_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣7⃣
Bayan ƙwana biyu, a yanzu kam mun shirya da MAN dinna soyayya muke ta kece raini, a gaba kowa nuna min so yake amma banda mutun ɗaya, lokacin da muka samu hutu a makaranta na tafi gidan Kawu 'na, nayi mamaki sosai da nayi araba da irin gidan da suke ciki a yanzu, ga ma'aikata sai shige da fice suke, ban san yanda akayi ba amma mata biyu na tarar a gida kuma gaba dayan su matan Kawu ne, sun amsheni hannu bibiyu ko wace sai nan dani take, ga su Bishira an zama yam mata yanzu, itama sai murnar gani na suke, duk da bana gidan amma dakina daban yake an zuba mun komai na jin dadin rayuwa..
Murmushi nake nima kamar yanda yake, cikin sanyin murya nace" Kawu na ina ANTY na!!?.."
Yace" taje gidan su, ina tunanin ta kusa dawowa..."
" Yaushe kayi aure Kawu!.."
Murmushi yayi yanzu kana yace" na jima sanyin idaniya ta, bana jin kinyi wata biyu da barin gidan, nima na dawo nan anguwar da saban aure amayar ce ma bata jima ba..."
Kallon shi nake zuciya ta ba dadi nace" ina so naje wajen ANTY Na!!.."
" Ok ki shirya zuwa anjima zanyiwa musa magana ya kai ku har da su Bishira!!.."
" To kawai nace, ina shirin mikewa yace" me yake damun ki yarinyar Kawu?..."
" Ba komai!.." nace cikin sanyin jiki dana zuciya...
Shima rabuwa yayi dani, har na fice a falon...
Ko da bai fad'a min ba d'aga ganin yanayin da ya amsa min na san akwai matsala, zuciya tana bani ba dadine yasa ANTY tafiya ba, duk yanda akayi akwai matsala me yasa ya kara aure bama mata d'aya ba har biyu!? kai na ya kulle na rasa gane mafita...
Bishira ce ta shigo d'akin, kallo na tayi cikin sanyi tace" ANTY MUNI! kizo ANTY RABI tana kiran ki!..."
Cikin rashin fahimta nace" wacece haka!?.."
" Matar Abba ce!.." ta bani amsa a dan tsorace..
Hannun ta na kama had'i dacewa" muje to."
Nokewa tayi hadi da yin kasa da kanta tace" a'a kawai kije ni zanyi wani aikin ne!.."
" Dole ne ki rakani tunda ba sani kan gidan nayi ba..."
Hawaye idanun ta ne ya digo a hannu na, cikin mamaki nace" ke lafiyarki kalau kuwa? kukan na menene kuma?.."
Rungume ni tai kukan ta na tsananta tace" ANTY dan ALLAH ki tafi ke kadai in naje zata dakeni!.."
Ido na waje nace" duka kuka!??.." cike da mamaki..
"Eh duka ANTY tun daga ranar da Abba ya kawo ANTY Rabi a matsayin mata...
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.