_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣6⃣
Tsaf na haɗa kaya na, cikin ƙwarin gwiwa nace" kiyi haƙuri ANTY nima bazan so 'na tafi na barki ba, amma tafiyar tawa itace mafi alkhairi tunda na shigo cikin ku kullum nice sanadin ɓacin ranku, zanje 'na zauna ni kaɗai koda su Kawun basu dawo ba, nayi imani da Allah Mommy bata taɓa marinki ba amma ta sanadiya ta, a gaban idona aka marar min *mahaifiya!!* amma ban iya aikata komai!..." kuka yaci ƙarfina, na share ƙwalla ta, na kalle Anty da take kallon gefe ko bata faɗa ba na san kuka take, cikin jan numfashi nace" *eh na san komai zuwa yanzu, ke ƙanwar baba na ce ko?*.."
Da sauri ta juyo fuskar ta fal mamaki tace" baby! ya akayi kika sani?..."
" Mama! karki musa mun, naji da ƙunne na, sannan 'na gani a zahiri kema kina da irin pic ɗin da baba ya bani a matsayin kaka ta, haka ne?..."
Tsareni da ido tayi 'na wani lokaci kana tace" Eh haka ne! 'na so nayi ido biyu da ɗan uwana amma Allah bai nufa ba, a yanda jama'a suka sheda, kuma aka gani mahaifiyar mu ta rasu, amma a zahiri mahaifiyar mu bata shiga cikin motar ba, mahaifun mu ne kawai a ciki sai wata baiwar Allah dake zaune a kusa dashi, a tunanin shi innah ce sai da tafiya tayi nisa, sannan ya ankara itama anata bangaren tana idar da sallah taga babu mota babu dalilin ta, Inna tayi kuka sosai sannan ta hawo wata motar domin bin sahun su, a haka har Allah yasa ta hange su bata da ko fice a hannun ta wanda zata biya me motar da take ciki, dan haka ta nemin alfarma akan ya tsayar dashi zata koma can, haka kayi kuwa Baban mu yana kallon ta, itama tama kallon shi fuskar sa cike da murmushi, basan abinda ke faruwa ba ƙwatsam sai ga motar da babanmu yake ciki ta dake titin baban gida, motar su Innah kuma tayi wani irin hantsilawa, a haka ta ringa gangarawa har ta faɗa wani ƙaramin kauye dake rangara, ita kaɗai ce ta rayu a cikin motar ta shiga mayuwacin hali sosai, hankalin ta ya gushe da taimakon wani bawan Allah Innah ta samu kulawa, sai da inda matsalar take sam tunanin ta ya gushe bata iya tuna komai, haka kuma bata ganewa amma ba hauka take ba, a haka Innah ta ci gaba da rayuwa yau da lafiya gobe akasin haka har lokacin haihuwar ta yayi, gidan da take zaune sun mutuƙar tausaya mata ganin irin wahalar da take sha, Allah cikin ikon sa ta samu lafiya, haihuwa yazo mata da warakar ciwan ta, Innah ta riƙe ni tamkar wata yar sarauniya, gidan da muke zaune sun fifitani akan yaran cikin su, na samu gata iya gata uwa uba ga tarbiyar sun bani ilimi isalamiya da boko, kullum Innah cikin bani labarin Yaya na take, bata da wani buri a rayuwar ta sai na fatan ta sake ganin shi ko da sau ɗaya ne, girma ya kama ta ta tsofa sosai kullum maganar ta Yaya na, duk da a lokacin bani da wani ƙarfi haka na ringa fafuta domin na samu mata shi, nayi iyaka bincike na ban haɗu dashi ba, har na cire rain samun shi, ƙwatsam Allah yayi ma Innah cikawa..." Cikin shasheƙa ANTY ta share kwallar ta haɗi da cewa" unguwar mu ɗaya da su Daddah, ba laifi gidan da nake suma masu arziki ne sosai gashi Innah ta tara min dukiya sosai, kullum neman Yaya na nake ko Allah zai sa mu gana, a haka har nayi aure ban dai na nema ba, har muka koma garin Abuja, a haka Allah ya haɗani da maƙonta ku a wajen wani biki nan take bani labarin ɗan uwa na da irin k'addara da ta same shi, a ƙarshe ta sheda min rasuwar sa, nayi bakin ciki marar musaltuwa na shiga damuwa sosai, abu ɗaya ne yake faran ta min rai shine yana da ƴa guda ɗ'aya tal mace amma Kawun ta na wajen uwa ya ɗauke ta, duk da ban taɓa gani yarinyar ba amma soyayyar ta shine yaza me min abun ado, a ko wannan lokaci, fatana shine na ganta cikin hikima na ringa bin didigi har na gano inda kuke, sai da ban taɓa ganin ki ba kulle yaumin nazo sai na tarar da gidan babu kowa, haka zan gaji da jira na tafi, a haka har Allah ya kawo mana AYSHA, wata irin soyayya nake wa yarinyar tun daga ganin farko, nafi kowa shiga damuwar halin da take ciki, wani abun farin ciki ashe ƴata ce ban sani ba, Allah ya kawo min ita har cikin gida, lokacin da kika samu lafiya a sannan ne na samu damar ganawa da Shafi'u na faɗa me koni wacece amma banyi yunƙurin shiga tsakanin ku ba, har sai kin buƙaci haka da kanki, shi da kan shi ya sheda ni din jininki ce yayi murna sosai a ƙarshe ya nemin na bar mai ke duk da ban amsa ba a lokacin sabida zuciya ta na tuzirani dole na haƙura na koma gida zuciya ta cike da begen ki, MUNIBBAT me sunan manya ke ƴata ce! shin zaki iya tafiya kibar mahaifiyar ki?..."

STAI LEGGENDO
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Storie brevilabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.