_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*~Alhamdulillahi na gode sosai da addu'oinku naje lafiya na dawo lafiya, ina fatan kuma kuna nan lafiya kalau, insha Allahu daga yau zakuna jina yanda aka saba da yarda Allah..~
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 1⃣6⃣
Fuskar ta cike da damuwa, tace" Babban mutun lafiya kuwa? "
ta faɗa tana dafa kafaɗar sa..Murmushi ƴaki yayi cikin inda-inda yace" No daddah babu komai.." " a'a yaro na akwai magana a bakin ka, ko kai ma zaka zama ɗan uwan naka ne? gaya min abinda naji kana faɗa kafin na shigo..?"
ta ida zancen da ƙura mai idanu..Sunkuyar da ka yayi kasa zuciyar sa na saƙamai abubuwa da dama game da yarinyar, cikin sauke a ajiyar zuciya yace" Daddah ina so muyi magana dake ta sirin.."
Yau garin an tashi da wani irin sanyi, ga hazo da ya gauraye ko ina, a kuɗinɗine take cikin bargo tana ta sharar barci me dan karan dadi, cikin takaici yake duban ta ji yake tamkar ya rufe ta da duka, ƙkafa yayi ya fice a ɗakin ruwan da ya ajiye a daren jiya ya ɗauko, wanda ya ƙwana a bude iska da kura sun gama sauya mai launi, babu tausayin ta ko kaɗai a ranshi ya ɗaga gaba ɗaya bokitin ya juye mata shi a kai...
Cikin tsananin kaɗuwa da firgici ta miƙe tsaye, zuciyar ta nayi mata kuna, gani wanda yayi mata wannan aika-aikar tsaye akan ta, yasa ta fashe da wani irin kukan takaici me kona zuciya, cikin shasheƙa tace" Abban Hanna a gaskiya shiga hakin nawa da kake ya fara isata, wannan wanne irin horone fiyye da wata guda, na gajiya³ kawai ka sauwake min yafi min akan wannan azabar da kake gana min a boye, ka hanin haki na, ka hanin taɓa yarana, ka hanin zaman gidan ka na awa guda, kullum ina yawo a titti neman yarinyar da nake ji a jiki na tana can tana yawan banza, na gode Allah da bani na koreta ba, kai da kan ka kace ta fita ta bar maka gidan ka, tunda ta tafi ni menene nawa a ciki?, ko ni na saka ka kore ta? ni nace ka furta? ya zaka aikata abu kuma ni ka adabi rayuwa ta babu gaira babu dalili, to wallahi ya ishe ni haka..." ta ƙarke zancen tana kara sautin kukan ta...
Allah sarki Kawu na a hankali ya sauke boket din hannun sa yana sulaliwa a wajen, cikin mutuƙar ladama yace" har abada bazan daina ganin bakin ki ba Sa'adatu, ko me na aikata kece sula ke kikayi komai har na furta kalamar da ta lalata min yarinyar ta, ita kaɗai ce nake gani na ji dadi, domin itace dangina, yarinyar ta baza tayi yawan banza ba har abada, jiki na yana bani duk inda take a yanzu bata cikin farin ciki, tabbas tana buƙata ta a halin yanzu, kin cuceni Sa'adatu kin cuceni cuta mafi muni, ki shiga tsakani uba da ya, kuma sai Allah ya saka mata kin zalinci marainiyar Allah, shin wake bakya tunanin yanda rayuwarki zata kasance nan gaba? lokacin da kike gallaza mata bakya tunanin kema ta Allah ta kasance akan ki? bakya tunanin Yaya yarakin zasu kasance in bakya raye?...."
Tabɗi a sai yanzu tunanin Anty ya ka nan, kuka kam ya sake ƙwace mata, cikin tsananin nadama tace" ka tabbar bazaka sake ni ba in na faɗa maka gaskiya? ka tabbatar bazaka min hukucin mafi muniba in na baiyyana maka gaskiyar lamari? bazaka rabani da yaran ba.."?
Kura mata ido yayi sosai yana duban ta, cikin zuciyar sa kuwa bugawa take da ƙarfi, a hankali jikin sa ya fara kaɗawa cikin ɗauriya yace" ina jinki, gaya min gaskiyar da za kiyi shi zai ƙwaceki ɗaga abinda nake miki dama wanda nake shirinyi miki yanzu.."
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.