Chapter 25

65 8 2
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar ce)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM

🅿 2⃣5⃣

Ban gane shi ba amma da alama mu yake tsayar wa, cikin taushin murya nace" an'a maka magana a can!.." yanda nayi maganar ne ina juya hannu abu ya birge shi, kawai sai yayi mun murmushi bai kuma tsaya ba...

Kawu ya dafe kirjin sa da yake masa zafi, cikin haki da gajiyawa ya fara tari! tun yana tsaye har ya durƙusa, ya jima sosai a cikin wannan yanayi...

Cikin damuwa ya dawo dakin, jiki a sanyaye ya ƙwaɓe kayan, daga shi sai gajeran wando ya tsaya, a hankali ya faɗa kan bed dinsa yana me nutsewa cikin katifa, a baiyana yace" me yake damu na ne? ya rabbi!!.." yana me shafo sajan sa..

Daddah ta dubi Anty data haɗa kai da gwiwa, cike da tausayin ta tace" yarinya ta tunanin me kike haka?..."

Cikin basarwa ta ɗago tana yake, Daddah ta zauna kusa da ita sosai, cikin kulawa tace" kina tunanin sauyawar baby ne ko?  me yiwa lokacin baya bata saba da irin kulawar da kuke bata ba, duk yanda akayi tunanin ta yana san dawo mata ne, kuma haka nake fata.."

Da sauri Anty ta dubi daddah idanun ta suka kaɗa, cikin raunaneniyar murya tace" ba wai bana farin ciki ba ne da samun lafiyar ba ne, a'a kawai ina hango yanda zata tafi ta barni, domin zata ji tamkar tashi daga barci ne, Daddah ina ƙaunar baby sosai dan Allah ki taimake ni ta zama mallaki na!!...." tayi maganar hawaye na bin kuncin ta...

Cike da tausayin ta tace" haƙuri zakiyi nusaiba insha Allahu kema zaki samu naki, ni a yanzu bani da iko kan yarinyar nan, maganar da nake miki duk wannan jimawar da tayi damu, har yanzu mahaifin ta bai fitar da rai da ita ba, kullum kwanan duniya sai yaje neman ta, hakiƙa yafiki son ta da ƙaunar ta, da kin sa  irin soyayyar dake tsakanin ta da Kawun ta, da baza kiyi  sha'awar raba su ba, ki duba ki gani sabida shaƙuwa da amanar ƙauna sunan shi yaki fita a bakin ta kasancewar ta me taɓin hankali, hakan bai yana ta tunanin sa ba! a ta dalilin rashin ta a kusa dashi, ya mayar da kanshi tamkar wani zarare, ya ajiye aikin sa me mahimaci ya zauna zaman jiran ta, karki sake ki shiga tsakanin su, muddin MUNIBBAT TA dawo haiyyacin ta nayi alƙawari sa hannu 'na zan ɗanƙamai yarinyar sa, kana 'na saka an'nuwar ya durƙusa ya bashi haƙuri, alƙawari nayi wa kai na ki cire ta a ranki tun wuri!!..."
[2/10, 11:19 AM] Mrs Abubakar ce🌹:
                 
                     

       


                
                 

Cikin kuka tace" hajiya dama kin san wacece ita? me yasa kika boye min? meyasa zakice na cireta a raina? sanin kan ki ne soyayyar da nake mata daga Allah nee! zanyi ƙoƙari nayi biyayya a gareki, amma bana jin har abada zan iya manta ta a rayuwa ta, a lokacin da kika mayar da ita ga danginta nima zan sake neman alfarmar sa akan ya bani ita zanyi masa alƙawarin abunda zanyi, dan Allah Hajiya karki hanani wallahi nima ina mata son so!..." cikin kuka take maganar..

MAN da tun dazu yana tsaye kuma yana jin su, ya ƙaraso cikin falo fuskar shi cike da tausayin Anty, ya zaune can kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace" Anty!! ba laifin Daddah bane! nine na hana a faɗawa kowa ko ita wacece, ita din ɗaliba tace! na san ta na san iyayen ta... daga nan ya ƙwashe labarin ta da yasani kaf ya faɗa mata, saboda tsananin tausayin ta  Anty kasa cewa komai tayi, ga tsanar matar Kawu da take ji har cikin ranta, a hankali tace" kinyi gaskiya Hajiya, dama kince halan a rayuwa ta ta baya bata saba da irin kulawar da muke bata ba a yanzu,  ina neman alfarma a gare ku dan girman Allah ko da ace ta warke ku bar min ita na wani lokaci, ina so ta san cewa mu masoyan ta ne kafin ta barmu!?.." ta ƙarke maganar cikin rauni...

Daddah za tayi magana MAN yayi mata alama da ido kan tayi shiru, cikin girmamawa ya kamo hannun Anty muryasa a tausashe yace" akan wannan ne kike zubar da hawayen ki ANTY!? nayi miki alƙawari ni da kai na zan roƙa miki Kawu ya bar miki baby haka yayi miki?.."

Duk da jikin ta ya mutu  haka bai hana ta sakar mai murmushi ba, a hankula tace" Allah yayi maka albarka yaro na!, dako har abada bazan mata da wanna ba!.."

Shigowar mu ne ya k'atse musu zance, da murna ta na shigo AN'NUWAR na biye dani a baya kaya niƙi-niƙi, kai tsaye jikin Anty na tafi na zaune ina nuna mata sweet din na, kallo na take cike da tausayi na tana min murmushi dole..

Daddah ta ƙarewa AN'NUWAR kallo cike da jin haushin sa tace" da izzinin wa  ka fitar min da yarinya?.."

Sororo yayi yana duban ta zuciyar sa babu dadi a dame yace" au sai an nemin izzini sannan za'a fata ita? a taunani na taimaka ta nayi.."

" To marar kunya rasa kunya beran tanka, wanda yayi gadon wahala, wallahi ko kusa ku alama kar na sake ganin ka da ita, wani yace maka tana buƙatar taimako? Lokacin da take buƙatar taimako ya wuce ai, daka gudu a tunanin ka ai zaje ka dawo ka tarar ta mutu, wato yanzu kaga  taza ma mutun shine zaka lalaɓo ka sake gigita musu yarinyar ko? to hawainiyar ka ta kiyayye ramata wallahi ka fita a ido na tun wuri! tunda uwar ka ta daure maka gindi sai kaje kayi iskacin ka akan wasa ƴan amma ba wannan ba kaji ni ko?..." Cike da masifa take maganar..

AN'NUWAR ranshi ya soso sosai da maganar ta, ya dube ta ranshi a bace bashi da yanda zan iya dole yace" Allah ya huci zuciyar ki Daddah, insha Allah zan kiyayye Allah ya bata lafiya.."
yana rufe bakin sa yayi saurin juye wa zaifice a ɗ'akin..

Da sauri Daddah tace" ameen in da zuciya ɗaya ka faɗ'a magulmaci..."

Man har zuciyar sa baiji dadin abunda Daddah tayi ma ɗan uwan sa ba, haka ma Anty amma basu da ikon magana, tsinkayo muryata  sukayi ina cewa" Kawu na! yau ma na ganka!.." sai na saki dariya me sauti...

A wani hautsine suka mayar da duban su gareni, kawai sai suka ga ina nuno MAN da yatsa, ANTY ta sauke a jiyar zuciya, Daddah ta shafa min fuska game da cewa" Allah ya baki lafiya baby!.."

Ameen suka amsa dashi ni kuma na cigaba da bare sweet dinna ina tarawa...

<==========°===========°>

Duk wani abu me saukin ɗauka, Kawu in yaci karo dashi a ɗakin watsi yake dashi, cikin mutuƙar tashin hankali da ruɗani yana hawaye da sumbato, yake watsu da kayan ɗakin,   Anty na, ta haukace ta firgice, cikin mutuƙar ruɗewa take cewa" dan girman Allah, Abban Hanna ka tsaya ka saurareni, kayi haƙ'uri ka sawa zuciyar ka salama, MUNIBBAT dinka zata dawo a ko wanne lokaci, wannan haukar da kake bazai amfana maka da komai sai tarin nadama..."

Cak ya tsaya yana duban ta zuciyar sa na tafasa, a mutuƙar harzuƙe ya shaƙe mata wuya kana ya buga ta a jikin bango ɗ'akin haɗin ya sake shake ta da kyau, idanun sa jawur yace" munafika ladama ta nawa kike so nayi? duk uban waye yajawo wanna wahalar? duk abinda ya faru kece sanadi! kin cuce ni SHAFA'ATU kin saka na aikata babban ƙuskure, yau da idanun na naga MUNIBBAT a cikin mota..." ya wugar da ita gefe guda ranshi babu dadi ya ɗaura.

dace"  kullum bana iya barci  sabida ita! walwala ta farin ciki na, kullum cikin tunanin ta nake, dai² da sa'a ɗaya ban taɓa mantawa da ita a cikin gidanan ba, na ajiye komai domin ta, amma abun bakin cikin shine ita ta manta dani ta manta ko ni waye! bata tunanin na, naji na aikata ƙusƙure amma me yasa zatayi min haka? da idanuna nagan ta tana dariya a gaban mota, ni gani rabo na dana dara har na manta kuma duk sabida ita, Ashe wahalar bazan nake...!"

Ya juya wajen Anty dake yashe a ƙasa tana aikin tari da murza wuya, tana ganin shi ta shiga ja  da baya tana zare ido, cakumo ta yayi yana mata wani irin kallo a hautsine yace" duk kece kika kulla komai! me yasa ma nake zaune dake har yanzu?..."

Wanna furicin da yayi shi yasa Anty sakin wani fitsari me zafin gaske, jikin ta ya dauki rawa...

Gaskiya sai naga ruwan comments zan ku samu ci gaba!   😕😔


Comments


Shared


Please



Mrs Abubakar ce

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt