_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 3⃣7⃣
Da salama na shiga shashin nata, shiru babu motsin kowa a palo, cikin na shiga dan na san bazata gaza nan ɗin ba, zaune ta a gefen gado daga gani ta jima a haka domin ta lula duniyar tunani me zurfi, a hankali na zauna a kusa da ita cikin biyayya na kamo hannun ta duk biyu, fuskata cike da murmushi nace" Daddah! tunanin me kike haka?..."
Murmushi ta sakar min tamkar ba abinda ya same ta tace" yaushe kika shigo yar amana ta!?..."
" Kin gani ko Daddah, bama ki san lokacin da na shigo ba, gaskiya ki cire tunani a ranki domin in muka rasaki shikenan mu ganta kan mu..."
Dariya tayi kana tace" babu wanda ya isa ya wuce lokacin sa, in lokaci na yayi ba wanda ya isa ya tsayar dani, abinda nake so daku shine ku k'asance masu mana addu'a, MUNIBBAT!.." ta kira sunan cikin wani yanayi...
Na gyara zama haɗi da ɗaura kai na bisa cinyar ta, kana nace" Na'am Daddah!.."
"" Ina so ki faɗ'a min tsakani ki da Allah, menene alakarki da Aliyu?.."
Shiru nayi babu ko ƙwaƙwaran motsi, zuwa can nace" Daddah yace miki wani abu ne?.."
" Ba tambaya ta nake buƙata ba amsa nake son ji..."
"" _Yana so na Daddah!!_ _nima ina son shi sosai_ sai dai akwai matsalar dake damuna game dashi, Daddah ina mutu'ƙar ƙ'aunar MAN har zuciya ta, amma bazan iya auren shi ba saboda shine burin Kawa ta, AYSHA tana son Mal Haidar so me tsananin, in na shiga tsakanin su tamkar na raba soyayya ne, Daddah muddin MAN zai kasance cikin farin ciki to ba makawa zan iya sadaukar mai da nawa farin ciki, Aysha tafi ni gaskiya Daddah ita ta fara son shi, tun kan na san waye shi take tare dashi, ni take gaya wa damuwar ta a duk lokacin da ciwan sa shi ya motsa mata, tayi kuka akan shi sau babu adadi, me yasa zan rabata da abinda take ƙ'auna? a ranar da zan dawo gidan nan take sheda min irin son da take mai, tayi min musali me girma, Daddah a gaban ta Yayan ta yake baiyya na min irin ƙaunar da yake mun, ga ANNUWAR shi ma yana kan nuna min so! a cikin su waye zaɓi na?..."
Cikin kuka na dakata da maganar ba wai dan raina yaso ba, na so na faɗi duk abinda yake damu na ko hakan zai sa na samu sausaucin a zuciya ta...
ANTY da tun farƙon zancen take tsaye jikin ƙofa, jikin ta yayi bala'in sanyi a hankali ta shigo ɗ'akin, ita ma kusa da Dadda ta zauna ta yanda bazan iya hango ta ba...
Daddah ta shiga shafa min kaina alamar rarashi, har sai da ta tabbatar nayi shiru kana tace" au ke saboda wannan ƙaramin dalilin zaki cutar da zuciyar ki akan abinda take buƙata? shin a tunaninki in kikayi haka MAN din naki zai yafe miki? ko ana gaya miki haka ake sadaukarwa? MUNI MAN fa ke yake so ba Aysha ba, hasali ma bai san tanayi ba, kema kuma kina son MAN to in baki faɗawa Aysha gaskiyar zance ba, kika sadaukar mata da SOYAYYAR ki domin tayi farin ciki har abada baza ta taɓ'a tunanin kinyi ne domin ta ba, tunda bata san abinda ya faru ba, musali in ke kince bakya son shi, kinyi ne domin Aysha ta samu shiga ko ba haka ba? to shi kuma Aysha ba tsarin sa bace kina tunanin zai so tane har ya aure ta? duk da ke kin rabu dashi ne domin ta! ba yanda za'ayi ya aure ta tunda bai san tayi ba, yarinya ta yana da kyau ki nutsu ki sauya tunanin tun wuri, MAN shine yake miki son gaskia, MUNI ko da wasa karkiyi wasa da soyayyar MAN a gareki domin nan gaba zaki gane abinda nake nufi, yana miki son so! shine wanda ya san ciwan ki, shine wanda zai riƙe miki maraicinki, ki bawa zuciyar ki zabin ranki karki bari wani bazan tunani ya haramta miki farin cikin ki, ba wai ina gaya miki haka ne dan ki aure jikana ba a'a iya gaskiyar nake faɗ'a miki a matsayi na na kaka a gareki, kije kiyi tunani wataƙila ki gano gaskiyar!..."
Jiki na yayi mutu'ƙar yin sanyi da kalaman ta, tabbas Aysha bata san akwai wata halaƙ a tsakani na da MAN ba, to in haka ne ni nake damuwa da damuwar ta ba tare da ta sani ba, kawai zan amince dashi in yaso daga baya sai na sanar dashi AYSHA tana son shi, in da rabo sai ya aure ta shikenan kowa ya samu cikar burin sa, amma ta yaya? bazan iya zaman kishi da AYSHA ba, tana da zafin kishi haka nima bana ƙaunar naga ko wace mace a tare dashi matsawar ba mahaifiyar sa ba, to ya zanyi yanzu? Me zan ce mata game da yayan ta da yake dakon soyayya ta? me zan cewa ANNUWAR in ya san abinda yake faruwa?..."
" Yarinya ta karki wahalar da kan ki fa, amsar a baiyyane take ki so me sanki tsakani da ALLAH, karkiyi ruwan ido kinji!..." Cewar ANTY na, ƙunya ta kamani a dan ƙunyace nace" yaushe kika shigo ANTY?..."
Ta harareni cikin wasa tace" kina can kina aikin kuka taya zaki sani, to yau dai abinda ake boye min na sani!, Daddah baƙuwar ta iso shine nazo na faɗ'a miki yanzu zan saka a rakota, ta gaidaki..."
Murmushi tayi kana tace"" to ba damuwa, memakon ki taho da ita kawai..."
" Tashi muje to!.." ta faɗa min tana mikewa tsaye...
Daddah ta harari ANTY cike da tsokana tace" au yau naga wariyar launin fata, wato na shawo miki kan yarinyar ki shine zaki ɗauke ta ko? to ke MUNI tashi kibi maman ki tunda bata son zamanki dani..."
A ƙunyace ANTY ta fice a ɗakin, nan Daddah ta cigaba da rarashi na, da nuna min ilar abinda zanyi, d'aga ƙarshe na shiga bayin ɗ'akin ta domin kimtsa kaina, ita kuma ta fice falo...
A takance dai haka muka ringa samun sabani da AYSHA bamu haɗ'u ba, gashi ANTY ta cika ta da labarin Baby, ta matsu sosai taga Baby sai dai kashi duk lokacin da zamu haɗu da ita, to koni na bar wajen ko ita ta bar wajen, a haka har ta shafe sati a gidan, ko MAN bata taɓa gani ba amma tun shigowar ta taci karo da mayan picture din su a babban falon gidan, kullum fatan ta shi ne ta ganshi ko taga baby...
Muna zaune tare dashi, duk lokacin sa zai ambata mun kalmar so ji nake kamar ba dani yake ba, gani nake tamkar karya yake domin duk abinda yake cewa bana ganin sa a tare dashi, ya kalleni a ɗan gayen ce yace" ina so ko daddah ta tambayeki waye zaɓinki kice mata nine kinji!.."
" To insha Allah..."
" Yauwa tawan tashi muje ciki lokacin cin abinci yayi.."
Gaba ɗaya jama'ar gidan su haɗu ciki har da Aysha daga zauna a kujerar dake kallon ta MAN, sai wani rawar kai yake...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce yar gatan baba habu💃
KAMU SEDANG MEMBACA
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Cerita Pendeklabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.