_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣8⃣
Bai faɗawa kowa zaiyi aure ba sai ganin shi mu kayi da matar sa, hankali Mama yaƙi ƙwanciya tun yana jure abinda take har yazo yana mata faɗa a sirince, amma duk a banza Mama taƙiji taƙi ƙwantar da hankalin ta su zauna lafiya, ANTY Rabi itama bata da sauki ko kaƙ'ai akan kishi, duk wasu hanyoyi na rashin mutunci da kisan mimiƙe ta sani, a wajen Abba ita macece me mutuƙar haƙ'uri da biyayya, amma da zarar ya fita macece me tsiwa da masifa wace bata jiran kaɗ'ai, wallahi ANTY Mama RABI tafi maman mu jidali nesa ba kusa ba, ko Mama tayi shiru a wani abu wani abu ANTY bata shiru, domin sam bata da hakuri ko kaɗ'ai...
Abba mu ya samu ƙarin girma a wajen aikin sa albashin sa ya riɓanya, kuɗi suna shigo mai ta ko ina a hankali ya sauya mana komai na gida, muma aka sauya mana makaranta, inda ka tsaye shi yake biya miki kuɗi makarantar ki kema, Mama taƙi haƙuri akan wannan nan ma sai da tayi magana, duk dan sabida a zauna lafiya suma duk wata yana basu wani abu a matsayin ihsani...
Lokacin da ya sauya saban gida, haka muka tataro muka dawo nan da zama, wannan ɗakin da kike ciki anyi masifa akan shi, domin Mama cewa tayi bata san zance ba, duk wata lalaɓawa da kika san Abba nayi mata yayi amma a banza, ANTY Rabi kuwa tunda tace Allah ya sanya alhairi, bata sake maganar ɗakin ba, domin kayan dake dakunan su yafi wannan kyau da tsada har da inganci...
Kullum ciki yada magana Mama take, Abba baya kulata a cewar sa tana da matsala, ba tare da Abba ya sani ba Mama ta siyar da komai na ɗakin nan, ya zama na babu komai a cikin sa, duk da haka bata haƙura ba kullum rigimar da zatayi daban...
A ɓangaren guda kuma ga faɗan kishi da kullum sai anyi shi, a gaban mu suke komai...
Saban salon da ANTY Rabi ta fito dashi, shine na kamamu tayi mana duka haka nan ba tare da muyi lefin komai ba, in Mama tayi magana sai tace ƴayan mijinta ne ta da ikon da zata hukunta mu duk lokacin da buƙutar hakan ta taso, muna shan wuya a hannun ta sosai, ita bata abu a boye wani lokaci ma a gaban Abba take dukan mu a cewar ta muyi lefi, shi ko sai dai yayi tai mana faɗa akan muna jin magana, to anyi haka ya kai sau uku Mama mu tana zuba ma Abba ido ko zaiyi wani abu aka, shiru babu alamar ya san me take...
ANTY kin dai san yanda Mamanmu take mutuƙar ƙaunar mu, haka ta tayar da hankalin kowa gidan nan, kullum da irin abunda take fitowa dashi, duk sabida mu! gani taƙi tayi hankali yasa shi ƙaro musu wata abokiyar zaman suka zama su uku, ANTY halimatu bata da matsala ko kaɗai domin ita gaba ɗ'aya mutanan gidan basa gaban ta, sai ta wuni a ɗ'aki ma bata fito ba, in kinga ta a waje to lokacin zafi ne ko wani dalili ne ya fito da ita da zarar ta gama kuma zata koma ciki ta rifu ɗakin ta, wannan abu yana ƙonawa Mama rai amma ta ɗaure, kishi tsakanin ta da ANTY Rabi ne kawai babu sausauci, duk wani abu da suke Abba yana sane dasu gaba ɗaya ya tatara su ya watsar gefe guda, ya cigaba da harkokin gaban sa babu wace bata san da zamanki a gidan nan ba domin kullum da sunaki a bakin sa...
Fitin-tinu iri-iri Mama take kunowa, zuciyar ta taƙi dangana da wannan aure da yayi a cewar sa shine hukunci da ya dace da ita, ranar gidan ba kowa duk sun tafi anguwa dagani sai Mama ko su Hanna basa nan, a gaba ido na Maman mu ta sakawa ɗakin ANTY Rabi wuta, sai da ya cinye tass sannan tayi waje neman ɗauki a cewar ta wutar lantarki ce, abinda bata sani ba Abba ya saka CC camera, kaf anguwar nan babu wanda baiyi mamakin yanda gobar nan ta tashi ba, Abba baice mata komai ba illa gyara dakin nan naki da yayi yace ANTY ta zauna kafin a gyara mata nata, to tace hankalin ta a ƙwance domin ta san waye mijinta...
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.