_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*_Dentist Aseeya wannan page naki ne har illa yau, Allah ya matso mana da nesa kusa musha biki_
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣1⃣
Yau gaba ɗaya gida ya hargitsi da shirye-shirye, ma'aikatan gida sai hidima suke, cikin sauri da ƙware wa ko wace burin ta shine tayi abinda aka umarce ta dashi....
Mommy da wuri ta shirya taci uban ado, ga gwala-gwale da danƙama su a wuya da hannu, in kuka ganta tamkar sarauniya gaskiya mommy yar gayu ce ta ƙarshe, fuskar ta babu wani hayaniyar ƙwalliya amma sai sheki take da ƙyalli tamkar wani yad'i, Mommy kyakyawace ta ajin karshe, cikin ƙasaita take tafiyar ta kamar bata son taka kasa, a hankali ta isa shashin Dadda bakin ta ɗauke da sallama, kasa-kasa Daddah ta amsa ta, ta saki wani mayaudarin murmushi kana ta shigo cikin ɗakin zaune ta same su ko wace cikin shigar ta irin babu raini din nan, a da dafe ta neme kusa da Daddah ta zauna kan ta a kasa..
Daddah ta matsa haɗi da tamke fuska, Mommy tayi murmushi a karo na biyu cikin muryar nan ta ta tace" wai fushi kike dani har yanzu mamah!!?.." ta faɗa cike da shagwaɓa..
Umm kawai Daddah tace, Mommy ta muskuta kana tace" Nusaiba! zanyi magana da uwa ta in babu damuwa.."
Murmushi tayi cikin halin ko in kula, tace" Hajiyar mu na barku lafiya..." ta inda zancen har lokacin bata kalle face din Mommy ba..
Daddah ta dube ta cike da ƙauna tace" ɗiyar kirki tsaya ni muje na duba marainiya ta!!.."
ta miƙe cike da isa...Ran Mommy yayi zafi, ta danne zuciyar a karo na farko kenan tace" Hajiya ki saurare ni dan Allah!!.."
" in a matsi kike zaki iya tafiya in na dawo sai kizo, yanzu kam zan dubo baiwar Allah.."
" Daddah!!" ta faɗa cikin rauni...
Ko waigowa Daddah ba tayi ba bare ta sa ran zata saurare ta...
Ina zaune nayi shiru, a zahiri zaka ɗauka tunani nake amma ni bana iya tuna komai, waje ɗaya kawai nake kallo zuciya ta bata min dadi, ko kaɗai tabbas naji shigowar su amma nayi buriss da su...
Cikin mutuƙar tausayi ne Hajiya Nusaiba ta dafa ni, haɗi da cewa" yarinyar Anty me kike tunani?.."
A hankali na dube ta take fuskata ta jike da hawaye cikin rauni murya ta na rawa nace" _Kawu na!!!_.." da sauri Daddah ta matso inda nake fuskar ta cike da damuwa tace" me ya samu Kawu naki?.."
Kare mata kallo nayi cike da shirme nace" zanje wajen sa.."
Ajiyar zuciya ta sauke cike da tausayi na, ganin ba abunda take tunani bane...
***
Tana gama faɗa Kawu na ya yanke jiki ya faɗi a waje ko shurawa baiyi ba..
Cikin mutuƙar razani da mahaukaci firgici Anty tayi kan shi tana kururuwa da ihu, haɗi da sumbatu marar ma'ana...
" Na shiga uku na lalace, shikenan zai tafi ya fari da wahala, wayoo Allah Abban Hanna kayi wa Allah da mazan tsira ka tashi!! in ka tafi ka barni wazai taffeni, ya zanyi da ɗawainiyar yara biyar, dan Allah ka tashi innalillahi!!.." ta faɗa cikin hargowa da matsananin firgici...

ŞİMDİ OKUDUĞUN
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Kısa Hikayelabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.