_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣3⃣
Kura mai idanu nayi ko kiftwa ba nayi, so nake na tuna a Ina san shi amma kwakwalwata taki aiki, ji nayi kai na ya fara d'aukar zafi nayi saurin dafe kai na da hannuwa na ina jujuya shi, har yanzu idanun na kan shi, gani yana shirin shigewa ciki nayi sauri zabura zan fice ga mota a rufe, da sauri MAN ya rigani ficewa, bakin sa d'auke da sallama yaje ga Kawu na, yana me mik'a mai hannu suka musabaha, sai kuma ya rasa abinda zaice mai...
Kawu yace" ya akayi ne yaro?.." hankalin MAN na mota ya sake waigowa ya dube Kawu kana yace" aa babu komai! .." d'aga haka ya nufo motar...
Kawu ya tsaya cak yana duban motar, ji yake tamkar akwai wani shashin sa dake wajen, da sauri Kawu ya tsayar dashi ta hanyar cewa" dan dakata!!.."
" Ko kana buk'atar wani abu ne?.." da sauri MAN ya kareni ta yanda Kawu na bazai ganin ba yace" a'a Kawu! sai kuma yayi sauri cewa" amm bana buk'atar komai yallab'e!.."
shiru yayi yana sake duban shi zuciyar na harbawa jin ya kira shi da sunan da ya jima bai ji wani ya kira shi dashi ba,
Cike da subutar baki Kawu yace" MUNIBBAT!! ka ganta ne?.."" WACECE?. Dum gaban Kawu ya fad'i cikin juriya ya wuce cikin gida, da sauri MAN ya dawo mota cikin tsoro da firgici ya ja da baya yana me ware ido, gani Aysha cikin tsaka me wuya sai buga kan ta take tana juya shi..
Da sauri ya isa gare ta yana me d'augo ta da dukn k'arfi sa, cikin rud'ewa yace" Aysha!! Aysha! kalle nan ke karki rufe idanun ki, kalle ni kalle ni nace!.." ya fad'a da k'arfin gaske ganin idanun ta na lumshe wa..
da wani mahaukacin gudu ya taka motar...Haka kawai Kawu yaji hankalin sa yaki kwanciya da yaron nan, har ya kai cikin gida sai kuma ya dawo da sauri, sam bai ga fuskar yarinyar ba amma yaga yanayin da yaron yake ciki na tsananin rud'ani, duk yanda akayi ba lafiya ba yana shirin isa gare shi ne shi kuma ya ja motar ya bar wajen...
Yau abun yafi na kullum domin tayi masa magana, cikin kuka da murya ta da bai cika ganewa ba tace" _ka cutar dani ka zalince ni! ka shiga tsakani na da ahali na, sannan ka gudu ka barni cikin mugun yanayi, ka tafi ka bani waje! ko zan mutu a nan banzan bika ba_ .. tana k'arke zancen ta hankad'a shi rami...
A wani hargitsi ya tashi zaune yana nishi da haki, tamkar wanda yayi tsire zufa na tsitsafo mai ta ko ina, d'akin ya bi da kallo gani koma lafiya kalau take kuma ya fara sallati, sai da ya samu ishashiyar nutsuwa ya mik'e ya wuce bayi...
Cikin hikimar zance da dabara Daddah tayi ma Mommy nasiha me shiga jiki da nuna mata illar abun da take, har yanzu tana kan ciyar ta a kwance, a haka AN'NUWAR ya same su, can nesa da su ya zaune fuskar nan kadaram-kadaham, yace" Daddah sannu da huta wa na same ku lafiya?.."
Cikin girma da izza tace" lafiya kalau!.."
" Daddah ya maganar yarinyar nan kuwa?.."
" Ai ban san wata yarinya ba, ko kazo da wata ne ban sani ba?.."
Ya numfasa, kana yace" marar lafiyar nan dana tafi na bari shin taji sauki kuwa?.."
" Me yasa baka tsaya ka gani ba, ka ma bani mamaki wallahi kai da aka turaka k'asar waje dan ka bige dan talaka, me yasa ka damu da ita? bayan watanin da ka dauka baka nan? baka bani ajiyar komai ba in ka matsu da ji kaje inda ka bige ta ka duba nima ban sani ba ta mutu ko tana raye ohho.."
Sam kalaman Daddah ba suyi mai dadi ba, Mommy ta mik'e zaune tana aika mai da hararar kana tace" to kai menene na damun kan ka da wannan abun da ya wuce? shin bana ce ka manta da ita ba? ita ba komai bace bata da kowa bare kace, ka manta da ka tab'a ganin me kama da ita a duniya, ka saki ranka kayi rayuwar ka kamar farko kaji?.." ta ida maganar tana shafa mai kumato...
Daddah ta tsare ta idanu, lallai Ameena ba hankali, yanzu fa ta gama cewa baza ta sake ba, to me takeyi haka kuma?..
A hankali ta mik'e ta wuce ciki abun ta, tana mata fatan shiriya...
Kai tsaye asibiti ya wuce da ita, tamkar yar baby ya haka ya d'auko ta da mugun sauri yake tafiya, ma'aikatan asibitin suka fita da sauri suka amashe ta, ya ga tashin hankali shin kad'ai, haka ya tai sintiri a k'ofar room din...
Sai da aka d'auki lokaci me tsayi kana doctor ya fito, fuskar sa cike da an'nuri yace" Alhamdulillahi a yanzu Bata buk'atar aikin komai, duk yanda akayi yau akwai abinda akayi mata wanda ya haddasa mata iyin tunani me tsaho, da kullum tana gani abun da take so, to da zamu sa ran a ko wanne lokaci tunanin ta zai iya dawowa, bata buk'atar aiki gaskia zata iya tashi a ko yaushe ka kula, da yiyuwar ta mik'e kalau haka muke fata..." ya bashi hannu suka musabaha...
ANTY jin shirun yayi yawa, ga faduwar gaba da take fama dashi, yasa ta fara kiran Man a waya amma shiru bai dauka ba, tun tana jurewa har ta gaji ta fito bangaren Daddah...
Fuskar ta kawai ta duba ta san ba lafiya, cikin yanayi ba dadi tace"
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.