_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*'''Wannan pagen naka ne Husaini 80k ban san sa wace irin kalama zanyi godiya a gareka ba, fatan alkhairi a duk inda kake...'''
🅿1⃣3⃣
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
Cikin tsananin gigita da furgici, ya fito yana me ɗaura hannu akai haɗi da sakin salati, jikin sa ya ɗauki rawa kamar mazari ya ma kasa ƙarasawa inda take, yayin da mutane da dama suke zagaye wajen da ta faɗo, jini kuwa sai zuba yake daga kan ta babu alamar numfashi a tare da ita...
Hajiya tuni ta jima da zuwa wajen, sabida tsantsar tausayin halin da yarinyar take ciki har hawaye take zubar wa...
Da taimakon wata baiwar Allah suka sakata a mota, jiki na rawa hajiya tace" AN'NUWAR ka shigo muje.." gani hankalin sa baya jikin sa yasa ta koma mazaunin tuƙi, shi kuma ya zauna a kujera me zaman banza, saboda ruɗewa har yanzu yaƙi ya kalle inda take...
Cikin ƙware da iyawa haɗi da nutsuwa hajiya ke tuƙin motar a haka har suka ƙarasa asibitin, cikin gagawa aka amshe ta babu wani ɓata lokaci kasan cewar AN'NUWAR sanan ne a wajen yasa aka fara mata aiki cikin hikima..
AN'NUWAR fatan shi ɗaya Allah yasa bata mutu ba, dan sai yanzu da ake ƙoƙarin fito da ita d'aga motar ya dube ta, sake tsinkewa yayi da lamarin gani yanda jini ke kwarara ɗaga kan ta, cikin kiɗima ya nufi Hajiya dake rawar ɗari yace" na shiga uku Mama, na k'ashe ta fa!..." ya faɗa a ruɗe..
ɗaurewa kawai take ita ma, ta yamutsa fuska cike da firgici tace" a'a AN'NUWAR bana jin ta mutu, domin na hango hawaye akan fuskar ta, kawai tana jin jiki ne muje ciki..." ta ƙarke maganar da kama hannun sa, suke shige cikin asibitin...
A bakin kofar room din da aka shiga da ita suke tsaya sai zagaye wajen suke, cike da fargabar abinda zasuji, cikin dauriya Hajiya Nusaiba tace" kana ji na? kayi maza ka faɗa wa Daddyn ku halin da muke ciki yanzu, musamma Hajiyar mu kar taga mun jima..."
Ko amsawa bai samu damar yi ba, wani doctor ya fito ɗaga ciki hankali a tashe, yace" please muna buƙ'atar jini yanzu nan, sannan ina son sa hannu ɗaya ɗaga cikin ku domin aiki za'ayi mata yanzu peshen din tana cikin wani mayuwacin halin a yanzu, in ba'ayi mata aiki ba za'ayi rasata a ko wanne lokaci..."
Sabon firgici da tashin hankali ne ya baiyyana akan fuskar su, cikin kiɗima Hajiya ta waigo ga AN'NUWAR da yake jin cikin sa nayi mai wani irin juye, tace" ya zamuyi yanzu AN'NUWAR ?..."
Bai bata amsa ba, yayi saurin ciro wayar sa ajihon sa, number Big man ya fara kira, cikin tashin hankali yake mai bayanin komai a dabar-barce, sam bai fahimce shi ba, dan haka ya tambaye shi yanzu suna ina, jikin sa na rawa ya faɗa mai inda suke a halin yanzu da kuma abinda ake bukata, gani nan zuwa kawai yace kana ya kashe wayar...
Tun kafin ya iso yayi waya da gida, duk ya gaya musu halin da ake ciki, yana zuwa yace yana son gani doctor din ai ko yazo, cikin hikima da iya magana yace" doctor brother na yayi min bayani komai ina buɓatar karin bayani ɗaga gare kai yanzu a wannan mataki take?.."
" A halin yanzu tana kan mataki na ƙarshe ne domin jinin dake zuba a jikin ta yaƙi tsayawa, minyi iya bakin ƙoƙarin mu amma abun yaci tura, dole ne sai anyi mata aiki a akan ta dan tayi mumunar buguwar da muke tunin zai wuya ko ta tashi, ta dawo normal..."
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.