Chapter 43

34 4 1
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

'''Wannan pagen na kune duk wacce tasan tayi comment a chapter 42 to wannan kyautar tace, kuyi yanda kuka ga dama dashi 'na bar muku halaka malaka!'''

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 4⃣3⃣


Mommy ce tana huce tamkar baƙin kumurci, ta nuna Anty da yatsa cikin zallar masifa tace" ko da wasa karki sake gigin taɓa mun yaro! domin yafi ƙarfin ƙazamin hannun naki! ki godewa Allah ba akusa zuciyata take ba da wallahi sai na yanke miki hannu!..."

Kauu tass tass! Daddah ta zuba mata wasu marika masu mutuƙar azabar zafi da raɗaɗi, cikin ƙaukausar murya tace" kinyi 'na farko kinyi na ƙarshe muddin ina raye a cikin gida nan ke baki isa kin wulaƙanta mun yarinyar ba, shigowarki kenan da abinda zaki saka mana kenan? wannan itace godeyar ? shin kin fara bin ba'asin dalilin hukunta shi? wato ke aimaka uwar ƴan ƴaƴa shine kika ware hannu kika zafgawa ƴata mari ko? ke tsaya m'a tafiyar da kikayi bai koya miki hankali acan ba dama?..."

Mommy riƙe da kunci take duban daddah zuciyar ta babu daɗi, wasu hawayen baƙin ciki suna zubo mata, babban ɓacin ranta shine a gaban kishiyar ta Daddah ta mare ta ga ɗan ta dake tsaye shima yana muzure...

" Daddah! nice 'fa! yanzu sabida nayi hukunci akan wannan abar shine kika mareni a gaba yaro na da ita?.."

" shitttt! Amina ki ɓace min a gani kafin nayi kasa-kasa dake!..." cewar
Daddah da ranta ya gama ɓaci...

Anuwar ya kamo kafaɗar Mommy domin ya kula bata 'da niyar tafiya, Daddah kuma tsaf yasan zata aikata abinda yafi wannan, cikin sanyin jiki yace" pls Mommy muje!.." ya faɗa yana tura ta, akan dole ta bishi ba dan ranta yaso ba...

Ni kam tunda aka mari Anty wani irin tsoro ya kamani ban jira komaiba, na gudu bayan kujera warwas nayi a kasa tamkar babu rai a tare dani...

Suna shiga shashinta, tayi maza ta juyo dashi cike da masifa ta zafga mai mari cikin ƙunar zuciya tace" uba me ka aikata musu da zafi haka? Antyn ku baza ta taɓa saka hannu ta dake ka haka kurum ba, dole sai da babban laifi! maza faɗa mun ko na sauya maka kamannin?..."

Ya gigice sosai zuciyar sa ta shiga soya, wata irin tsana ta yake ji kamar yaje ya shaƙeni 'na mutu, ya daure cikin biyayya yace" kiyi haƙuri Mommy zanyi miki bayani a tsanake yanzu ki hutu zuwa anjima zan shigo, amma ki yarda dani banyi musu komai ba, har yanzu My son dinki yana nan yanda kika sani magance akan wata matsiyaciyar yarinya, Mommy bana son talaka ko kaɗan..." cike da shagwaɓa yayi maganar...

Zuciyar ta tayi mata sanyi ta dube shi cike da ladamar hukunta shi, ta kallen hannun ta a hankali ta sauke ajiyar zuciya kana tace" bana son daukar magana Son ka kiyayyeni kaje zan kira ka!..."

" Mommy!!.." Ya faɗa a sangarce.. cike da soyayyar sa ta dube shi, da ido yayi mata nunin abinda yake so, babu gardama ta ware mai hannuwa ya taso da sauri suka rungume juna, cike da ƙewa...

ANTY ta wuce shashin ta, zuciyar ta babu daɗi, Daddah ma ɗakin ta wuce zuciyar ta a jagule...

Shirun da naji wajen yayi ne yasa na taso a hankali, kamar ɓarauniya na gudu  ɗaki na...

Duk wannan badaƙalar da ake DADDYN su bai sani ba, haka MAN DA NAFISATU...

Daddy kai tsaye ɗakin Anty ya taho, cike da ƙewar matar sa sauƙi ɗaya ma suna video call, ANTY kuwa zuwan ta ɗ'aki ba sanya ta tsaya ba uban ado taci na kece raini tamkar ba abinda ya faru, ko ina na ɗ'aki sai tashin ƙ'amshi yake, gaskiya ANTY na yar gayuce gashi ta iya shanye damuwa, a haka ta shigo ɗakina fuskar ta a sake tace" Baby! Baby! wai har kinyi barci?..." ta faɗa tana juyoni, ɓata fuska tayi gani hawaye shaɓe-shaɓe a face dinna...

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now