_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣6⃣
Tsananin firgici, da ruɗani shine ya baiyyana akan fuskar ta, jikin ta tamkar ana kaɗata da majajawa, hannun ta na rawa ta miƙe cikin tashin hankali tana mai wani irin kallo me cike da alamomin tambaya, cikin sauri Kawu ya juya mata baya haɗi da share ƙwallar sa, a hankali tazo ta bayan nasa ta rungume shi ramm, tana wani irin kuka kamar ranta zai fita a gangar jikin ta...
" Dan girman Allah kaji tausayi na! kar ka mayar dani bazawa! kayi haƙuri Abban Hanna...?" cikin wani irin yanayi tayi maganar...
To kun dai sai halin maza, musamma Kawu da ya ɗauki watani ba tare da yaji shi a duniyar wata ba...🤭
Shasheƙar da take mai a bayan kunne shi ya haifar mai da wata muguwar kasala, take wani baƙon lamari ya ratsashi, cikin dakewa ya fara ƙoƙari rabata da jikin sa nan fa suka hau kokawa, yana ɗagowa da nufi yi mata masifa tayi saurin cefke mai.....🤭
*******
Washe Gari...
Da sasafe MAN ya fito domin yau yake sa ran haɗu wa da Kawu na, waje daddah ya fara zuwa bayan tayi masa Addu'a, ya wuto nan shashin mu a sa ilin Anty ta gyara ni duk da ba wata ƙwalliya tayi mun ba amma nayi mutuƙar yin kyau a cikin wani pink din material ɗinki ya amshi jikina sosai, ta ɗauko blue din hide ta ɗaura min, gaskiya na haɗu iya haɗuwa ta sakani a gaba sai addu'a take tofa min wai maganin baki, ni kam ina zaune kamar an dasani sai wasa nake da teddy ban ma damu da miyan da take tofa min ba...
A hankali MAN ya shigo ɗakin bakin sa ɗauke da sallama, sun gaisa da ANTY kamar yanda suka saba, daga bisani ya fara tsokana ta, har ya juya zai wuce nayi saurin bin bayan sa bai kula dani ba sai da ya kai ƙofar fita ya juyo, aiko mu kayi karo dashi...
A razane nayi baya zan faɗ'i, inda shi kuma ya dafe goshin sa da hannun sa, na gama sadaƙarwa na kai kasa ga mamaki na sai jina nayi a jikin mutun, aiko tsoro yasa na ƙan-ƙame shi...
MAN ya ɓata fuska cike da jin haushin ƙannasa yace" AN'NUWAR!! kana da hankali kuwa? kalle fa yanda ka anagizani!..."
A hankali ya gyara min tsewa ta cikin halin ko in kula yace" kai baka ganin baby na! zata sha kasa!!! salon ka sake ja mana zagi a wajen tsohowar can, ai gara kai ka faɗi akan ita..." tunda ya fara maganar bai kalle inda Man yake ba, ni din dai ni yake kallo...
Ina gama watsakewa nayi saurin koma inda man yake cikin turo baki nace" ni sai na bika!.."
Ɗauke idanun sa yayi akan AN'NU yana sauke su akai na, zaiyi magana nayi saurin komawa ta gaban sa ina me ƙifƙiffta zara-zaran idanuna, cike da shagwaɓa nace" ni dai zan bika!..."
AN'NUWAR yayi sauri zuwa inda nake cikin taushin murya yace" Baby ki kyale MAN yayi tafiyar sa, muma zuwa anjima sai muje yawo ko?..."
" _lallai ma yaron nan wato dan ƙwana biyu ina sakar mai shine har ya samu damar zuwa gaba na yana cewa wai ta kyale ni, kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi kenan tabdi..."_ Duk a zuci yayi maganar nan..
Cikin sauri ya kamo ƙuguna yana me jana ɗaya gefen yace" dama ai dake zai wuce.."
ko kallon inda ANNUWAR yake bai sake ba ya jani muka fice...Anty dake zauna akan kujera tana kallon abunda ya faru, ta ɗanne dariyar ta a fili kuma tana baiyyana murmushin ta har cikin zuciyar ta yau bata so taga nayi mata nisa amma sabida farin cikina shi yasa bata hanni ba...
Sai bayan mun fito kuma, ya fara tunanin inda zai ajiye ni, yaje ya dawo ba tare da ana samu matsala ba, dabara ce ta faɗo mai kawai sai ya saki murmushi, bai zarce ko ina ba sai gidan mu...
Bamu ɗauki wani lokaci ba muka isa, shi kaɗai ya fita a bakin ƙofa ya tsaya, yayi sallama ta ciki aka amsa mai, kana ya dawo cikin mota ya zauna, kaffe ni yayi da idanu babu ko kifftawa a hankali ya kamo hannu 'na cike da sha'uƙi yace" kina so 'na!!??..." cikin taushi da ƙauna yayi maganar..
Murmushi nayi masa cikin alamon jin dadi nace" a... Fitowar kawu na ya dakatar dani...
Jim kaɗan sai ga Kawu na ya fito, cikin sakin fuska suka gaisa da MAN, gani maganar me mahimmaci ce yasa Kawu ya koma ciki, sai gashi da abun zama...
To kamar dai yanda suka tsara komai shi da daddah haka ya ƙwashe komai ya faɗawa Kawu na, inda a ƙarshe ya daurawa da cewa" yarinyar tana tsananin ƙaunar ka, duk da tana cikin wani hali hakan bai sa ta manta da sunan ka ba, likitoci sun sheda mana muddin muna so ta warke cikin sauki, lallai sai mun nuna mata abun da tafi so a rayuwar ta, shine Daddah ta aiko ni gareka akan 'na faɗa maka komai ko zuciyarka zata samu salama, tunda muke da ita bata taɓa nuna wata alama tajin sauƙiba har sai ranar dana zo da ita nan ta ganka, a ranar 'na sheda kai na farin cikin ta...
Kawu a yanzu muna buƙatar taimakon ka ne, ba kuka ba, kayi haƙuri ba muzo maka da wuri ba hakan ya faru ne sabida wata matsala da aka samu, mun sha wuya sosai kafin mu gano nan din, amma da tare zamuyi jinyar ta, a madadin ɗan uwana da iyaye 'na ina me baka haƙuri akan hakan!..."
Na gaji sosai da zaman motar ganin har yanzu shiru bai dawo ba, sai na fata taɓe-tabe a cikin motar cikin sa'a 'na bude murfin motar, a hankali na zuro ƙafa ta ɗaya na jima a haka ina kallon inda ya shiga....
Har lokacin Kawu 'na hawaye yake zubar, na tsananin tausayi 'na tabbas yasan duk wuya duk rintsi bazan manta dashi cikin sauƙi haka ba, ya kasa cewa komai sai aikin share ƙwalla yake...
Ko da nazo bakin ƙofar sai na tsaya, ina leƙwa a hankali kuma 'na sako ƙafata ɗaya, tunanin 'na fara amma ba wai can ba, tun daga ranar da Kawu na yayi fushi dani har zuwa ranar da ya koreni har lokacin sa mota ta makeni, bana iya tunawa sosai ɗishi-ɗishi nake gani a haka 'na shigo zauren gaba ɗaya ina dafe bango...
Gaba ɗayan su miƙewa sukayi tsaye, MAN yana tsakanin mamakin yanda akayi 'na iya buɗe motar, inda Kawu 'na! yake mun wani irin kallo nayi ƙewarki jikin sa 'narawa hawaye ba gudu akan ƙuncin sa, ganin zan faɗi suka tahu a tare da nufin taroni, kafin MAN ya kawo hannu Kawu 'na! yayi saurin ture shi na faɗo jikin sa, idanuna akan sa face din sa...
So nake na tuna shi, amma na gaza gani sosai, cikin rawar baki yace" MUNIBBATU NA!!! kece? dama zan muke haɗuwa? ashe da gaske yake? kece ? Ke kalle ni nan nine nan Kawunki? kin gane ni? ki kalle ni nace karki rufe idanunki sanyin idaniyyata dube ni nace Kawun ki ne kin tunani ? ko zaki manta kowa a'i na san bazaki manta ni ba ki kalle ni nace!!..." ya faɗa da ƙarfi...
Tunda 'na faɗo jikin sa nara iya gane komai nawa, tun farkon rayuwa ta na fara har zuwa lokacin sa mota ta makeni, cikin ƙaraji nace" Kawu na!!!!...." Take kuma na saki gaba ɗaya 'na tafi duniyar suma...
Hayaniyyar mu ne ya jawo hankalin Anty 'na dake ɗaki jin kamar da gaske murya tace ba gizo nake mata ba, zuciyar TA ta buga da karfin gaske, cikin kiɗima tafito zuwa zauren a ruɗe kwance TA same ni shame-shame a jikin Kawu ba na tafi duniyar suma, itama suman tsaye tayi dafe da kirji...
Wani irin tausayin mu ne ya ratsa zuciyar Man dake tsaye akan mu, cikin daure yace" Kawu tana buƙatar ganin likita a yanzu...
In fatan na wanke kai 'na a wajen ku👏
Comments
Shared
Mrs Abubakar ce😘☺
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.