Chapter 34

36 1 0
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 3⃣4⃣



"" Baby na!! kece da gaske?..." ta ida zancen da ɗago min fuska, muna haɗa ido da ita tayi min wata wawuyar runguma...

MAN gaba ɗ'aya ya kasa cewa ko ƙaza, kawai kallon mu yake, Dadda kam ta haɗe hannuwan ta waje guda sai aukin murmushi take.....

A ranar naga gata, naga yanda ake nuna kulawa, a cikin su ko wanne gwanine wajen nuna min ƙauna....

Kamar yanda suka tsara, duk ranar Monday ANNUWAR ne yake kaini makaranta, in aka tashi MAN yazo sauran ranaku kuma MAN ne yake kaini...

Sabowar rayuwa, saban farin ciki da nutsuwa gaskiya jama'ar gidan su MAN mutanen kirki ne, sun nuna mun gata sun bala'in shagwaɓ'a ni a yanzu ko yatsa na ka taɓa saina saka maka kuka, duk cikar gidan nan sai sun fito wani lokaci na saka dariya, haka zasu ta bina kamar zasu dake ni, amma fa da naje wajen ANTY na! na tsira! ina jin dadi rayuwa dasu sosai....

A ɓangare ɗ'aya kuma ina ƙewar Kawu na kamar me, ganin ba sa son bacin raina yasa nake ɗ'anne wa har sai na kebe waje guda sannan nayi kuka na...

Soyayyar mu  da MAN kullum kara haɓ'aka take, mo sa yaushe sa irin kalaman sa yake gaya min, ina jin don shi sosai a raina, amma van taɓa furta mai ba..

Shiru wajen ya ɗauka tamkar babu mutane a cikin sa, cikin wata zazzaƙar murya yace" BEBBY NE!!! har yanzu fa banji kince komai kan soyayyar mu ba, shin kin amince dani a matsayin wanda zaki ƙare rayuwarki dashi? ko har yanzu baki gama tunanin ba?..."

Shiru nayi ina wasa da yatsun hannu na, zuciya ta na saƙamin abubuwa da dama, cikin sarƙewar murya nace" ina so na tambaye ka wani abu! Ahmm dama nace ya kukayi da Aysha?..."

Cikin rashin fahimta yace" wacece haka?.."

" AYSHA Musubahu Aliyu mana ɗalibar ka!..." na faɗa zuciya ta na bugawa, tsorana ɗ'aya kar naji abunda raina yake saka min."

" Ohh wanna wai? yarinyar tana da kirki sosai, ta taimaka min a lokacin da nake neman gidan ku, duk wani bayyani ɗaga gareta na same shi, gashi yanzu ta fara mayar da hankali akan karatun ta, da farko bana son yarinyar gaskiya, amma sabida ta zamu wani babban sanadi a rayuwa ta, tana dan birgeni amma fa kaɗ'an..."

Lumshe idanu na nayi hadi da ɗ'anne zuciyata da ƙarfin tsiya,  a hankali nace" to WACECE AYSHAN DA KAKE AIKOWA DA SAK'ONIN IRIN NA MASOYA!..??"

Wani makirin murmushi ya saki game da shafo sajan sa, kana yace" AYSHA!!! shine suna da muke kiranta dashi lokacin da bata da lafiya, babby  kuma shine inkiyar ta, ina fatan yanxu kin gane?..." ya faɗ'a yana waro min idanun sa...

Na kasa jurewa, harshena yayi min nauyi, maƙoragona ya bushe, zuciya ta na tafasa a hankali na mike zan wuce ciki, yayi saurin riko min hannu ido cikin ido yace" baki gane ba ko?..."

Wani irin kishi nakeji a zuciya ta, na sake ɗannewa haɗi da daga mai kai alamar Eh, murmushi yayi min kana yace zauna..."

Ba musu na zauna amma fa kasa nake kallo, cikin hikima da dabara ya shiga bani labari na, da dalilin saka min sunan tamkar a novel haka naringa jin sa,
yace" tun daga ranar da kika shigo rayuwa ta na fara sanki! shin ke bakya jin irin abunda nakeji a raina? ina ji in na rasaki nima tawa rayuwar tazo ƙarshe, Ina miki wani irin so wanda ban taɓ'a ganin wanda yakeyi miki irin sa ba,  zan iya sadaukar da rayuwata domin ki, muddin zaki kasance a cikin farin ciki to tabbas zanyi haƙura da nawa farin cikin dominki! karki nauyin baki MUNI in kin san bakya so na tun wuri ki shada mun, kar mu wahalar da juna mu! KINA SO NA MUNIBBAT!!???..."

~KIN DAUKA SOYAYYA TA A GARE SHI WASAN YARACE?  INA MASA SON SO, SOYAYYAR DA BABU IRIN TA,INA MUTUWAR KAUNAR HAIDAR DAN ALLAH IN KIN SAN BAZAKI MIN ADDU'A YA ZAMU NAWA BA, KARKI SAKE CEWA KOMAI PLEASE!...~

Maganar Aysha ta dawo min cikin kaina tamkar yanzu take gaya min, a tsorace na kalle shi idanu sun ciciko da ƙwalla, na mike a fusace zan gudu yayi saurin juyo dani gaban sa, ƙoƙari ƙwacewa nake naji yace" _na fahimta MUNI, bakya so na ko? shi kike son gaya mun ko? ba komai ni bazan takura miki ba, abinda kike so shi nake so, amma karki cutar da kanki please!! shi so ba'ayin sa dan dole, na barki lafiya!..._"

Galala na tsaya ina kallon sa zuciya ta nayi min wani irin zugi, na kasa cewa komai illa ƙura mai ido da nayi kawai har ya ɓacewa gani na, a hankali na sulale a wajen sai haki nake kukan ma yaki fitowa bare na samu sausaucin a zuciya ta...

Duk wani abu na fashe wa dake ɗakin sa sai da MAN ya rotsa shi, cikin ƙunar zuciya da azababban kishi, idanun sa sun kaɗa sunyi jawur, ya faɗi a wajen yana dafe saitin zuciyar sa, da ƙarfi ya buga kan shi da jikin garu, ji kuke tauuuu!!!..."


A haka na lalaɓ'a na koma ciki, nayi sa'a ba komai a hanyar na wuce dakina, kye nayi ma ƙofar da kyar na samu na isa kan bedroom dinna, numfashi na yana sama da kasa, jikina ya bani MAN dinna baya cikin hayacin sa a yanzu, na mike tsaye cikin rashin sa'a na zame ban tsaya a ko ina ba sai a ƙ'asa kaina ya bugu  da gefen gadon ji kike kauuuu!....


Comments



And



Shared



Please



Mrs Abubakar ce

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz