Chapter 51

20 1 0
                                    

Wani irin zullo nayi na faɗ'a kanta cikin wani bahagon kuka,  ina jijiga ta nake cewa" me yasa? me yasa zakiyi min haka? a lokacin da nake buƙ'atar ki a lokacin dazaki gudu ki barni! ya kike so nayi da raina ne ANTY? dan ALLAH ki tashi karki tafi ki barni dan ALLAH!..." Gaba ɗ'aya na dawo abar tausayi, kuka nake kamar zuciya ta zata fito a kirjina...

Bishira ta sunkuyo fuskarta jiƙe da hawaye cikin muryar kuka tace" menene lefin da tai miki haka MUNIBBAT da kika kasa furta mata kalmar yafiya? kukan me kike yanzu ? kamata yayi kiyi farin ciki tunda burinki ya cika, kece matun na ƙarshe wanda Mama tai magana da ita kafin ta samu kanta a cikin wannan halin,  bakin cikin ki ne ya kashe min Mama na, bazan taɓ'a daina ganin ki da wannan tabon ba, a yanzu matsayin ki darajarki kimarki...."

Maganganu zafi suke min tamkar wace take watsa min tafashashen ruwa, cikin zafin nama da ƙwarin gwiwa na zafga mata mari idanuna cike da hawaye ina nuna ta da yatsana manuniya nace" kul dinki Bishira! karki ƙusƙura ki ɗaura min lefin kisan kai! ki bar ganin ba ita ce ta haifeni ba, amma a matsayin mahafiya na ɗauke ta, ke haifarki kawai tai amma nakifi ki jinta a raina!  kina tunanin wannan daliline zai sa ta kashe kanta? kin ɗauka ni kaɗai ce damuwar ta? in kika sake buɗe bakin ki a kai na da nufin faɗar kalma marar dadi zan saɓa miki wallahi!..." cikin izza nayi mata woning...

Shiru tai dafe da kunci tana kuka, Kawu ya matso a hankali yana duba kana yace" da gaske ta neme yafiyar ki kafin faruwar lamarin?.."

Ba tare da nayi tunanin komai nace" Eh! Amma bata tsaya taji abinda zan faɗa na ta wuce ɗ'aki.."

Kan ANTY na koma  na ci gaba da kuka na ina rarashin ta, cikin kuka na kwanta a bisa kirjin ta a hankali nace" innalillahi ANTY yanzu a kai na dama zaki iya kashe kan ki? tun ba yanzu ba na jima da yafe miki ANTY, tun dana bar gidan nake miki addu'a har kama I yanxu, ban taɓ'a ganin lefinki ba ANTY na sake yafeki miki tun a gidan ku da kike zuwa min cikin dare kina kuka, na sake yafe miki a karo na uku lokacin da kika rungume ni a kirjin ki da zan faɗi a shashin ANTY Rabi, to me kuma kika sake nema ANTY? inda domin na furta miki ne kinaji na  to ki saurareni ANTY *na yafe miki na yafe miki duniya da lahira, na yafe miki har ƙarshen rayuwa ta* dan Allah ki tashi ki cireni a zargin da ake shirin jefani...."

Kawu na ya dafani cike da damuwa yace" wa ya gaya miki ANTYnki ta mutu ne MUNIBBAT?..."

Soror nai Ina kallon shi baki na a bude, nace" kana nufin tana jina?.."

" Eh amma a halin da take ciki bazata iya magana ba sai nan da awa hudu, yayi mata allure ne sanadiyar    bugawa tai a kai shine yayi silar faɗawar ta ruwa, gashi jikin ta babu ƙwari na rashi. abinci da bata ci ba kwana biyu, a yanzu tana buƙ'atar hutu!..."

Dariya nake me haɗe da kuka, na sake kallon ANTY sai yanzu naga alamar numfashin ta amma kadan-kadan! Nace" Kawu mu tafi asibiti mana d'aga gani tana jin jiki!.."

Murmushi kawai yayi ya wuce abin sa, Bisha ta dubeni da nufin nayi mata murmushi aiko na haɗe fuska tammau, jikin ta a sanyaye ta fice a d'akin...

MAN ya sakani a gaba da tsokana, tun abun na bani haushi na ya fara bani dariya,  kamar ba jinya na zauna ba sai gamu muna ta guje-guje a cikin ɗakin har tsallake ANTY nake ina dariya, shima haka!...

Gaba ɗaya zuciyar ta ajagule take, cikin takaici tace" yanzu dan Allah honey bani da iko akan yarana bisabilillahi yaron nan da lalacewa tunda ya tafi har yanzu yaki dawowa, kamar wanda yaje dangin uwar sa ni dan Allah ka kyaleni naje har gidan na ci mai mutunci tunda bai da hankali..."

Kare mata kallo yayi cike da jin zafin ta yace" Amina zo nan!..." d'aga yanayin da yayi magana ta san abune me mahimmaci cikin dauriya ta zauna kusa dashi haɗi da cewa" gani!..."

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang