babi na sha daya

10.1K 967 31
                                    

       *RUMFAR BAYI*
      (A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 11
Wattpad @afreey101

******************
      'juyi kawai yakeyi a gadon barci ya'ki daukarsa,ya kalli gefen da surayya take a kwance tana ta sharar barcinta hankali kwance..

"gobe ne zam'to tafiyar su kasar chadi,ga tunanin wannan yarinyar gaba daya yaki barin kwakwal'warsa,ya mike ya zauna yana dafe kansa,ya za'ayi ya nemo ta a cikin dubban bayin dake cikin rumfar bayi,wata zuciyar kuma tana gasgata masa cewa wannan yarinyar ba baiwa bace..
Ya koma ya kwanta yana sauke lumfashi  bayan ya yanke wata shawara wacce kila ta amfane shi(ni ko afrah nace ko wacce shawarar ce? )...

****************
"Da safe juwairiya ta gama shirinta tsaf,tana fitowa daga dakinsu taga an jera bayi layi layi kamar ana asambili..

"Mamaki ne ya kamata sosai ta karasa wajen ummanta dake ta kokarin jera wasu fuskar nan a daure kam..
   Lafiya umma?ya naga duk sun ja layi?haka

  Hansai ta dan girgiza kanta cike da jimami tace, kema shiga layi ki bi mu..

Juwairiya a tsorace tace harda nima umma?ina zamuje ne haka?
Laure dake karasowa wajensu tace, sashen gimbiya kilishi zamuje,dan haka inaso ki nutsu da kyau nasan dai ko hauka sukeyi bazasu dauke ki cikin yan tafiyarsu ba..

  "Hansai ma kallon diyar tata kawai takeyi,a tsorace take sosai dan kuwa idan har za'ayi tafiya irin wannan kuma aka bukaci daukar bayi mata dan a tafi dasu,toh duk akasari  dawowa sukeyi da ciki wasu kuma ace an sayar dasu ga mutanen can garin,wasu a lalatasu,wasu kuwa a maida su SA'DAKA..

   "Juwairiya ta dafa ummanta,kada ki damu umma na fahimci duk tsoron da kikaji sbd ni ne ko...
Hansai ta dan kamo hannunta, idan mukaje kada ki kuskura ki dago da kanki kina jina?duk da ma nasan da wuya ne a zabe ki,juwairiya tayi dariya tana nuna mata tabon fuskarta,tunda inada wannan umma ba inda zani je..
A sanyaye hansai ta gyada kai,hakane ..
Yanzu shiga layin mu tafi..

*****************
"A sashen gimbiya kilishi kuwa,yarima ne tare da magaji da hamza a zaune gabanta..

Kilishi tace,na saka duk a kawo muku bayin dake masarautar nan,ku zabi wacce tayi muku dan bana so kuje can ana yi muku kallon baku isa ba..dan ni burina a kullum shine ku samu girgimawa a wajen mutane..

     Magaji yayi murmushi, godiya muke umma..
Hamza yace,abun mamaki wai yau yayane da kansa yake son tafiya da bayi mata...
ba'cin kullum fada yakeyi min idan na dauke su..

Yarima ya banka masa harara. .
Kilishi tace ina ruwanka toh?ka manta jiya ba yau bace?duk suka saka dariya..

Suna cikin mgn sai ga jakadiya da du'bu sun shigo suna sanar dasu an tara bayin suna waje..

    Yarima gaban shi ne ya fadi,idan ya ganta a cikin bayin can ya zayyi?addu'a kawai yakeyi Allah yasa bata cikinsu wata zuciyar kuma na addu'ar Allah yasa ya kanta..
Cikin wannan tunanin ne ya karasa waje shima yana baza idanuwansa ta ko ina...

Kilishi ta kallesu cikin kasaita tace,yarima....je ka duba wadan da sukayi maka,ta mika masa wata sanda kamar yadda al'adar su take idan yaga wacce tayi masa zai sa sandar ne ya nuna ta dashi...
    Cikin tafiyarsa me daukar hankali ya karasa gaban bayin dake jere kowacce ta sunkuyar dakanta cike da ladabi...
  
************
"A wajen juwairiya kuwa tana jin ance yarima...gabanta ya fadi..ras!
Ta sake sunne kanta kasa tana matse hannayenta duk da tasan ita dai ba daukarta ma zayyi ba amma hakanan bata son ya sake wulakanta ta kamar yadda ya saba..
 
Yarima na tafe har ya kusa kai wa karshen layin kawai ya hango side view dinta,
bai gama tantance ko wacce yake tunani bace kawai kai tsaye ya saka sandar cikin saurinsa ya dauke mayafin data lulluba akan ta..

    Jikin juwairiya ne ya hau rawa,miye hakan?
Ita ya zaba?
Kodai bai gane ta bane?
Yau ta shiga uku...runtse ido tayi kawai.....tana ji kilishi na cewa KE!! Fito...!
**********
Shi kam yarima wani irin yamutse fuska yakeyi ganin wacce ya canko,me yasa wannan me konannar fuskar ta cika bibiyar rayuwar shine?
Tsaki yaja ya koma gefen su kilishi ya tsaya dan gaba daya ranshi ya baci..
  
A sanyaye juwairiya ta fito ta tsaya kamar ta rusa ihu takeji..

Kilishi ta yamutse fuska tana mamakin duk a cikin bayin nan wannan ce yarima zai dauka?ko da yake tasan dan nata,komai nashi na daban ne..

     Kilishi tayi gyaran murya tace,toh sai kije ki shirya kayanki dan tafiyar tasu cikin nan da minti talatin ce...
Ta juya wajen magaji,kai ka koma ka zabar muku sauran dan naga ra'ayin abokin naka sai a hankali...tana gama fadar haka ta shige ciki abunta..

  Du'bu da jakadiya duk ransu bai so aka zabi juwairiya ba ko kadan,toh balle hansai da laure dake gefe suna hawayen bakin ciki...

     Yarima ya banka wa juwairiya harara kafin ya wuce magaji da hamza suka bi bayan sa..
    Ai suna watsewa bayin duk sukayi kan juwairiya dake kuka,hansai ta kamo hannunta suka karasa rumfar bayi..

   Suna kuka suna hada mata yan kayan ta..
  Laure tace,kada ki damu juwairiya babu abunda zai faru dake se alkairi..
Hansai ma sauke lumfashi tayi,ta riko hannun ta..

Hankalina yadan kwanta jin tafiyar tasu yarima da magaji ne,na tabbata babu wani abunda zai faru dake dan kuwa yarana ne da suka san abunda sukeyi,ki kwantar da hankalinki kinji?duka kwana uku zakuyi zuwa biyar,kada ki manta da tabon fuskar ki shine kariya a gareki kinji?
Juwairiya ta gyada kai kafin ta dau kullin kayanta ta fice..

**********
Tana fitowa ta hango zainaba can gefe a tsaye tana jiran shigowar ta..
Da sauri ta goge hawayen ta tayi wajen ta..

Zainaba na ganinta ta fara hawayen itama a shagwabe tace..
Yanzu fi sabilillahi dauke min ke yaya jalal zayyi..

Juwairiya tayi murmushi, kada ki damu zanki ya dade babu me dauke miki ni,tafiya kawai zamuyi mu dawo kinji..
Zainaba ta gyada kai,muje kiyi sallama dasu fulani...

Suna shiga sashen fulani diyya,juwairiya ta zube kasa tana kwasar gaisuwa..
Fulani a sake ta amsa mata tana fadin,ashe dake zasuyi tafiyar?

Juwairiya tace uhm,fulani tace,toh Allah ya dawo daku lfy,gaba daya falon suka amsa da amin..
    Suna fitowa waje suka ci da turaki..
Yana ganinsu ya sauke idonsa kan juwairiya,a take ya fahimci hankalinta a tashe yake..

   Gaida shi sukayi,yayi murmushi yace,ah ah yan matah ana ta bankwanar ne?
Zainaba ta shagwabe fuska,yaya harda kai zolayar ko?
Turaki yayi dariya,naga ai kwana uku ne kawai miye abun damuwa?ya karashe mgnr yana kallon gefen juwairiya..

    Juwairiya tadan murmusa kawai..
Turaki yace,addu'a kawai zakuyi abunda akaje nema a samo shi lafiya,yana gama fadar haka ya shige ciki cikin takunsa...

  Zainaba ta ja juwairiya zuwa sashen ta..
Wani kulli ta miko mata..
Gashi ki ringa ci ahankali a hanya kinji..
Juwairiya cike da murna tace nagode ranki ya dade...
Wani bawa ne yazo yana sanar dasu ana neman juwairiya...

*************
Motace irin ta da dinnan,sai wata bus..
Juwairiya da gudunta ta karasa wajen..
Yarima da magaji na tsaye da sauran bayin duka an gama saka kayansu a cikin motocin..

    Tana zuwa duk suka maida kallonsu gareta..
Yarima yaja tsaki...lallai ya gama kufsawa kansa yanzu haka zai tafi da waccan yarinyar yana kallon konannar fuskar sa,mtsw ..

Surayya ce ta karaso wajen tare da baiwa a bayanta..
     Wajen yarima taje ta mika masa kullin dake hannunta..
Se daya kalle ta sannan ya maida kallonsa kan kullin yace,menene?

Tadan karkace kai,
Ka amsa mana kaga fa akwai  mutane a wajen,yadan yi yake sannan ya amsa ya shige mota,surayya tabi bayin dake wajen da kallon wulakanci balle ma juwairiya data gani duk a tsorace...
Suna shiga mota shamaki da galadima sukayi  musu addu'ar suka lafiya sannan suka hau hanya...

"Toh ya kuke ganin wannan tafiyar zata kasance?"

Keep following rumfar bayi..

For the rating so far....
Team juwai-80%
Team yarima -60%
Lol naga ma harda team Turaki munada big ups 2 u

Rumfar bayi حيث تعيش القصص. اكتشف الآن