Chapter 52

20 0 0
                                    

5⃣2⃣

A nan dai muka tatara muka koma ciki, kowa yana jan mu da hira ta yaushe gamo, a sace na kalle Mommy cikin biyyeya na tsuguna a gabanta nace" Mommy  ina wani? mun samu ku lafiya?..."

Shiru wajen ya ɗauka kowa yana kallon mu, TA ɗanne zuciyar ta tace" lafiya kalau ya hanƴa da iyayyenki?.."

Daɗi naji sosai yau ta amsa gaisuwa, aiko 'na saki fara'a kafin nace" suna gaida ki!.." bata sake kula ni ba hankalin ta yana wajen MAN, sai wani dudduba shi take kamar gyada!...

Ma'aikatan gidan ne suka fara shigo da kayan dana zo dashi, kowa mamaki yake yanda kayan suke da yawan gaske, ina jikin Mama na bayan mu gama cin abinci, tana shafa min kai na tace" Baby! wanna kayan duk na menene haka?.."

Mommy tana jin mu amma batace komai, nace" tsaraba ce Kawu na ya siyo min kowa na shi daban, motar da muka zo da ita kuma tawace ya siya min!.."

Mamaki ne ya kama Mommy batace komai ba illa tashi da tai a wajen, kai tsaye ɗakin ta wuce zuciyar ta cike da wasi-wasi a ina iyayena suka samu irin wannan kuɗ'in da sukayi wannan bajintar?.."

Sai da aka gama shigo da komai sannan MAN yazo nashi kad'ai ya dauke, ya gudu ganin yanda Daddah ke shirin bude mai...

A nan aka bar kayan har sai da Dady ya dawo bayan naje na gaida shi, yake ce min" MUNIBBAT ya maganar da mu kayi dake? shin kin amince zaki aure Aliyu ko kina da wanda kike so?.."

Ni wallahi tambayar tashi tazo min a bazata, cikin jin kunya nace" bana jin akwai abinda zaka umarceni dashi na bijire maka, kai ubane a gareni zan k'asance me biyayya a ko da yaushe, na amince da Mal kuma zan zauna dashi da zuciya ɗaya har ƙ'arshen numfashi na..."

" Masha Allah Allah yayi miki albarka, ki gaida min da Kawun naki in kuyi waya, ki masa godeya sosai!..."

A kunyace na bar wajen sa, shi kuma dadi yaji sosai ganin dai karamar yarinyar amma ina aiki da hankali, komai nawa cikin nutsuwa nake yin sa gaskiya Haidar yayi dacen mace ta gari Allah ya bashi ikon riƙe ta bisa a amana..."

Mommy ce zaune a gaban Daddah ance ta raba tsaraba, ta kalle Daddah ranta a haɗe amma haka ta d'aure tace" to ai abu a rabe yake Hajiya, ku kirawo yarinyar tazo ta  nuna shine kawai!.."

Dadi sosai Daddah taji yanda Mommy ta amshi zance bata hautsine musu ba, aiko aka kirani banji daunin kowa ba na miƙa mishi tashi tsarabar, hata ANNUWAR da nashi akwatin...

Duk wanda ya bude sai ya rik'e baki ganin irin uban kudin da aka kashe akan kayan...

Bayan kwana biyu biki na sake gabatowa inda aka fara shirye-shirye  babu kama hannun yaro, a yanzu Daddah bata bari na na fito ko falo kullum ina cikin ƙuriyar dakinta, da ko ishashen haske babu gyara suke mun na fitina, d'akin kaɗai ka shigo tashin k'amshi yake bare kuma kazo inda nake, na kara kyau jikina ya sake murjewa, ANTY NA ma tazo amma bata kwana ba kayan gyaran jiki ta kawo mun yan uban su, hata waya yanzu sun ƙwace sun hanin dauka a cewar su MAN bazaiji murya ta ba sai bayan aure...

Muna cikin halin damuwa sosai na rashin ganin juna da mukayi na kwana biyu, sautari wani lokaci ba kukan rabuwa dasu nake kuka rashin ganin sa nake, a na shi b'angare kuma Mommy ya saka a gaba da naci lallai sai ta saka an fito dani, wani lokaci ma haushi yake bata ko kula shi batayi...

Hafsat ta samu labarin auren ko irin kishin nan bata ji ba domin ita yanzu ba aure ne a gaban ta ba, a yanda take harsashe in ma aure zatai bazata auri d'an najeriya ba bare kuma wani MAN...

Nafisatu ce taje har gidan su Aysha ta taho min da ita, jameel yayi aure shima ita kuma an kawo kudin nata aure, ko zuwan ta ma sai Daddah ce ta gaya min amma baa barta tazo inda nake ba,  da farko nazo dabarar guduwa cikin dare, kamar yanda nake yau ma na kwanta kamar me barci Daddah tazo ta kwanta babu jimawa naji ta fara munshari duk da bashi da k'arfi amma alamar barci ne, na miki a hankali saɗaf saɗaf nake tafiya kamar wata barauniya bata ce min kala ba har sai da na kai bakin kofa sai ji nayi tace"  sannu Karishima Kapoor duk nacin ki baza ku haɗu yanzu ba dawo ki kwanta!.."

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now