_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 3⃣9⃣
" *Ita din yata ce Eh yata ce nace miki! kin ɗauka bata da kowa a duniya? ko an gaya miki bata da gata ne? ba ita take soyayya dan kuɗi ba kece kika haukace domin kuɗi, tun wuri ki kauce a hanya ta, ko uwarki bata isa tayi abinda kikayi ban hukunta taba, alaƙar mu da MUNI ta jini ce ba wai irin taki ba ta ƙawar uwa, shashar yarinyar kawai akan wata bazan soyayyarki da bai san kinayi ba zaki zo kina ɗaga mutane murya wai kenan me masoyi!, kin san yanda muke fama da ita akan shi kuwa tana ƙi? tana son MAN fiye da yanda kike son shi amma taƙi yarda dashi sabida ke! wallahi azeemin da na san kece Aysha da kike saka min yarinyar a damuwa, da ko hanyar gidan nan bazaki sani ba bare ki shigo shi..."*
Kuka nake sosai maganganun ANTY na dawo mun cikin kai, *yata ce alaƙar mu da ita ta jinii ce*
Aysha ta gigice, da irin huƙuncin da ANTY ta yanke mata, maganganu ANTY sun sosa mata zuciya sosai, ta runtsi idanun ta hawaye na zuba a hankali ta zube akan gwiwoyin ta, cikin mutuƙar dana sani tace" kiyi haƙuri ANTY, banyi haka dan na bata miki raiba! na kasa jurewa!..."
Tausayin ta ya kamani, cikin ƙarfin hali nace" kiyi haƙuri ANTY dan..."
" Ki min shiru baby! bana so ki sake cewa komai a nan!..."
Da gudu nayi ɗaki na, kuka na yana kara tsanan ta, tabbas tun da nake a duniya babu wanda ya taɓ'a gaya min magana me zafi da ciwo irin ta AYSHA ba, na shiga rera kuka kamar me waƙa...
Aysha ta ringayiwa ANTY naci akan sai tayi haƙ'uri, har sai da ta sauko a tsanake ANTY tayi mata bayani halin da ake ciki yanzu, ta kara dacewa" MUNI ƴata ce ta ciki na, domin yarinyar Yaya nace ita, ita kadai ce damu ko ita bata san alaƙar mu da ita ba, duk kan mu nan MAN muke so ta aura, ita ma shine zaɓin ta gobe insha Allah zaa kawo ƙ'arshen wannan matsalar ki shirya kayan ki yau zaki komai gidan ku..." tana rufe bakin ta ta mike ko a jikin ta...
Aysha tayi kuka kamar zata mutu ganin babu sarki sai Allah yasa tayi shiru ta shiga bawa zuciyar ta haƙuri, amma taji daɗi yanda MUNI ta nuna mata ƙauna duk da basa tare, gashi ita kuma ta ci mata mutunci...
" Kiyi haƙ'uri ƙawata ni sam ban san halin da ake ciki ba, ANTY ta gaya min komai kiyi haƙ'uri kinji!.." cewar Aysha dake tsaye akai na..
Na share ƙ'walla ta cikin muryar kuka nace" ba kiyi min komai ba Aysha, duk wani abu da kikayi kinyi ne akan abinda kike so, to ni banga laifinki ba, ki ƙwantar da hankalin ki gobe insha Allah MAN zai zamo naki haka yayi miki?..."
Ta sauke ajiyar zuciya tace" a'a MUNI ni yau zan tafi, na sani MAN shine mafarkin ki, me yasa kike so ki sadaukar min da farin cikin ki? shine zaɓ'in maman ki kaka Daddah, haka shima ke yake so, to me yasa ni da ba'a san inayi ba zan shige tsakani, a'a MUNI bazan raba ku ba nima Allah ya bani nawa!..."
Tausayi ta bani nace" Ina so ki jira zuwa gobe kinji ƙawata! bana so ki sake cewa komai, na fi kowa sani kina mutuƙar ƙ'aunar MAN ki bani zuwa gobe..."
MUNIBBAT da kan ta roƙi ANTY ta bar AYSHA zuwa gobe...
Washe gari, gaba ɗ'aya kowa na gidan yana zaune a cikin tanƙameme palo, babu wanda yayi ƙ'aramar shiga ko ka kalla ba baya ba, Daddah da kowa ita yake sauraro ta dube MAN da manya idanun ta, cikin isa tace"" MAN kai muke sauraro!!.."
Ya saki murmushi yana sosa kya a ƙunyace, yace" a'a Daddah ni a shirye nake da duk abinda aka yanke, fatana ɗaya shine a tambayi yarinyar abinda take so!..."
Daddah ta ƙura mun ido har sai da na tsora ta kana tace"" MUNIBBAT! ke muke jira!.." da sauri na kalle AYSHA dake kallo na cikin tararabi, ANNUWAR yayi gyaran murya nayi saurin kallon sa...
ANTY tace" baby! dake fa ake!..."
Rintse ido na nayi abubuwan da suka faru dani a baya suka shiga dawo min tamkar yanzu akeyi, a hankali na furta"" *kuyi haƙuri da abinda zan ce, tabbas ina mutuƙar ƙaunar jarime na, domin shine cikar burina, ina son shi sosai bana ji ko nan gaba akwai wanda zan so sama dashi, na kalle MAN ido cikin ido nace kana sona kamar yanda nake son ka? zaka iya sadaukar min da soyayyar ka? kana jin abinda nake ji a zuciya ta MAN?..."*
ANNUWAR ya zuba mana idanu cikin ƙunar zuciya da mamaki abinda muke, domin shi sam bai san akwai wata alaƙa tsakani na da dan uwan shi ba...
" '''Ina son ki!! ina kaunar ki, ina ji a jikina bazan iya rayuwa ba tare dake ba MUNI, ina miki son so! naji dadi sosai yau a gaba jamaa kike baiyya na min abinda na jima ina son ji daga gareki, amincewar ki kawai nake jira shin zaki aure ni!?.."'''
A hankali na miƙe tsaye hawaye na zubo min, na share cikin ƙarfin hali nace" ina so kayi mun alfharma ɗ'aya tak MAN! *Ka manta ka taɓ'a son wata me suna MUNIBBAT a rayuwar ka, ma'ana ka manta dani!.."*
Dumm gaba jama'ar waje Ya faɗi zuciyoyin su sukayi baƙi, ran su ya ɓaci MAN ya mik'e a zuciye...
COMMENTS
AND
SHARED
Please
Mrs Abubakar ce
DU LIEST GERADE
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Kurzgeschichtenlabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.