_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)**Godiya nake SALMERH MD Allah ya bar so da ƙauna, Noorul yana tafiya dani wallahi, Allah ya kara basira da hazaƙa, Allah yasa kifi haka aci gaba da gashi soya sai ranar sallah..*
'''MAMA QUEEN kema kina raina Rushin So na wujijiga ni gaskiya, akara mana yawan typing Allah ya kara basira yasa kifi haka..'''
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 1⃣2⃣
Cikin tsananin kuka nake maganar wanda ya karyar da zuciyar Kawu na, jikin sa yayi bala'in yin sanyi zuciyar sa tayi mai nauyi, sai yake gani kamar yanzu ne ƙanwar sa ke bashi amanar MUNIBBAT...
Gani yayi shiru baice mun komai, zuciya ta ta sake tsinkewa wajen kayana na nufa, a hankali na tsugona na ɗauka wasu irin hawaye masu zafin gaske suna zubo min, ban sake juyowa na kalle cikin gidan ba murya a sanyaye nace" na tafi Kawu! na gode sosai da soyayyar ka a gareni har abada bazan manta da kai ba, domin kai ne jigo na, ka sanya ni farin ciki a lokacin da narasa mahaifiya ta, ka gata tani a lokacin da narasa mahaifi na, ka zamo mun babban bango lokacin da dukan ginina ya rushe, ka fifitani akan ƴayan cikin ka, ka bani kulawar da har na ƙwanta dama bazan manta da ita ba, kuma har yanzu na san kana so na Kawu na, amma dan Allah ko bayan bana nan kar kayi min kuka, karka zubar da hawayen ka saboda ni, ka ƙasance me min addu'a kamar yanda na sanka, domin ita na fita buƙata a yanzu, ka mayar da soyayyar da kake min akan su BISHIRA, ina me maka salama Kawu Allah ya haɗa mu a aljanar fiddusi...""
har na kai ayya bai waigo ba, gani zan tafi bai tsaƴar dani ba yasa na zubar da kayan hannu na, da wani mugun gudu naje na rungume shi ta baya, ƙanƙame shi nayi iyakar ƙarfi na, ina sakin wani rikitacen kuka ji nake tamkar ƙarshe na ne yazo, shikenan zanyi bankwana da sanyi idaniya ta, sake ruɗewa nayi cikin kuka me hauhauwa nace" zanyi ƙewar ka sosai Kawu na! dan Allah kar mu rabu, wallahi ina son ka ina jin dadin rayuwa da kai Kawu na!! rayuwa ta zata shiga garari Kawu in na tafi ina zanje? kar fa ka manta ban san kowa ba a garin nan, ka mayar dani kaduna dan Allah..."
kuka yaci ƙarfi na numfashi na yana wani fita da ƙyar...Dis-dis naji saukar ruwan hawayen sa a hannu na, da wani mugun sauri na ɗago kai na, ina kallon kyeyar sa gani bazai waigo sa nayi saurin shigewa gaban sa ta yanda ina iya kallon fuskar sa, gaba na yayi mumunar faɗuwa ganin da gaske kuka yake a kai na da sauri naja baya ina girgiza kai na, cikin kasalaliyar muryar da ta gaji likis da kuka nace" bazan jure gani hawayen ka ba Kawu, bana so ka sake kuka sabida ni kuka..."
Da sauri na ɗauki kayana na fice a gidan da mugun sauri bama na gani gaba na sosai wallahi tafiya kawai nake duk inda na samu saka ƙafata nake, ko tunanin banyi ba akan na je gidan su Aysha hawayen sa kawai nake tunawa zuciya na sake tsinkewa, tsoro na kara kama ni...
Sam Kawu baiyi tunanin na fita ba, zuciyar sa da tunanin sa gaba ɗaya sun tafi ne ga tsananin tausayi na da ƙauna ta, yana shirya yanda zan fuskace ni na yafe mai kukan da ya sakani, wata irin kunya ta yake ji a hankali yace" ƴata nima ina ƙaunar ki har abada bazan taɓa korar ki ba, nayi miki haka ne ko zaki kiyayye gaba, ki yafeni hawayen da kika zubar ta dalili na.." ya fad'a yana waigo game da haɗe hannuwan sa waje guda, wayam yaga wajen sai Anty dake tsaye zuciyar ta na tafasa tunda take dashi bai taɓa kuka akan ta ba, ko neman yafiyar ta in yayi mata laifi, sai yau kan ƴar ƙaramar yarinyar yake zubar da hawayen sa har da haɗa hannu, ga kalamai masu dadi da yake furta mata, zuciyar ta tayi baƙiƙirrin...
" SHAFA'ATU ina take!!?.." ya ƙatsi ta cikin daka mata wata irin tsawa...
Tsananin tsorata da tayi ya hanata amsawa sai raba ida take, cikin mugun ɓacin rai yayunƙuro zaiyi waje tayi saurin shan gaban sa, fuskar ta cikin kalar tausayi tace" haba Abban Hanna! ya kuke abu kamar wasu yan drama, nayi imani duk inda MUNIBBAT take bazata wuce gidan su Aysha ba domin nan ne wajen zuwan ta, kar ma ka d'aga hankalin ka akan ta, bata da wani wajen zuwa da ya wuce ta dawo na santa farin sani wallahi ko awa baza tayi ba zaka ganta ta dawo, ai ta huro gaba ko wuka aka nuna mata akan ce taje yawon maula baza ta fita ba, yanzu kam za tayi hankali..."
" Ke bana son maganar banza zaki matsa min a hanƴa ko sai na maujeki? *Munafiki kawai* me yasa lokacin da take miki tambayoyi baki ce komai ba? ashe haka kika riƙe min marainiyar tawa? amma dan gulma dana shigo cikin gidan nan na zauna da kin fara lisafo min munanna abubuwa kuma kice duk ita ce, ke baki ji kunya ta ba ma ɗazu-ɗazu nan kika ce baki San wajen zuwan ta ba, amma yanzu kina wani ce min bata da gidan zuwan da ya wuce gidan su Aysha a ina kika san wannan bayan kince kullum canza waje take kamar kurciya? ki shirya abinda zan miki muddin na gano gaskiyar lamari zanje na dawo da ita yanzu ke kuma ki fara shirin amsar huƙucin ki *wawuya me kishi da ƴar cikin ta*... ya wani ingizata ta faɗa gefe ya tsallake ta ya wuce abun sa...
****
Kamar yanda ya saba yau ma tukin sa yake na ganganci, da yake ya rufe ko ina naci bazai gane abinda yake faruwa a wajen ba, a hankali Hajiya Nusaiba ta dube titti ganin yanda suke gifta ababan hawa cikin sauri yasa ta fahimci abinda ke faruwa, cikin taushin murya ta tace"" yaro na bana son irin wannan tukin please ka rage gudun nan kaji..."
Wallahi AN'NUWAR yana jinta yayi mata banza, sabida ta kira shi da yaron ta, hakan sai ya kona mai zuciya..
Allah sarki Nusaiba baiwar Allah sai ta sake maimaitawa nan ma shiru, ranta ya ɓaci domin sare ta san yana jin ta isakaci ne kawai, ɗaure tayi tace" AN'NUWAR!! yanzu dama akwai lokacin da zanyi maka magana kayi min banza a matsayi na matar baban ka? ashe yanda na ɗauke ku ba haka kuka ɗauke ni ba? to ka sani wallahi bazan ɗauka ba, tunda Ina da ikon huƙunta ka muddin kayi ba ɗai-ɗai ba, kayi na farko kuma shine na ƙarshe idan ka sakeyi min makamcin sa zai saɓamaka wallahi! ka rage gudun nan nace!.." ta faɗa a tsawace, cikin gigita yayi saurin saita nutsuwar sa domin ta farat ɗaya wani irin tsoranta ya ratsa shi, take ya hango wautar da yayi muryar sa cikin ladabi yace" ki gafarce ni Mama! insha Allah bazan sake ba..." har cikin zuciyar sa yayi maganar..
Ko kallo bai ishe ta ba, ta fara latsin² waya..
Yana ɗago kan shi ya taka wani uban burki cikin tsanannin kaɗuwa da zarani, amma ina motar taki tsayawa sai ji kake tauuuu....
Jama'ar dake waje suka miƙe tsaye kowa ka duba hannun shi a saman kai, yana zafga sallati yayi da wasu suke zubar da hawaye cikin tsananin tausayin ta tun kan ta dawo k'asa....
Comments
And
.Shared
Please
Mrs Abubakar ce
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.