_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣4⃣
" Hajiya! har yanzu su MAN basu shigo ba ne..?"
Shiru Daddah tayi na wani lokaci, to ganin Anty ta ɗaga hankalin ta yasa, tace" ɗazu muyi waya dashi, suna hanyar dawowa insha Allah.."
Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗi tace" aiyya ai ban sani ba, nima ina ta kiran shi bai ɗauka ba, gashi gabana yana ta faɗuwa Allah dai yasa lafiya.."
Sosai Dadda taji tausayin ta ya kama ta ganin ta damu da abunda ba nata ba, a zuciya tayi mata addu'a ita ma Allah ya ba nata, a zahiri kuma tace" umm kaji masu ƴaƴ yanzu ko ƙunya ta ma bakiji ba?.." ta faɗa cike da zolaya, da sauri Anty ta miƙe...
A gogon hannun sa ya duba cike da jimami, ya koma mota ya ɗauko wayar sa, zuciyar sa na halbawa number Anty ya fara kira amma shiru bata ɗauka ba, yana shirin sake kiran ta ne sai ga wani kiran ya shigo Daddah ce cikin faɗa tace" kai! ina ka tsaya min da yarinya ne?.."
Jiki a sanyaye yace" bata jin dadi ne muna asibiti.." da sauri ta mike zaune haɗe da sakin sallati, zuwa can tace" me ya same ta? ko kai ma ka ƙarasa tane?..."
A hankali cikin wani yanayi na tsananin tausayi yace" Kawun ta! ta gani yau Daddah! da Allah yasa sunyi ido biyu shikenan mu kuma mun rasata!.." jikin sa a sanyaye yake maganar..
A hankali Daddah ta sauke wayar zuciyar ta babu dadi, hango irin rikicin da za'ayi take duk ranar da MUNIBBAT ta dawo hayyacin ta, mutane biyu nan kawai take tausayi...
Ɗ'akin ya dawo ya saka ta a gaba, sai addu'a yake mata zuwa can ta fara motsa ƙ'afar ta ɗaga bisani kuma idanun ta suka bude, ta dauki lokaci me taho a haka kana ta ɗ'ago tana duban sa, tabbas daga irin duban da take mai yasa cewa ta shi ta kare, cikin halin masu jinya tace" ina jin ciwo sosai a nan!.." tayi maganar tana dafe kan ta..
Da sauri ya miƙ'e tsaye cikin jin dadi yace" zaki samu sauki insha Allah baby, jirani ina zuwa.." yana shirin fitane doctor ya shigo shi ma, tambayar yasa ya jikin ta, ya bashi amsa da cewa gata nan ai yanzu nan take faɗa min tana jin zafi akan ta sosai.."
Doctor ya saki murmushi cikin jin dadi yace" tabbas muna samun nasara, tunda yanzu ta fara sanin ina ne yake mata ciwo, shine me tafi so a rayuwa ta ta baya? yana da kyau ku haɗa ta dashi tabbas zata dawo normal.."
Murmushin ƙarfin hali kawai MAN yakeyi amma ya kasa cewa komai, har ya fice a ɗ'akin bai kula ba, a hankali na tashi duk da ba na jin wani dadin jikina yanda ya kama ta, gaba ɗaya bai kula dani sai gani na yayi a gaban sa, murya ta cike da shagwaɓ'a nace" Ya MAN!!.."
Da wani irin mugun sauri ya ɗ'ago yana duba na, gaban sa na tsanan ta faɗuwa, ido cikin ido nace" ka kai ni gida!.." har yanzu bai gama mamaki na ba, jin na kira shi da sunan da kowa yake kiran sa dashi...
Gaba nayi abu na, a hankali kuma abinda na gani ɗ'azu ya sake dawo min, dishi-dishi nake iya tuna komai na rayuwa ta, bana iyawa duk sai na ɗanne kunena da ƙ'arfi, a da dafe na kai mota, shiko yana baya na bai san halin da nake ciki ba, domin shima baya cikin hayacin sa...

YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.