_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RRAHMANI RRAHIM
🅿3⃣0⃣
Washe gari, ina tsaka da shirin tafiya makaranta na, ANTY ta shigo d'akin fuskar ta a sake take duba na, " MUNIBBAT dinna, zauna muyi magana dake kinji!!.." ta fad'a cikin sanyin murya..
A hankali na koma na zauna, cikin biyayya nace" Anty kun tashi lafiya? ya k'wana su Hannah!.." a lokacin baya na san bata amsa min sai ma dai ta kawo mun bugo, amma abin mamaki sai naji tace" duk Alhamdulillahi, me ya same idanun ki haka?.."
Da sauri nayi kasa da kai na cikin kasalaliyar muryar nace" humm dama dama jiya ne kafin na kwanta abu ya shigar min idanu na shine yake ciwo!.."
" Aiyya sannun kina kiyayye wajen abunda kike sabida gaba, yauwa dama nazo ne muyi magana dake game da _gidan rokon ki!_ .."
Jin ta ambaci gidan roko na sai da gaba na ya fad'i cikin jimami nace" to!.."
" Da yamma in kin dawo Abba Hanna zai tambaye ji, menene zabin ki game da inda kika fi jin dadin zama, abinda nace so dake shine kada ki k'usk'ura kice nan gidan, nafi so ki koma can gidan yan gayun can dan abun duniyar nan da kin samu aiko mun dashi gida a matsayi na na uwar rukon ki, amma bari ba yanzu ba dole ne ki ce mai kinfi son zama a gidan Hajiya, akan wannan gidan! ba shawara nazo nema ba umarni ne na bakin matsayi na wace na isa dake, zan gani in naka matsayin danake harsahe..."
Tana zuwa nan a batun ta, ta fice a d'akin ko kallo na bata sakeyi ba, shiru nayi ina tunanin maganar ta, to yanzu tana nufin na bar nan gidan sabida abin duniya? shikenan Kawu na zaiyi min nisa? a ina zan nemo mata abun duniyar?.." to ganin zan b'atawa kai na lokaci da tunanin Anty yasa nayi saurin k'arasa abunda ke gaba na fice a gidan...
To kamar yanda tace, ko da na dawo da yamma banga kawu na ba, ashe yaje gidan su Hajiya ne dan ya sanar mata, duk ban san wainar da ake toya ba...
****
Cikin mutu'kar girmamawa, jamma'ar gidan suka tarbe shi, tamkar wani babban mutun haka aka kawata zuwan sa, ga abinci kala-kala da abin sha, an jere masa su, a gaskiya sun mutunta shi iya mutuntawa, Hajiya Daddah da kanta tafi ta shigo dashi har cikin falon bak'i, nan Kawu ya zage sai kalle-kalle yake a wayance, a zuciyar sa kuma tana hango Mai d'iyar sa yanda tayi rayuwa a cikin wannan tank'amemen gidan...
Sun gaisa cikin sakin fuska d'aga bisani Kawu ya fara da cewa" Hajiya maganace ta kawo ni, kamar dai yanda nayi miki alk'awari, to lokacin cika shi yayi Allah ya nufa, insha Allah gobe in war haka _MUNIBBAT tana tare daku_, domin nima zan wuce wajen aiki na tunda na ganta, hankali na ya kwanta na samu ingataciyar nutsuwa, nima a gobe zan wuce Legos, nazo na na sanar miki shin har yanzu kuna nan kan bakar ku na san rik'e ta ko kun canza ra'ayi?..."
Cikin mutu'kar farin ciki marar musaltuwa, Dadda ta mik'e jikin ta narawa gani zata samar wa matar d'an ta farin ciki tace" da gaske kake zaka iya bamu Aysha har cikin zuciyar ka!?.."
Tabbas Kawu na, nice zuciyar sa amma sabida na samu farin ciki, maradin zuciya ta ya tabbata, sai ya d'anne zuciyar sa yace" sosai ma kuwa ina mutu'kar k'aunar MUNI, ina son ta sosai haka kuma ko ban fad'a ba zanyi bala'in kewar ta, amma dole zan ha'kura domin nafi k'aunar farin cikin ta akan nawa, Hajiya Muni tana buk'atar ku a halin yanzu fiya dani! tana son kasancewa daku, farin cikin ta a yanzu shine kullum ta bude idanun ta ta ganta a tare daku, ba wai dan bana son ta ba ne a'a zan rabu da ita ne akan dole, Ina fatan bayan barin ta waje na bazaki bari tayi kukan maraici ba Hajiya? ki kula min da ita Hajiya karki bari tayi kukan bakin ciki, ga amanar ta nan na baki halak_ malak Allah ya tayaku ruko, in Allah ya kai mu zuwa safiya sai azo an d'auke ta..." da sauri ya mik'e zai wuce, cikin sauri Hajiya ta riko hannun sa, tausayin sa ya kama ta muryar ta na rawa tace" bazan k'asance me son kaina ba har abada, muddin zuciyarka bata kwanta da wannan kyautar ba, ka barta a wajen ka kawai inda rabo mu sake zama inuwa d'aya da ita sai kaga tazamo tamu..."
" A'A ya zama dole nee ta dawo inda kuke, ina so ta samu nutsuwa ne, burin ta na cikin ahalin ki duk ranar da ta dawo zaki tabbatar da haka, ni dai rokona a gareku shine ku kula min da marainiya ta!! domin ita amana ce a gareni..."
" Insha Allah zan mu kiyayye, zan bata kulawa kamar yanda nake bawa jikokina, Shafi'u ba kai ne zaka bani umarnin yanda na kula da baby! da zaka zauna ko da na awa d'aya ne zaka tabbatar da baby tana da babban matsayi a cikin gidan nan, kaje wajen sana'ar ka cikin nutsuwa ka sa ranka tamkar tana gaban ka ne, insha Allah bazakayi danasani da damu ba...."
" Allah ya yarda Hajiya, ni na wuce sai wata rana kuma in Allah yayi min dawowa..."
Nan sukayi sallama da Hajiya Daddah, cikin kwanciya hankali...
Kawu yana fita Hajiya ta mike cikin farin ciki ta koma d'akin ta zuciyar ta fal murna da an'nashewa...
****
" Yarinyar ta! kina jina?.."
Cikin nutsuwa nace" eh Kawu na!!.."" Ina so ki saurareni da kyau, duk da a lokacin baya kinyi rayuwa irin wace, nake so ki koma yanzu, amma karki manta a lokacin baki da wayo ne bare dabara, ki k'asance me hak'uri da tausar zuciyarki, bana so ki zamo me son zuciya da hangen nesa, MUNI ko da wasa kar tsutsayi ya Kai hannunki d'aukar abinda ba naki ba, ki k'asance me janye jikin ki a duk inda kika fahimci matsayinki bai kai ba, girmama na gaba dake na san baki da rashin kunya bare rainuwa, dan Allah ki zauna a yanda na sanki, karki d'auko wani hali wanda bamu sanki dashi ba, biyayya itace abinda nake so ki k'asance akai, ki nuna duk wanda kika gani a gidan cewar shi me daraja ne, domin sune gaba dake gobe insha Allah zaki bar gidan nan, ma'ana zaki koma gidan su Aliyu da zama domin nima a goben zan koma wajen aiki na! kibi umarni na ki zauna lafiya, karki manta da darajarki mutuntukar ki shine mutuncinki, ki rike mutuncinki domin yana da mutu'kar amfani a rayuwarki, karki bare ko wanne na miji ya rabeki muddin ba mijin aureki bane, ki k'asance me hak'uri a duk halin da kika tsinki kanki, insha Allah burinki zai cika muddin kika zamo me rike alk'awari da amana, zauna a me gaskiyarki dana sani..." cikin sanyi yake min maganar, jikina yayi bala'in sanyi na gagara cewa komai..
A hankali na d'ago kaina, a raunane nace" me yasa Kawu na? shin dama akwai ranar da zaka badani ga mutane da baka san ko su suwaye ba? kamar yanda ka saba tafiya ka barni haka kuma ka dawo ka tarar dani lafiya kalau, a yanzu Ina me neman alfarma a wajen da ka barni a cikin gidan nan, bana son zuwa ko ina Kawu na!.."
" *Kin ha'kura da (A&M) dinki? shin zaki iya rayuwa ba tare dashi ba?*..."
Cikin mutu'kar razani na d'ago, idanuna sun ciciko da k'wallar bakin ciki....
Comments
And
Shard
Please
Mrs Abubakar ce
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.