*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 16
Wattpad @afreey101*****************
"Me yasa bakiyi amfani da kyallen dana baki ba?"Juwairiya taji muryar sa me dadin saurare a bayanta yana mgnr kamar bayaso dan itama zuciyarta na wajensa da bazataji me yace ba..
Juyowa tayi kanta a kasa kafin tace a sanyeye..
Kayi hakuri ranka shi dade amma bazan iya daure kafata da abunda ya fito daga hannunka ba,dan ko kadan ban kai wannan matsayin ba..Yarima ya jinjina kai..sannan yace da ita,
Daga yau duk umurnin dana baki ina so ki bi shi inda har kin dauke ni a matsayin da nake din..
juwairiya ta gyada kai da sauri..Kinci abinci?
Tambayar tazo mata a ba zata..Juwairiya taji kamar ta nutse,miye na sa wai idan taci abinci ko bata ci ba..
Girgiza kai tayi..Yadan ja lumfashi idan kin koma cikin masarauta ki same ni a sashena...
Zatayi mgn taji karasowar khadija...
Khadija ta mika mata maganin tace ta shafa,ta amsa da hannu biyu ta shafa ,sannan khadija da kanta ta daure mata kafar..
Godiya sosai juwairiya tayi mata sannan ta fice....***********
"Har ta kai wa zainaba wasikar amma ta rasa taya zata je sashen yarima,me yasa yace mata taje?tunani ne ya cika ta sosai har bataji firar da zainaba ke mata ba..Zainaba na lura da ita tace,lafiya juwairiya ko kafar ce?..
Kije kawai ki huta zuwa anjima.
zansa fulani ta aiko min da wata baiwar..
Juwairiya ta samu kanta da jin dadin hakan..
Ta mike tayi mata godiya kafin nan ta fice..***************
"Tana fitowa daga sashen sukaci karo da turaki zai wuce ..
Tayi saurin gaishe sa..Ya amsa yana kallon kafarta..
Ciwo kikaji ne haka?ya fada cike da kulawa..
Juwairiya tace eh dazune wlh..
Turaki yace ayyah,muje na baki magani kiyi amfani dashi..
Juwairiya zata fara mu'sa masa sai kawai yayi gaba,dole tasa ne tabi bayanshi..'Tafiya kawai takeyi,amma hankalinta na kan umurnin da yarima ya bata na zuwa sashen sa...
Suna shiga sashen a bakin kofa taja ta tsaya,turaki ya shiga ya fito mata da maganin,amsa tayi tana masa godiya...Turaki ya saki murmushi yace, ki rin ga kula da lafiyar ki..
Juwairiya ma murmushin tayi tace nagode sosai yaya turaki..
Juyowar da zatayi ta hango yarima da hamza a tsaye zasu wuce..Idanuwansa a kanta..
Gaba daya taji wani irin faduwar gaba..
Yarima ya dauke kai kamar bai gansu ba yayi gaba abunsa...********
"RUMFAR BAYI ta nufa kai tsaye babu wadu bayi dayawa a ciki,dakin du'bu ta shiga,ta tarar itama bata nan..
Komawa tayi dakinsu ta canza kayan jikinta sannan ta zube akan taburma.Da sauri ta mike ta dauko kyallen da yarima ya bata dazu tana kare masa kallo,wata zuciyar na tunashe ta umurnin sa na zuwanta sashen sa..
Ta mike da sauri ta fito kai tsaye tayi sashen nasa..Ta dade a waje tana tunanin ko kada ta shiga..
Can dai ta tayi shahada ta shiga tana addu'a Allah yasa ba wani laifin tayi masa ba.
bawan dake waje ne ya sanar da shigowar ta...
A sanyaye cike da tsoro ta shiga falon da sallama..Zaune yake ya lumshe idonsa..
Ta samu waje ta takure sannan tace..
Ranka shi dade gani nazo..
Har cikin ransa yaji sautin muryar ta..
A hankali ya bude ido ya sauke su akanta..Juwairiya tayi saurin dukar da kai..
Yarima yace,zauna yana nuna mata waje a nan kusa dashi kadan..
Juwairiya ta kalleshi taga yarda ya tsare gida dole yasa taje ta zauna wajen a takure..
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid