_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣5⃣
Ƙare mai kallo tayi sosai bayan ya gama maganar, kana ta sauke ajiyar zuciya haɗ'i da cewa" MY SON! ba wai naƙi ta taka bane, a'a ina hangen abunda zaije ya dawo nan gaba, bazanyi fatan Auta tayi aure a sako min ita ba, dan haka kai ma bazan yarda ka aure ta ba, bare har saki ya shiga tsakanin ku, bazan so a fara irga maka aure ba kana ji, daga yanzu bana so ka sake magana akan ta inda na isa da kai! shi kuma Yayan naku zaizo ya same ni..." ta faɗa zuciyar ta ajagule...
Langwaɓewa yayi a cinyar ta kamar wani ƙaramin yaro, yace" Mommy ya maganar Hafsat din?.."
Ajiyar zuciya ta sauke tace" ta nan har yanzu, zuwa anjima zaka kaini gidan su..."
Muna zaune gaba ɗaya, hira suke cikin jin daɗi yayin da nake gefe ina tunanin Kawu na, ni ban saba da Dady ba shi yasa in naga Auta tana wani abu sai Kawu na ya ringa faɗo min a rai, ƙamshin turaren tane ya dake hancin kowa, babu wanda bai kalle inda sautin takun ta yake fitowa ba, a zuciyar sa yayi hamdala da samu mace irin Mommy ga ANTY a gefe, ya saki murmushi cikin jin daɗi yace" Hajiya! ga mutuninyar ki nan fa zuwa..."
Shiru Daddah tai kamar bata ji me yace ba, da salama a bakin ta shigo falon, bin ko ina take da kallo kamar me neman wani abu, ta yamutse fuska cikin yanga tace" Sannu ku da hutawa!..."
" Yauwa." suka faɗa a tare!...
Shiru ne ya ratsa wajen, a hankali na miƙe zan gudu ɗaki na domin har ga Allah ni Mommy tsoro take bani, naji murya Daddah na cewa" MUNI! wai me yake damunki ne yau? gaba ɗaya naga baki da sukuni.."
Murmushi nai kaina a ƙasa nace" ba komai Daddah! kawai bana jin daɗin yanayi ne!.."
" Yo ina zakiji daɗi, tunda ba sabawa akayi ba! wallahi ina mutuƙar takaicin ganin gilmawar yarinyar nan a gidan nan, fisabilillahi a rasa wace za'a ƙwaso mana sai mahaukaciya, yanzu dama akan wannan abune ranar dana dawo na tare kuma dakar min yaro, shi da yake ɗan asali wanda ya gaji arziki gaba da baya, yaro ɗan madara me aji da babban matsayi..." Cikin tsananin masifa take maganar...
Auta ta mike jiki a sanyaye ta fice a falon, ya rage dagani sai su dama mazan basu shigo ba, ANTY, Daddah, Dady, Mommy sai ni...
Dady bai ce komai ba ila zaman shi da ya gyara, ta ƙare musu kallo a masifance tace" magana nake fa! naji duk kunyi min shiru kuna kallo na!.."
" MUNIBBAT! zo ki wuce ciki!.." cewar ANTY..
" Ciki ina???." Mommy ta faɗa a ƙausashe..
Jikina yayi bala'in sanyi, daƙar nake ɗ'aga ƙafa ta haka nazo wucewa ta kusa da ita, kai na a ƙasa aiko tai saurin danƙo hannu na cikin mutuƙar ɓacin rai tace" KE!! nan yayi miki kama da gidan gadonki?..."
Da sauri na girgiza kai alamar AA domin na firgita sosai da roƙon da tayi min, ta ɗaura da cewa" yarona yayi sanadiyar zuwanki, nayi haƙuri an riƙeki har kin warke to zaman uban me kike kuma? baki da iyaye ne? ko baza su iya riƙ'eki ba ne? ko baki da dangi ne?..."
Kuka kam tunda ta riƙeni nake faman iyasa, cikin shasheƙar kuka nace" kiyi haƙuri Hajiya!.."
" Ba haƙ'uri nake nema ba, ki tatara kayanki ki bar mun gida kar nake ganin ki, a cikin gida na! tunda babu gadonki a ciki 'in ba haka ba kuma zan gigita miki rayuwa..."
*" Gidanki ko nawa? yaushe ya zama naki?.."*
Cak ta tsaya cikin mutuƙar mamakin mijin nata, bakin ta a buɗe zuciyar ta na bugawa tace" please bana so ka shiga cikin wannan cas din! ka barni na gyara a hali na!.."
" ANTY! zo ki kai yarinyar ki ɗaki!..." ya faɗa yana me ƙurawa Mommy idanu alamar tayi babban lefi!..."
Mommy taƙi saki na, domin tayi min mugun riƙo, sai da ANTY tai da gaske sannan ta ƙwaceni a hannun ta, shima Daddah ce ta miƙe shine dalilin saki na da tayi, ina kuka ANTY ta turani muka bar falon zuciyoyin mu a jagule...
Daddah tazo har gaba ta tace" Amina! a wannan karan bazance miki komai ba, tunda a gaban mijinki kikayi..." ta wuce a abun ta...
Mommy taja da baya cike da fargaba, Daddy ya shafi hancin sa da bayan hannun sa, alamar ranshi a ɓace yake yace" baki bani amsa ba yaushe ya zama gidan ki!??..." A yanzu a ƙausashe yake maganar...
" Honey baka gane bane!.." ta faɗ'a tana miƙe hannu zata shafi kirjin sa, yayi saurin matsawa baya Mommy ta zare ido cikin razani, tace" Abdul!!!.."
" Amina!! kin sha aikata abubuwa da dama a gaba na ba tare da nayi miki wani hukunci ba, ki sani a yanzu bazan lamunta ba! Ameena! ki kiyayye ni wallahi akan marainiyar nan zan saɓa miki!..."
Mommy ta ware ido cikin mutuƙar tsoro tace" akan wannan yar mitsiyatan kake ikirarin saɓa mun?.."
" Ameena!!!..." ya faɗa yana ware hannun shi zai kifa mata mari, Mommy tayi saurin kare fuskar ta hawaye na bin k'uncin ta, tsakanin miji da mata sai Allah, jikin sa yayi sanyi gani yanda take zubar da ƙwalla hankali ya sauƙe hannu shi, gajeran tsaki ya saki kana ya bar mata wajen da sauri...
Mommy ta share ƙwallar ta cikin ɓakin ciki tayo shashin ANTY a zuciye...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce
BẠN ĐANG ĐỌC
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Truyện Ngắnlabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.