Chapter 44

26 1 1
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

'''bani da abinda zan baki na saka miki, tabbas ke maƙociyar arzikice kin cancanci yabo ta ko wanne gefe, 'na gode na gode sosai Allah ya biya miki buƙatunkin 'na alkhairi, dan Allah ina neman alfarmar ku duk wanda yake b'in wannan novel dinnawa ya tayani godeya wajen MAMAN IMAN OR ALMAN, AND BASHIR ALLAH ya kara danƙon zumumci na gode...'''

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 4⃣4⃣

Nayi kasa da kai na gabana yana tsananta faɗuwa, Nafisat tace" mommy ga ƙawa ta munibbat  wace nake baki labarin ta kafin muje wurin daddy! Munibbat ga mommy na!..."

Tsuru-tsuru nayi da idanu cikin rawar murya nace" Hajiya ina wuni! kun sauka lafiya?.."

Shiru tayi tana so ta tuna fuska ta amma abun ya gagara, siririn tsaki tayi kana tace" lafiya kalau! ya akayi kika san zata dawo yau? dama kin taɓa zuwa nan ne?.."

Ciki na ya ƙulle, zufa ta shiga karyo min har ga Allah tsoron matar nan nake kamar me!!..

" Mommy!!!.." cewar Nafisat cike da shagwaɓa...

Kallon tayi da alamar tambaya kana tace" Munibbat ko? Ƴar waye ke, ma'ana waye baban ki?..."

" Mommy! marainiya ce fa! a hannun Kawun  ta taso!.." Nafisat ta faɗa gudun kar a wulaƙanta mata ƙawa...

" Shi Kawun nata waye shi to?..."

" Mommy! pls!!!, Munibbat kinga wannan shine BIG MAN din mu! kinyi mamaki ko ? Malam Haidar yaya na ne! sai Ya ANUWAR! dama duk sun san da zamaki ganin ki ne kawai basu taɓa ganin ki ba sai yau! Mommy ita fa ƴar wan Antyce!..."

Ta faɗa tana duban Mommy da ta kafe ta ido jin abinda tace, dariyar MAN muka ji cike da nishaɗi yace" Auta banda  shirme irin naki, ai mun santa mu ta jima a gidan nan sosai!..."

Na zuba mai ido ina duban sa soyayyar sa nayi min wani irin suka a zuciya, nayi murmushi nace" ni zan koma can Nafisat!.." cikin sanyi nayi maganar...

Cikin siririyar muryar sa fuskar nan a shagwaɓe yace" Mommy karya ne ba wani ƴar wanta mahaukaciyar nan ce fa!!..."

Dum gaba na ya faɗi, na daure ban tsaya ba har 'na kai ƙofar fita naji muryar Mommy na cewa" kallon sani nake mata! amma wannan batayi kama da wace na bari ba..."

Man ya sauke wata nauyayiyar ajiyar zuciya kana yace" Mommy bari na shiga ciki!.."

Dai-dai fuskar ta ya sunkuyo kana ta sakar me kissing a goshi, haɗi da cewa" Allah yayi maka albarka babban mutun..."

Ameen yace yana murmushi ya biyo baya na da sauri, Allah Allah nake 'na shige shashin Anty caraf naji ya danƙo mun hannu nayi saurin juyowa a tsorace, tamkar leɓen bakina jira yake nace" MAN!!.."

Haɗi fuska yayi yana nazari 'na kana yace" jeki!..." yana matsa mun a hanƴa...

Cikin sanyin murya nace" kayi haƙuri kai ma dan Allah?..."

A tsanake yace" me ya faru kuma?.."

Shiru nayi ina tunanin to ko bai sani ba? tambayar da nayiwa kai na kenan, daga bisani kuma na sauya akalar zancan nawa da cewa" in ba damuwa ina so na koma gidan mu!.."

" Wani abu akayi miki a nan d'in?..."

" Ina son komawa ne wajen Kawu na.." cikin rauni nayi maganar...

" Ok ki faɗawa Daddah to..." ya faɗa fuskar a haɗe..

Shiru nayi ban sake magana ba, amma a zuciya ta daɗi nake ji yau gani ga MAN dinna har muyi magana me tsayi...

*" Har yanzu kina nan akan bakarki  na san ki aure ANU?.."*

D'um kirjina yayi wata irin faɗuwa, nayi maza nace" a'a..."

" a'a me?.." ya tambaya yana kare mun kallo, "Ya kuka yi da aminiyar taki?.."

Shiru nayi domin bani da amsar tambayar sa, gajiya yayi kana yace" a karo na ƙarshe Daddy zai tambayeki saura kuma naji wannan bakin naki yace wani!..." yana rufe bakin sa Nafisat na fitowa idanun ta fal hawaye...

Ban jira naji me zata ce ba nayi saurin shigewa ciki, a jikin sa ta ƙwanta cikin shasheƙar kuka tace" Ya MAN! bana son wannan halin na Ya ANU! ya dage sai zuga Mommy yake har sai da ta mareni kawai 'dan na kare ƙawata..."

" Shittt bana son jin komai Auta, kiyi haƙuri kinji wataƙila kema kinyi kuskure ne haka kawai Mommy bazata hukuntaki ba..."

" Banyi komai ba 'fa, haka yace..." "Nace miki bana son jin kinji?.."

Shiru tayi zuciyar ta nayi masa zafi...


Bayan ƙwana biyu, lafiya kalau muke zaune da kowa a gidan, su Mommy sun huta sosai, tazo har ɗakin Daddah ta bata haƙuri, Daddah sam bata da roƙo a take tace ta yafe mata, haka kuma bata gayawa kowa abinda ya faru ba,  Anty ta zamo daga kan kujera cikin biyayya tace" Maman Auta!  kiyi haƙuri kema akan abinda kika tarar..."

Wani irin daɗi ne ya kama Mommy, cike da nuna ita wata ce tace" No Antyn su! ai ke zan bawa haƙuri, domin nayi saurin yanke hukunci cikin rashin sani, kiyi haƙuri kema!..."

Daddah ta karewa Mommy kallo, ganin yanda take ta wani murza zoban zinaren dake hannun ta tace" lafiyar ki kalau Amina?.."

Cikin sauri Mommy tace" Eh me kika gani Hajiyar mu?.."

" To saki hannun haka kar kiji rauni!.."  da murmushi akan face din ta ida zancen...

Murmushi Mommy tayi kana tace" HAJIYAR MU bari na leƙa ɗakin yaran nan..."

Ok kawai tace, ita kuma ta fice a ɗakin...

Shiru nayi ina tunani halin da Kawu na yake ciki yanzu, maganar MAN ce ta faɗo mun na lumshe idanuna zuciya ta fari ƙwal...

Idanun ta sun kaɗa sunyi jawur dasu, cikin tsananin ɓacin rai tace" me? kana nufin mahaukaciyar yarinyar nan itace har yanzu tana cikin gidan nan basu mayar da ita inda ta fito ba, ga wani wawan zance da kake  wai soyayya da MAN abun ma babu daɗin ji! yanzu dama akan haka ne suka rufar maka da mari?..."

" Mommy na sha wahala sosai da bakya nan, ba yanda banyi da mutanan ba akan kar su sake dauko yarinyar nan amma suka ƙi, a karshe ma sai mari 'na sha a hannu Dadda..."

Mommy ta miƙi zuciyar ta na azazala mata, ANU yayi saurin dawo da ita zaune, cikin hikima irin tashi ya ɗurata aka burin sa 'na aure na daga baya yayi min sakin da babu dawo ba, bare 'na sake kasancewa a cikin a halin su...




Comments



And


Shared

Pls



Mrs Abubakar ce😘😘

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now