*RUMFAR BAYI*
(A historical fiction)
Na Afrah bhai
Page 40
Wattpad @afreey101*******************
"Washe gari.."
"A babban falon tsohon sarki Abdul-Jabbar duk aka hallara dan damka musu amanar amarya juwairiya..
Tsohon sarki yayi godiya sosai sannan ya saka ayi masa kiran hansai da laure ...
Suna shigowa falon a take ya cika alkawarin da ya daukarwa mai martaba sarkin zazzau...wato ya YANTAR dasu kenan..Zo kuga murna a wajen juwairiya da ma sauran bayi...jakadiya sai taya su murna takeyi...hansai da laure kam ji suke tamkar mafarkine sukeyi...
Fulani da gimbiya kilishi sunyi murna suma sosai saidai ba karamin rashin bayin nasu zasuyi ba sbd dai an dade tare..
Lkcn da akazo rakiyar su Ammi..
Hansai ta tabbatar musu da cewa ba zata bar juwairiya ita kadai a masarautar nan ba,zata zauna tare da ita dan ta kula da diyarta..
Laure ma tace itama bazata bar juwairiya ba zasu kula da diyar su sannan zasu fara kasuwanci dan tallafawa rayuwarsu..
Sosai ammi da gimbiya amina sukaji dadin kalamansu dan dama suma damuwarsu yarda juwairiya zatayi rayuwa acikin masarautar sukeyi
Sukayi masu godiya sosai kafin suka hau hanya.."A sashen sarauniya JUWAIRIYA kuwa,hanne ce da zainaba zaune suna ta shan firarsu..
Hansai da laure suka shigo suna gu'da sosai suna rawa cike da farin ciki..
Juwairiya tayi dariya dan ta san yarda sukeji yau sun samu YAN'CINSU..Rabi ce shiga lekowa tana komawa..
Tunda taji lbrn juwairiyya ce matar da jalal ya aura take ta son tazo ta ganta....
zabba'u dake zaune a bakin kofar ta hangota ta mike tana fadin..
Ki shigo mana rabi..
Rabi ta shigo ta zube gaban juwairiya tana kwasar gaisuwa..
Juwairiya tayi murmushi tace..
haba rabi nifa ce juwairiyar da kika sani a baya kawarki..
Rabi tace kai amma na tayaki murna sosai ranki ya dade, kingan ki kuwa?kamar ba juwairiyar mu ta RUMFAR BAYI ba..
Gaba dauansu suka kwashe da dariya......."Da yamma kuwa sai ga jakadiya ta shigo da sakon kilishi akan a shirya juwairiya dan yau kwanan sashen AMALE zatayi..
Jiki na rawa su hansai suka shiga shiryata..
Wanka sukayi mata cikin madara kamar yarda al'adar su take..
Aka turare ta ga mayuka kamsu sanyin kamshi an shafe ta dasu..
Samira da zainaba suka gyare mata gashinta sai santsi da kamshi yake..
laure kuwa murna takeyi sosai yau zata tsantsara wa diyarta kwalliya ba wannan TABOn a fuskata .."Sosai suka gyara juwairiya ta fito amaryar ta kyau kam ba'a mgn..
Dan har daukar ido takeyi😉..Zainaba,samira da nafisa tare da jakadiya ne suka kai ta har sashen jalal..
Har cikin makeken dakinsa suka shiga.
Mamaki ne ya rufe juwairiya ganin da tayi kamar ba dakin data sani bane,..Yasha gyara sosai da furenni (flowers) masu kamshi ga fitilu an kunna ko ina ya dau haske..
Zainaba tace yadai Giwar Amale munyi kokari ko kuwa?juwairiya ta juyo tana musu kallon mamaki..
Samira da nafisa suka tafa suna dariya..
Jakadiya ta zaunar da ita kan gadon sannan ta kalli su zainaba tace..
Toh Ku Muje dan nasan duk inda mai martaba yake yana gab da shigowa..Zainaba ta rungume juwairiya tana rada mata wani abu a kunne..
Juwairiya ta waro ido tana kai mata dukan wasa...
Da gudu duk suka fice daga dakin suna mata dariya.."Ta zauna shiru tana kare wa dakin kallo..
Wai fa nan Dakin da take shigowa gyara ne...
yau gata a cikinsa a matsayin matar me dakin..
Taja lumfashi tana shakar kamshi me sanyin dadin dake mamaye da dakin..
Ji tayi kamar ana shirin shigowa dakin..
Tayi saurin hayewa kan gadon ta gyara zamanta tana lullubawa kanta mayafi...
YOU ARE READING
Rumfar bayi
Historical FictionA historical romantic hausa love story.. Between a prince and his maid