Chapter 29

44 2 0
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 2⃣9⃣

Har na sako ƙafata waje, na tuno kaina babu ɗankwali da sauri na juya zuwa ciki, zuciya ta a cunkushe...

Ƙofar gidan ya sake kalla cike da ƙosawa, ya dubi a gogon dake ɗaure a tsitsiyar hannun sa, sirin tsaki yaja kana ya kawar da kai gefe, a baiyya yace" me ya kawo ni nan ne? wata zuciya ta bashi amsa da cewa kazo ne kawai sabida ANTY, Ya MAN, amma kafi ƙarfin gidan nan..." ya sake sakin tsaki...

A ran shi sam ba haka yaso ba, dole ya ɗauki motar ANNUWAR  bai wani sha wahalar tafiya ba ya iso ƙofar gidan, yana tsaya wa KAWU NA na fitowa, sun gaisa cikin mutunci daga bisani, ya koma mota duk ƙunya ta ishe shi, sai wani noƙ-noƙ yake tsarabar da yayo mun ita ya bawa Kawu na, cikin jin ƙunya yace"  gashi ni zan wuce a bawa baby!  muna ƙewar ta sosai..." cike da nauyi ya mika saƙon...

Kawu na, idanun sa akan MAN yace" ba damuwa, amma ka jira tazo ku gaisa !!.." cikin sauri yace" a'a zan dawo wata rana, a gaishe ta kawai...'"

Ba haka Kawu yaso ba amma ba yanda ya iya dole ya rabu dashi...

Na ɓ'ata lokaci sosai, wajen gyara kai na nayi matsakaiciyar ƙwalliya,  hijabi na saka har kasa sannan nayo waje abu na, domin zuciya ta na bani cewa JARRIME NA yana waje, cikin sauri na taho sai tashin ƙamshi nake, fuska ta cike da walwala...

Ya juya bayan sa da nufin  shiga mota ni kuma Ina fitowa daga cikin gida, a lokacin Kawu na shima ya waigo tare da sakar min tattausan murmushi, sam hankali na baya wajen sa, gaba d'aya nutsuwa tana ga wanda ke gaban mu, cikin zazzaƙar murya ta nace" JARRIME NA!!!.."  idanu na tar akan sa, baki na yaki rufowa burina muyi ido biyu dashi...

Cak ya tsaya shi bai waigo ba haka kuma bai shiga motar ba, tausayi na ya kama Kawu na cike da dabara ya rungumo ni zuwa jikin sa, fuska ta na ga wanda ke gaba na, yace" ya akayi ne yarinyar kirki!!.."

Wallahi ban taɓa tunanin akwai ranar da Kawu na zaiyi min wani abun farin ciki na gaza dariya ba sai yau, shiru nayi a jikin sa idanu na kan bawan Allah nan..

Shi kam jin ba dashi nake ba, take zuciyar sa tayi masa nauyi cikin bacin rai, ya waigo yaga ko mun shige gida, tarrr ya hango fararan idanuwa na akan sa, ko kifftawa banayi, shima kallo na ya fara babu ko ƙwaƙwaran numfashi,  mun ɗauki lokaci me tsayi a haka, ni na fara dauke kai na sabida Kawu na ya magantu, sam hankali na baya wajen sa, bamma san me  yake cewa ba, ni dai naga ya wuce gida ya barni a wajen...

A hankali MAN ya matso inda nake cikin jin ƙunya nayi kasa da kana, shiru wajen yayi babu abinda yake tashi sai sautin numfashin mu, zuciya ta na bugawa da ƙarfi, ya bude baki zaiyi magana nayi saurin cewa" barka da yamma malan!.."

Bai amsa min ba yace" shin bakya ganin saƙo na ne! ?.."  cikin wani taushin murya yayi min maganar, har cikin kai na naji yanda ya fitar da kalmar...

" Kayi haƙuri kullum tana gaya min, yau nee kawai bamu haɗ'u ba, nace ta faɗ'a maka YAYA NA ya sauya min makaranta, na dauka ma kunyi maganar da Kawu na!!.." cikin nutsuwa da jarimtar da na aro nayi maganar...

Dafe goshin sa yayi, cike da karaya yace" No ba wannan nake nufi ba, wace shawara kika yanke yanzu?.."

Gaba ɗaya na gaza fahimtar inda ya dosa, a magan-ganun sa kallon sa kawai nake, a iya sani na AYSHA itace budurwar sa, a yanda take faɗa min da bana nan kullum sai yazo taɗi to me kuma zai kawo shi waje na?  ɗanne abinda zuciya ta da jiki na yake min nayi cikin ƙarfin hali nace" in na fahimci zance kai, kana so ka baiyya na mata cewa kana son ta ko?..." na faɗ'a ina zuba mai manya idanuwa na...

A tunanin sa na gane abunda yake nufi, cikin jin dadi yace" eh a duk lokacin da zaki ganni ki daina ce min malan, ki kirani da  sunan da ya dace dani,  munyi kewar AYSHA!! sosai, rashin ki a tare damu ya haifar mana da matsala babba, muna mutu'kar k'aunar ki, kullum fatan mu shine ki dawo gare mu, musamma ni tun kafin ta san ko ita WACECE nake Son ki, tun kafin kowa ya san ta a cikin ahali na nake tare da ke, ina mutuwar son ki da ƙaunar ki, zuciya ta hanani sakewa duk dan sabida ke, kullum cikin begen ki take, ki dawo gareni ko na samu sausauci abun da yake damuna, ke ajiye maganar yarinta a yanzu domin ki wuce a tsayayi miki musali, Aysha auren ki shine maradin zuciya ta, nutsuwa da cikar kamalarta shine na mallaki mata kamarki!!!, ina fatan kema kina so na kamar yanda nake ƙ'aunar ki?..."

Dumm zuciya ta, ta buga da masifar ƙ'arfi, jikina ya ɗauki tsuma hawaye suka cicikowa idanu na, tunda ya fara magana jikina ya gama sandarewa, tabbbas ko ba'a faɗa min ba a yanayi kalaman sa na gane ko shi  waye, '''Shi nake jira'''  muryata narawa gaba na yana tsanenta faɗ'uwa nace" nima ina tsananin ƙaunar ka JARRIMA NE!!..." kuka ya kwace min na kwasa da gudu nayi cikin gida, a tsakar gida na wuce Kawu na, kai tsaye ɗaki na na nufa Ina sake fashewa da matsanancin kuka, a baiyya na furta "" ko tantama banayi shine JARRIME NA, kalaman sa sake irin wanda yake rubuto min, har sun fi dadin sauraro a bakin sa, amma kashe _bani yake so ba_  komai na Aysha ne! shikenan na faɗo a karo na farko a soyayya banyi nasara ba, ya zanyi da dafin da ya mamaye min zuciya? ya zanyi da maƙauniya soyayyar kai? me yasa kayi min haka? dama kai ne JARRIME NA?  bazan iya shiga tsakanin masoya ba, dole na miƙa ka ga masiyayiyar ka, muddin zaka kasance a cikin farin ciki to ni kuma zan iya hakura da kai ko dan ka samu cikakiyar  nutsuwa,  _har abada har abada bazan manta da kai ba! ina ƙaunar ka nima!!!..._" cikin matsanancin kuka da kunji nayi maganar...

MAN ya runtsi idanun sa cikin mutuƙar farin ciki  da jin dadi, murna fal ran sa, gani ya samu karɓuwa a wajen SAHIBAR sa, ko bata faɗa mai ba a yanayi yanda ya ga fuskar ta, tabbas soyayyar sa tayi mata mugun kamo, ya saki wata siririyar ƙara haɗe da dan taka rawa kana ya shige motar sa, a haka ya isa gida bakin sa har ƙunne...

ANNUWAR shima karasowar sa kenan, su kayi kilashin, MAN ya haɗ'e fuska cike da nuna iko yace" ANNU! wai yaushe muka fara yar haka da kai ne?..."

Kun dai san halin mutumin ku, cikin izza da isa yace"  bana jin akwai ranar da na taɓ'a ɗaukar wani abu naka ka nuna min rashin dadin haka! na gaji da ganin ku kullum a cikin gida babu walwala shine naje wajen baby! dan na ɗ'auko ta ko zaku samu nutsuwa, bam san fita zakayi ba..."

" Wace baby!??.." "" babyn ANTY mana, bam ma samu damar ganin ta ba Hafsat tayi min kiran gagawa na wuce!.."  wata ajiyar zuciya ya sauke jin abinda yace, cikin farin ciki yace"  ka san wani abin farin ciki ANNU?.."

" A'A sai ka faɗa tukuna.."

" Ya MAN din ku ya faɗ'a tarƙon ƙ'auna, ina cikin farin ciki sosai yau! ta amince dani!  a matsayin JARRIME ta, ina son ta sosai! ina ƙ'aunar ta! nayi nasara a karo na farko ANNU, ta dube tsakiyar idanuna ta furta min Ina ƙaunar ka JARRIMA NA!!! NI MA INA ƘAUNARKI SAHIBA TA!!!..." ya faɗa da ƙarfi....

ANNUWAR ya toshe bakin sa da hannu biyu, dariya na ƙwace mai ganin yanda yayan nasa yake taka rawa, ya ƙarewa YAYAN nasa kallo kana yace" lallai soyayya tayi maka mugun kamo, na taya ka farin ciki sosai Allah ya bar ƙ'auna, amma karka manta da alƙawarin Mommy!..." yana zuwa nan ya wuce ciki abun sa...

To wannan nasarar da yake ganin ya samo itace ta zamo sanadin farin cikin, ANTY da Daddah babu wanda baiyi farin ciki ba a cikin su...

Allah sarki dama haka rayuwa ta gada, yau in kaine gobe wani ne, a ɓangaren MUNIBBAT kuwa yau ƙwana tayi tana aikin kuka, ga tarin takardu a gaban ta, banda hawaye babu abinda take sharewa, Kawu ya san halin da take ciki dan haka yaki shigowa ɗakin, yana nashi ɗakin yana taya ta bakin ciki....


Comments

And

Shared

Please


Mrs Abubakar ce

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now