Chapter 33

37 2 0
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 3⃣3⃣

A hankali ya dafa kafaɗar ƙanwar sa, alama yayi mata da ido akan ta bani waje na wuce, babu musu ta matsa min, tamkar jira nake na fice da gudu ɗ'aga gidan ko Umma banyi wa sallama ba,  ina shigowa gida na tarar da Kawu na, a tsaye a bakin ƙofa ta ban iya cewa ba komai ba ila rungume shi da nayi, sai a sannan na samu damar fashewa da wani irin kuka, cikin hargowa nace" *YA ZANYI NE? YA ZANYI WAI!!!*..."

" Shittt!! yarinyar kirki, addu'a zakiyi shine kawai mafita!..." ya faɗ'a yana shafa min bayana a hankali...


*****. ****.   *******

Yau tun farar safe Daddah ta saka kowa  a gaba sai da taga ya kimtsa tamkar za'ayi wani dan ƙ'aramin biki, babu wanda baiyi mamaki ba, amma ba halin tambaya ita kaɗai ta fice yau ko mutun ɗaya bata nemi ayi mata rakiya ba, an gyara ɗaki na sosai yayi kyau komai an saka  sabo, picture din na kuwa an mamaye su a jikin bangon dakin, wanna duk umarni Daddah ne, ANTY na kam kishi ya hana ta sake shiga ɗ'akin tunda bani zan zauna a ciki ba, shi yasa bata san wainar da ake toya ba...

Ina shiryawa Kawu na yana haɗa min kaya na, har ya gama shirya kayan ban gama shirya kai na ba, da na ɗ'ago mun haɗa ido dashi sai na fashe da kuka, shi da kan shi ya shirya ni tsaf, har wata ƙwalliya yayi min abun gwanin ban sha'awa, zan so ace masu karatu kuna wajen lokacin da Kawu na yake min ƙwalliya,  sai shagwaɓa nake zuba mai yana biye min, duk abinda na nuna shi yake min, gaskiya ina haukar son Kawu na! haka shima yana masifar so na,  naga gata iya gata, ba laifi Anty ma ta nuna min so, sai wani nan suke dani take, suna gama shirya ni tsaf sai ga sallamar Hajiya Daddah nan har cikin ɗ'aki na ta shigo,  sai a sannan ne idanu ya sake rinewa da kukan rabuwa da SANYIN IDANIYATA, shima cikin dabara da wayo yake goge nashi hawayen, har mota suka rako ni ko wannen su na ɗ'ago min hannu, a haka har muka bar layin....


Babbar tarba na samu ɗaga ahalin gidan, Anty na tana ciki taki fitowa, har sai da Daddah ta shigo ɗ'akin  da kanta, cikin murmushi ta dube ta kana tace" ƴata me kike a ɗ'aki ban ganki wajen tarbar bakuwar mu ba? ta buɗe baki zatayi magana Daddah tayi saurin cewa"  cuff!! na san duk wannan abun da kike akan baby ne ko? ƙwantar da hankalin ki, za muyi maganar amma kafin nan zo kiga wani abu!..." hannun ANTY ta roƙo har bakin ƙofar palon inda ta barni, kuma ta hanani buɗe fuska ta...

JARRIMME NA tare da ANNUWAR, sunyi bala'in haɗuwa ko wanne su yana bani waje, gaskiya Allah yayi halitta a nan kyau iya kyau, babbancin su a baiyyane yake MAN ya fishi sakin fuska, da ƙwarjini amma shima fa ba baya ba wajen haɗuwa, ta cikin yalolon mayafi na nake hango su, akan MAN idanu na suka tsaya, wata irin soyayyar sa ce take fizzga ta, a hankali nayi kasa da ido haɗe da ɗanne zuciya ta, wasu siraran hawaye na zubo min, Daddah ce ta katsi min kuka nawa da cewa" yarinya ta BISMILLA!..." da idanu tayi wa ANTY alama akan ta buɗe mun fuska, cikin yake da basar wa tace" ANNUWAR zo ka buɗewa baƙuwar mu face din ta..."

Har a zuciyar ta kishi take da wannan baƙuwar, sam ba'a san ranta zata zauna a ɗ'akin babyn ta ba...

Da sauri Daddah tace" No ke nake so ki bude!.."

MAN kam ya kafeni da idanu, haka shima ANNUWAR, a cikin su babu wanda yake ƙwaƙwaran motsi, a hankali ANTY  ta matso inda nake,  tun daga kasa ta fara kallo na har zuwa saman kai na, cak idanun ta suka tsaya a face din, kirjin ta ya buga da ƙ'arfi cikin sauri ta yaye min mayanin kaina....

Masu karatu kun dai san yanda nake da kyau dama, gashi Kawu na yayi min ratsatsiyar ƙwalliya, da sauri nayi kasa da ido cikin wani salo me ɗ'aukar hankali, iskar na kaɗa min gashin idanun na,  gaba ɗaya su ƙamewa su kayi, domin sun ga cikar haiba, kyau me asali da nagarta, ilimi haɗ'e da tarbiya, gaskiya Alhamdulillahi...

Da sauri ANTY ta juya ga Daddah, da ido tayi mata nuni da cewa to ya kika gani?..." a suƙwane Anty ta saki wani mahaukacin murmushi har haƙoranta na baiyyana, ta sake gyara tsawar ta da kyau, cikin sanyin jiki kuma tace"" BABY NA!!!..."""



*Welcome to the house*



COMMENTS





AND


SHAERD



PLEASE



MRS ABUBAKAE CE

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now