_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*
'''A gaskiya bani da abinda zance muku sai godiya da fatan alhairi a rayuwar ku, 80ks da N. Yareema, Ina mutu'kar gideya a gare ku Allah ya zab'e muku mataye na gari, na gode k'ware da gaske.'''*Dentist Aseeya, ke ta daban ce bana haɗaki da kowa, kalaman baƙi na sunyi kad'an wajen miko sakon godeya ta a gareki, Allah ya cika miki burinki duniya da lahira, Allah ya baki abinda kike nema, ameen Allah ya baki miji na gari me sonki da kaunar ki wanda zai ƙaunaci kowa naki, na gode na gode ƙware da gaske..*
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿2⃣0⃣
WACECE Hafsat?
Hafsat ɗiyar aminiyar Mommy ce, wace su kayi makaran ta ɗaya tunda matakin farko har zuwa ƙarshe.
murjanatu macece me tsatsauran ra'ayi, yar masu kuɗ'i ce gaba da baya, ta ko wanne bangare ta gaji arziki, iyayen ta sun shagwaɓa ta ainu tun bata san menene duniyar ba.
ta taso da wani irin hali wanda gaba ɗaya iyayen ta ne silar ta shigar sa, duk iskaci da zatayi ko rashin kunya a tsakani uwar ko uban babu wanda zai kwaɓ mata, gaba ɗaya ma'aikatan gidan ta adabi rayuwar su kusan kullum sai ta saka ana kore mutun biyu ko uku, a haka tayi rayuwar ta a cikin gidan su har girma yazo mata...
Mommy ita ma gwana ce a wajen kyarar ma'aikata da nuna musu su ba komai bane a face bayi, rashi nasarar ta ɗaya shine Daddah duk iskacin da take tatawa Daddah bata sani ba, sau tari ta sha kamata tana wulaƙanta mata bayin Allah, a gaban idanun su take ci mata uwa tass take mata sannan kuma ta gindaya mata sharaɗu haka kuma dole ta bi su, Daddah macece me haƙuri da san taimakon na kasa da ita, bata da kyashi ko kaɗai, haka ma yaran ta guda biyu da Allah ya bata, mijin ta ya mutun tun Abdulazizi yana ƙaramin, bata da kowa sai ƙanwar ta mahaifiyar Mommy wace bayan rasuwar mahaifin su Abdulazizi ita ma Allah yayi mata rasuwa, bayan ta mika amanar ta a hannu yayar ta, tun farko Mommy ta taso a sangarce iyayen ta suna da hali sosai, sun nuna mata gata amma sun bata tarbiyar da ilimin boko da na adinni, kun san ace albasa batayi halin ruwa ba to haka mommy take..
Zaman ta a gidan Daddah gani shi take tamkar zama a cikin kurkuku, domin duk tsiya da bala'in ta Daddah bata raga mata, a hankali ta fara taushi...
Zaman ta da murjanatu tamkar kara rura mata wutar kiyayyar talakawa ne, aminene na ƙ'arshe, duk da murjanatu ta kerewa Mommy a fagen wulaƙanci, murjanatu bata da mutunci ko kaɗai, duk wanda yayi gigin shigar mata gaba zuwa ɗaya take mai ta wuce wajen, Mommy kam bata da wannan damar domin Hajiyar mu ta tsare ko ina...
Wannan dalilin ne yasa Daddah ta aura mata Abdulazizi, ba dan komai ba sai dan tana so Mommy ta gane gaskiya, ko Allah zai sa ta shiryu, sai akayi sa'a dama suna son junan su ba matsalar komai akayi biki aka gama...
Murjanatu sabida tsabar raini da isa, cewa tayi ita bata jin har yanzu akwai sa'an auren ta a cikin rangaza, daddy din ta da kan shi ya nemo mata mijin aure ɗan aminsa, me dai-dai da irin ra'ayin ta sai dai inda giro ke saƙa, shi baya wulaƙaci haka bama ya kyamar kowa, shi dai bar shi da zama waje guda, baya shiga mutane ko kaɗan ɗindinan walahairan yana ɗaki a zaune, muskilacin sa yayi yawa sosai bashi da surutu bare hayaniyya, ko da mahaifin sa yazo mai da maganar aure cewa yayi inda tayi kawai ayi auren babu damuwa, ko sau ɗaya bai taɓa zuwa zance gidan su murjanatu ba har akayi auren, lokacin Mommy tana da tsohon ciki itace babbar kawa da ita kayi komai har amarya ta tare a gidan ta...
Da farko ta ɗauka tsananin mulki ne da izza yasa bai cika mata magana ba a hankalin kuma ta fahimci ko shi waye, domin duk lokacin da zata shiga ɗakin sa, sai da ta same shi da littafin adinni a hannu, in bashi ba kuma waya..
Da yake ance duk mugun halin na miji sai dai in ba'a haɗa shi da mace ba, zuwa murjanatu rayuwar sa tamkar samun canji ne, cikin shekara ɗaya ta sauya shi, ya zama me surutu yana murmushi ya kan shiga cikin mutane har ya ɗauki lokaci, iyayen sa sunji dadi sosai sabida canji da ya samu ta dalilin ta yasa suka mata kyautar maƙudan kuɗaɗe, gaskiya su sake shagwaɓa ta, masu aikin gidan ta ƴan kasar waje mahaifin ta ya kawo mata su daga ture, yan channa ne irin fararen matan nan, suna mata biyayya sau da ƙafa, duk da haka basu tsira ba in abun nata ya motsa mata uban su take ci, tana juya kuɗi yanda take so, domin mijin ta ya sakar mata ga na uban miji ga na baban ta, ita kan ta tada manya kudaɗe bana wasa ba, sai ta sake azawa kan ta girman kai kamar bala'in, hata Mommy bata ragawa ba in bata ga dama ba Mommy ko zuwa tayi sai tace ace mata baza ta samu ganin ta ba, duk tsiyar Mommy da iskanci ta murjanatu ta shayen ta....
To me karatu kar ku manta mommy fa ba baya wajen arziki da mulki, tana da kuɗi sosai haka mijin ta ma yana dashi, a irin ma'aikatan gidan murjanatu ne ita ma aka kawo mata guda biyar masu kula da ita, in baku manta ba zuwan Hajiya Daddah tasa aka sallame su, Mommy tana bala'in so tayi rayuwar shakatawa amma Daddah ta hana...
Sai da murjanatu tayi shekara biyar da aure sannan ta haifi ƴar ta mace, kyakyawa da ita domin uban ta tayi sak, murna a wajen su ba'ace wa komai, yarinya ta sha gata fiyya da zaton ku musamma aka ɗauko masu kula da ita d'aga kasar waje, rayywar Hafsat abar dubawa ce sosai an sangar ta ta, duk girmaka da mulki ka in Hafsat tace bata son ka ana gama da kai, malaman ta duk haƙuri suke da ita a gida ake zuwa koya mata karatu sabida gata ko waje ba'a barin ta zuwa, da sauki tunda tana da ƙoƙari wajen fahimtar karatu amma fa kusan ko yaushe ana sauya mata malamai, d'aga wannan sai wannan, mahaifin ta yana ƙoƙari sosai wajen gani ta ƙware a fannin ilimin adinni, shi yasa ko ta dawo cikin gida yake sake sata a gaba har ta iya kana ya sallame ta...
Gaskiya sun bala'in shagwaɓa ta, bata da kunya ko kaɗai duk girma ka zagewa take ta ci maka mutunci, a rayuwar ta babu me mutunci sama da iyayen mahaifan ta, sune kaɗai take ragawa abun ya zo da sauki baa barin ta fita da bamu san a iya ina abun zai tsaya...
Haka take rayuwar ta a cikin gidan su, har ta girma ta isa aure amma kullum kara iskacewa take, abinda iyayen nata Basu sani ba a cikin ma'aikatan nata akawai wata budurwa baturiya me SUNA Ariyna, tataciyar iyar duniya ce ta bala'in ƙwarewa a harka mata, duk wani salon shiga da yaudara ta san shi, bata da aiki kullum ribatar Hafsat take da nuna mata yanda rayuwa take tafiya yanzu, amma abun dadin shine Hafsat babu na miji a gaban ta bare kuma mace, wani bin ma da Ariyna ta fara mata irin wannan maganganun sa ta saita mata hanƴa, sau tari ta sha kawo mata films irin na yan duniyar nan ta ajiye mata, sai ta saka ta zata kalla sai taga abun da bata son kallo, kusan sau biyu tana marin Ariyna akan abinda take mata...
To Ariyna ba ita kaɗai bace me irin wannan ɗabi'ar a cikin su, kun san rabin yan mata haka suke, da zarar dare yayi basu da wani aiki sai na neman junan su, ita kaɗai ce ta daura ranta akan Hafsat...
Babbar ilar su kenan
A yanzu mommy ta samu sake sosai wanda murjanatu har gidan su Mommy ta taɓa zuwa sau ɗaya shi ma kuma daga tsaye- tsaye...
Zuwan Mommy gidan murjanatu a nan ne ta ga Hafsat duk da haduwar su ta farko rashin kunya ce ta shigar tsakani su, tunda Hafsat take bata tabayi ma wani rashin da mom din ta tsawar ta mata ba sai akan Mommy nan ta gane Mommy tana da daraja kenan, jiki a sanyaye ta wuce ciki duk da haka bata bawa Mommy haƙuri ba...
Tun lokacin Mommy ta ɗaurawa ranta cewar Haidar ya samun matar aure...
Shiko Haidar ya taɓa kai Mommy gida akan hana su shiga ƙarshe sai cewa akayi wai tace bazata gana da kowa ba yau, wannan abun yayi mai ciwo sosai a rayuwar sa tun daga ranar bai sake zuwa ba ko da wasa, da Mommy ta fahimci haka sai take zuwa da AN'NUWAR, a hankali suka saba shida Hafsat, shine mutun na farko da ya fara ɗaukar ta ya fita da ita daga cikin gidan ba tare da ana mai shamaki da komai ba, shi ya fara koya mata yawo kallace-kallace, a hankali suka shaƙu amma ba wai can-can ba....
Zamu dawo labari a next chapter
Comments
And
Shared
PLEASE
Mrs Abubakar ce
VOCÊ ESTÁ LENDO
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Contolabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.