_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿3⃣5⃣
ANTY dake zaune tayi saurin tashi tsaye a hankali tace" MUNIBBAT! Or MAN..?"" ai bata tsaya godon nazari ba tayo ɗaki na, ta tura taji a rufe Aiko ta shiga kirana kamar tashin hankali, tanayi tana bugun ƙofar...
Da kyar na iya juyawa, kaina yana min wani azababban ciwo, ga jini da yake diga ina jan jiki a haka na isa ƙofar, numfashi na sama-sama nace" ANTY!..." gaskiya na sha wahala sosai sannan na samu na buɗe ƙ'ofar room din...
Hankali a tashe ta shigo ɗakin, halin da ta ganni a ciki shi yafi komai birkita mata lisafi, tamkar jirin zuwan ta nake, a jikin ta na ƙwanta murya ta na sarƙewa nace" ANTY MAN DINNA!!!." na faɗa ina nuna mata hanyar waje da hannu na...
Tana shirin tambaya ta na sume a hannun ta...
Ko nauyi na bata ji ba, haka ta saɓe ni sai shashin Daddah...
Gaskiya ranar anga tashin hankali a gidan, kamar yanda ta kasance dani haka ce ta faru a bangaren MAN, shi kuma Daddah ta shiga duba sa, duk a gida aka zo aka duba mu, sai maguguna da aka bamu...
Tun daga ranar muka shiga wasan yar buya tsakani na dashi, muddin yana waje bana zama, ko magana nake da na hango shi zan koma ciki, tun su Dadda basu fahimta ba har suka gane halin da muke ciki...
Gashi kullum san shi da ƙaunar sa kara ruruwa yake a cikin raina, gashi bama iya haƙ'uri sai muga juna mu hankalin mu yake ƙwanciya...
Ina ƙwance a gado na, na lula duniyar tunani inata karanta wasiƙar jaki, har ban san lokacin da ANTY ta shigo ba, tsaye tayi a kaina tana ƙare min kallo gani bana cikin duniyar yasa ta dafani cikin sigar rarashi tace" Baby! lafiyarki kalau kuwa?.."
Hmmm na sauke ajiyar zuciya, zanyi magana tayi saurin cewa" muddin kin san abinda zaki faɗa min ba gaskiya bane kiyi shiru da bakin ki bana buƙata, ban san wannan irin matsayi nake dashi a zuciyarki ba baby, a tunani na yanda na ɗaukeki ƴ'a haka kika ɗaukeni uwa, ashe abun ba haka bane! shin kina da wanda zaki gayawa damuwarki sama dani a yanzu? kin san halin da nake shiga idan na ganki cikin halin fushi ko rashin walwala? MUNI ina ji a jikina ni uwace a gareki ta jini, zan so ki faɗa mun abinda yake damunki ni kuma muddin baifi karfina ba insha Allah zaki sameshi ko menene? zan gani nakai matsayin da nake tunani ko kuwa!...""
Shiru nayi ina tunani mafita, ta juya zata wuce zuciyar ta babu daɗi nayi saurin cewa" *KE UWACE A GARENI ANTY!!* nima Ina jinki sosai a raina, Ina miki kallon mahaifiya tane, na samu duk wata kulawa da nake buƙ'ata a wajenki, a yanzu kece jigona! ina ƙaunarki ANTY ki fahimceni please!..."
_nima haka ƴ'ata ina sonki_... ta faɗa cikin rauni...
To tun daga ranar fa ANTY ta saka min ido, duk inda take ina zaune a gefen ta, ko MAN ya fito bana samun damar guduwa domin kallo ɗaya take min na nemi wajen zama...
Ɓangaren ANNUWAR kuwa mukayi wata irin shaƙuwa ta ban mamaki, a ɓangaren na bana jin komai akan sa, a nashi ɓangaren kuma wata sabuwar soyayya ta yake ji tana fizgar sa, a hankali a hankali ya fara turamin ra'ayi irin nasa, soyayyar me zafin gaske ta fara shiga ta, dana rufe idanu na shi nake hange sai nayi nisa a tunanin sa katsam kuma sai MAN ya faɗo min, tamkar na tashi a barci haka nake zabura duk lokacin da nayi irin wanna dogon tunanin...
ESTÁS LEYENDO
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Historia Cortalabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.