_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 3⃣6⃣
" Alhaji yana da kyau ka duba lamarin yarinyar nan, a gani na barin ta a kasar nan shi zaisa ta mayar da hankalin ta sosai wajen karatun ta, kai da kan ka kace kaga sauyi cikin rayuwar ta, dan Allah a karo na farko ina neman alfharman haka??.." ta fad'a cikin mutu'kar biyayya!.."
Ya gyara zaman sa, cikin nuna kulawa a gare ta yace" banki ta taki ba ai Ameena! abinda nake so ki gane a nan shine, Hajiyar mu tafi so gaba d'aya mu zauna a waje guda, a gabanki fa akayi komai kina jin abinda tace umarini ta bani ba shawara ba, dole tare da Auta zamu koma najeria, in ta amince shikenan sai ta dawo ai!.."
A hankali Mommy ta mik'e zuciyar ta babu dadi tace" dama na san ni har abada bazance ga abinda nake so na samu a wurin ka ba, shikenan ni zan d'auki nauyi yata..."
tana rufe bakin ta Auta na shigowa, fuskar ta a sake take duban su, a shagwab'e tace" Mommy and Daddy wai yaushe zamu koma gida ne?..."." Tambayi daddy din ku, amma ke a nan zamu barki, ANNUWAR zai zo ya zauna dake har ki kammala karatunki!.."
Murmushi tayi me sauti kana tace" a'a Mommy ni bana son zama kasar nan, shikenan fa ni da ku sai dai a waya, a'a wallahi bazan jure ba nima binku zanyi!..." ta fada tana noke kafada...
Dariya abin ya bashi, har ya gaza jurewa yace" to wace akayi domin ta tace bata so, ya kenan yanzu? zo nan Mama na!..." ya fad'a yana d'ago mata hannu....
Haushi ya kama Mommy tayi kofa ta bar wajen...
*****. *****. *****
A haka muka cigaba da tafiya da rayuwar mu, babu ranar bazan sai na rubar da hawaye, tuni a ANTY na ta fahimci me nake nufi da kuma abinda nafi k'auna, tana bala'i k'ok'ari wajen bani kulawa, ko da yaushe ita ke rarashi na, da nuna min hanya, duk zaman da za muyi da ita to insha Allah sai ta nuna min MAN shine yafi cancanta da soyayya ta...
A halin da ake ciki a yanzu shi kan shi ANNUWAR ya fahimci akwai wani abu boyayen sirri tsakani na da MAN, duk sanda muke hira dashi, da zarar naga MAN tofa shikenan maganar ta yanke, haka zan kafeshi da ido babu ko kifftawa, shima nashi bangaren haka ne, ko a wajen cin abinci hakace take kasancewa, sau tari sai yayi min magana nake ci, ANNUWAR kuwa ko ta kan shi bana bi...
Kawu na sau biyu yana zuwa gani na, sosai yaji dadi ganin yanda na sauya, na dawo wata k'aramar Hajiya, ga kyau dana kara, shima yayi fass dashi kamar ba Kawu na me shekaru da yawa ba, mun jima sosai dashi d'aga bisani mukayi salama ya wuce ni kuma na shiga ciki...
Zaune yake a gaban Daddah cikin biyayya yace" Hajiya dama nazo ne muyi magana akan MUNIBBAT, ni da ita mun yarda da juna, shine nake so ki shige mun gaba har ta zamo mallakina!..."
A wani gatsine take duban sa fuskar ta sam babu alamar farin ciki, zuwa can tace" ANNUWAR yarinyar fa Yar talakawa ce, masu warin talauci, har yaushe ka fara tunani irin wannan,? ita fa ba yar kowan kowa bace, yanzu har ta kai matsayin da zaka zauna da ita? cewa fa kayi in ma ta mutu ba damuwar ka bane tunda su talakawa basu da galihu, shin me ya sauya maka ra'ayi? _ki kwantar da hankalin ki Mommy inda ina raye sai na auro miki yarinyar da kaf garin nan babu me irin kudin ubanta, ki rabu dasu shirme kawai suke,_ ko ba haka kace mata ba? yanzu ka fasa cika mata burin nata ne? bazan shige maka gaba akan auren yar talakawa ba, kar uwarka tazo tace na lalata mata yara, kajira ta dawo sai ta nema maka irin macen da take so, amma ba MUNIBBAT ba domin ita din ba sa'ar aurenka bace..."" a wulak'ace take mai maganar..
Ranshi in yayi duba ya baci, cikin jin haushi yace" Daddah yanzu ba lokacin tuna baya bane, tunda nace zan aure ta kawai kiyi min abinda nake so, har yanzu ba wai na sauya a buri na bane, ina nan yanda kika sani zan aure tane kawai dan na taimaka mata, kamar yanda kika fidota a ranar kika kawo ta innuwa, ba wai auren soyayya zanyi da ita ba auren taimako ne, wallahi ban tab'a son ta ba, kuma bazan taba sonta har abada, domin ita mumunar k'addara tace, ban dani bana jin akwai wanda zai iya wanna jahadin ya aure ta!..."
" To naji ubana! MUNIBBAT bata buk'atar taimakon kowa sai na Allah, kaje kaji da mumunan burinka, amma ko zaka mutu bazan yarda na aura maka yarinyar mutane ba, ka sani ita din ba ajikan bace, matar manya ce ka rubuta ka ajiye zata auri wanda zai rik'e ta bisa amana, ba shasha irinka ba, alk'awari nayi wa kai na zabin ranta zan bata ko waye a cikin garin nan..."
" _Ni kuma nayi miki alk'awari nine wanda zata zab'a sai naga yanda zakiy_...."
Tauuu tauu tauu!!!
A jere ta zuba mai wasu maruka masu mutu'kar gigita tunani da lisafi, cikin kunar zuciya ta nuna shi da yatsa idanun ta suyi jawur tace" _ko ubanka bai isa ina fad'a yana fad'a ba balle kuma kai!! in kuma kana takama da uwarka ne ko ita bata isheni kallo ba, dan uwarka!!_..." ta ingiza shi zuciyar ta nayi mata zafi domin ya kai ta k'arshe..."
ANNUWAR tsananin zugin mari da raradi, ga tsoron da ya dalsu a zuciyar sa, na gani yanda tayi masa yasa shi saurin barin shashin nata, a hankali yake jin wani tsana ta na taso mai, tun daga ranar dana shigo rayuwar su na sauya komai, a ta dalili na sau biyo kenan yana shan mari a hannun Daddah, ko da wasa bai tab'a jin sona a zuciyar sa ba, yayi haka ne kawai dan ya ci min mutunci, ya nuna min ni ban isa na shigo cikin ahalin su ba, sai gashi Daddah na shirin bashi matsala a karo na biyu, ni ban isa na shigo cikin rayuwar sa na fita haka ba, har yau bai daina min kallon kazamar talaka ba, a baiyya ya furta "" '''NA TSANE KI NA TSANE KI
MUNIBBAT, KUMA SAI KIN GANE BAKI DA WAYO'''Take ya rikid'e ya dawo ainahin ANNUWAR din sa, idanun sa sun kada sunyi jawur, a sanyaye yace " I missing you Mommy!!..."
Tsaf ta gama shirya kayan ta yau, zata kai wa aminiyar umma ziyara, sai murna take yau za'a barta taje gidan ANTY...
Kallo tayi fuskar ta cike da murmushi tace" y'ata yau insha Allah muna da bakuwa yarinyar aminiya ta tazo, kinga kin samu kawar hira na kwana biyu, duk da bazan hada ku a d'aki d'aya ba..."
Gani tana farin ciki da bakuwar tane yasa nace" ANTY in ba damuwa ki bari mu zauna a d'aki d'aya mana, ita ma ai kamar yace ko!.."
Murmushi ta sake sakar min tace" k'ware kuwa, bana so a takurawa baby na shi yasa, dole a d'akin baki zata zauna kinji!..." shiru nayi ban sake cewa komai, jin gabana yana fad'uwa sosai a hankali na fara ambaton sunan Allah...
Kamar yanda akan kwatanta mata, haka tabi har zuwa bakin get din, gida ne na gani na fad'a galala ta tsaya kallo bakin ta a bude, murna fal ranta da yake akwai ilimi tayi saurin dakewa, zuciyar ta nayi mata zullo, a haka ta ida shiga cikin gidan...
Har na kwanta wata zuciyar ta raya min zuwa shashin Daddah hira, cikin nutsuwa nake tafiya har zan shiga naji karar kofa alamar ana buk'atar budewa....
AYSHA ta sake gyara tsawar ta zuciyar ta fass, tana zumudin shiga wanna dankareren gidan...
_Ni kam tsoro ne ya kamani nayi sauri fice a gidan gaba daya_
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce
ESTÁS LEYENDO
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Historia Cortalabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.