Chapter 19

62 5 1
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*


BISMILLAHI RAHMANI RAHIM

🅿 1⃣9⃣

Shiru tayi mata zuciyar ta na zafi, Daddah ta dafa kafaɗar ta haɗi da yi mata alama tayi shiru...

" Hajiyar mu, ina son magana daku dan Allah?.." ta faɗa a raunane...

" Nusaiba ki shiga ciki gani nan zuwa.."

Da sauri tace" Hajiya har da ita nake nufi.."

Fuskar su babu yabo ba fallasa suka iso inda take, Mommy ta sake gyara zaman ta cikin nuna jimami tace" Hajiyar mu Ina so zanyi miki tambaya ne ɗaya zuwa biyu in babu damuwa!.." da raunaniyar tayi maganar..

Hajiya ta sake gyara zaman ta cikin nuna ita wata ce tace"  ina sauraron ki?.."

Mommy ta sake marairaicewa kana tace" magana ne akan abunda ya faru ƙwana kin baya, nayi tunanin sosai akai tabbas na aikata ƙuskure musamma dana na nuna fifiko akan yara na, dan Allah Hajiya kiyi haƙuri muddin abinda nayi bai miki dadi ba,  ke uwace a gare ni domin duk duniya nan bani da tamkar ki, ke kaɗai kika rage min a cikin iyaye na mata, ni amana ce agareki kuma  ina iya ƙoƙari na wajen gani na faran ta miki, amma me yasa kullum bakya  gani ne Hajiya, wallahi duk abinda kika ga inayi ba wai dan na rainaki bane ko rashin darajaki a'a Ina yin sa nee kawai dan martabar ƴaƴa na, har zuciya ta bana so talaka, bana ƙaunar naga ya raɓe mu bare kuma har na zauna dashi a inuwa ɗaya, dan Allah nima kiyi min adallaci kar kuce zamu zauna gida ɗaya da wannan abun!!.." ta faɗa tana nuna ni...

Hajiya ta kama baki cike da mamakin Mommy, " a yanzu kam lamari ki sai addu'a yarinya, da farko kin ɗauko magana kamar ta masu hankali a ƙarshe kuma sai kika bata wasan ki, har abada ba zan wulakan taki ba ko na tozartaki domin kamar yanda kika ce ƙanwa ta hannu da hannu ta danƙa mun amanar ki, sanin kanki ne ban taɓa nuna miki bambanci ko da sau ɗaya ba, kamar yanda na ɗauki su Jan Zaki haka na ɗauke ki, ban koya miki ƙin wani ko aibata wani ba, can makarantar da kikayi nan kika koyo mugun halin nan, kuma ina miki fatan samun sauki in larurace Allah yaye miki, adallaci ɗaya xan  miki shine yarinyar bake zaki riƙe ta ba, amma fa zama a cikin mu tamkar anyi a gama ne, ki godewa Allah akwai yarinyar arzikin nan a gidan nan, dah wallahi tallahi kinji na rantse ke zakiyi jinyar ta har ta warke tunda wan can ɗan ido nee ya make musu yarinya, yana ina ne ma wai?..."

Mommy ta ƙarewa Dadda kallo cikin shagwaɓe fuska tace" nayi imani da Allah, da ke kika haife ni bazaki bari nayi ɓacin rai har haka ba, naji a dah kin nuna mun so yanzu kuwa ba abinda nake fuskanta a wajen ki in ba muzgunawa ba, shikenan Daddah kiyi min ko ma meye amma karki manta ni amanace kuma marainiya alƙawari kika dauka na faranta min.."  ta ƙarke maganar da fashewa da kuka...

Zuciyar ta ce tayi mata wani irin nauyi, kalaman Mommy suka taɓo mata wani tsohon taɓo a zuciyar ta, take jikin ta yayi sanyi tayi shiru bata ce komai ba, kukan Mommy na shigar mata cikin ƙwanyar kan ta, a hankali ta dube ta sai wani irin tausayin ta ya rufe ta...

Ta dube Nusaiba dake zaune cikin jimami da tausayin MUNIBBAT, sai ta ɗanne tausayin Mommy fuska a haɗe tace" dama kin taimaki kan ki kiyi shiru dan ba janye kudiri na zanyi ba, ɗan ki ne ya make ta har ya ta samu matsala, Dole ta zauna a nan har Allah ya kawo ƙarshen abun a san nan nee zan amince ta koma inda ta fito,  maganar kuma bani na haifeki ba kije ki tayi ni duk abinda zanyi inayi sa nee domin Allah ba dan mutun ba, Allah yana gani in ni na cuce ki,  in kuma ke kike cutar da kan ki ke kika sani..."

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now