauri tana sake kallon shigarta,tabbas bata taba saka kaya irin wannan ba,ta dan murmusa zataso ummanta dasu jakadiya su ganta a cikin irin wannan shigar..
Wani tunani ne yazo mata..
Da sauri naga ta shige dakin zainaba ta dauko mirror tana kallon kanta..

Rumfar bayi Where stories live. Discover now