_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣2⃣
Na sake riƙe shi da kyau, idanu na fal ƙwalla tsananin soyayyar sa tana ribata ta...
Cikin hikima ya zame hannun shi daga nawa, a hankali ya sulale ya bar falon, wani irin kuka ya ƙuɓuce mun...
ANNUWAR ban san yanda suka ƙare da mutanen gidan ba, amma da dukn alamu sun hukunta shi domin yanzu ko ganin sa ban cika yi ba...
A cikin wata biyu da suka wuce abubuwa da dama sun faru, masu daɗi da akasin haka...
Gaba ɗaya yanzu bana ganin mazan gidan, babu abinda yafi ɗaga min hankali samu da rashin MAN a tare dani, Anty na ta sauko amma ba kamar yanda na santa ba...
Ƙwance nake akan cinyar Daddah, muna hira tamkar ana jeho shi daga bakin baka, ya faɗo ɗakin fuskar shi babu wani annuri yace" Daddah ina wuni?..."
Ciki-ciki ta amsa da lafiya..
"" Dama zan faɗa miki ne na kai ƙuɗin aure na kuma sati biyu nace ina so aka saka..."
" Dariya tayi tana mai kallo mashirmaci tace" ka kyautawa rayuwar ka a'i, waye ubanta to?..."
Ya saki wani ƙyasaitacen murmushi kana yace" ita ba ƴar kowan kowa bace, face ƴar matsiyata! bata da wani gata domin ko mariƙanta ma sun garara riƙeta, Daddah ba kowa bace face yarinyar dai dana faɗa miki ƙwanaki zan taimaka mata!..."
Kamar yanda ya sunƙuyo da face d'in sa yana magana, haka ta wanke sa da wani mugun mari, kafin yayi wani yunƙuri nima 'na sakar mai nawa marin zuciya ta na tafasa, cikin tsakanin baƙin ciki da matsananciyar damuwa, nace" kai waye!??? da me kake taƙama ne? duk duƙiyar da ba kai ka tara ta da kan ka ba suna ta ohho! domin kuɗin magadane! akwai babban matsiyaci ma irinka wanda zuciyar sa ta mutu akan abinda bashi da iko akai! kullum maganar ka akan ƙuɗi, kuɗi dai ko? bazan san kai me kuɗi ba ne har sai ka tashi ka nema da kan ka, me mataciyar zuciya kawai!!..."
Tsananin mamaki na da tsana ta shi ya hana shi aiwatar da komai, kallo na yake cikin matsananciyar kiyayya ta, 'na juya zan wuce ya wani fizgoni gaba sa kafin 'na daidaita tsawa ta, shima ya zuba mun wani ingarmar mari me hawa ka.
Bai gama sauke hannun sa ba, shima yaji saukar wani bahagon mari me tsakanin ƙara da zafi...
ANTY CE a tsaye akan shi, zuciyar ta 'na tafasa ta buɗe baki za tayi magana. itama taji saukar nata marin cikin mutuƙar mamaki da mutuwar tsaye gaba ɗaya mu muka juya, idanun mu a waje...
Tsananin tsorone ya saka 'na saki wayar nima, mamaki al'ajabi ƙarar a fuskanta.
Jamaa waye zaiyi wannan aika aikar 'dan Allah?
bari na gani su waye zasu ci gari🙂
Comments
And
Shared
Pls
Mrs Abubakar ce💕
VOUS LISEZ
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Nouvelleslabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.