_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣7⃣
Gaba ɗaya a halin gidan suna tsaye bakin ƙofa, ko wanne da kalar tashin hankalin dake kan fuskar sa, Hajiya Nusaiba ta dube MAN cikin alamun karaya tace" me yasa? ya zakayi mun haka? shikenan fa ɗaga yau zata barni!..." sharrr wasu zafaffan hawaye suka biyo kuncin ta...
Daddah tayi saurin dafa ta baya cikin taushin murya tace" bashi da laifi Nusaiba! nice 'na aika shi! amma bamuyi dashi zai tafi da ita ba..."
AN'NUWAR dake tsaye shima yayi jigum, yana tausayin a halin sa ganin sun shiga damu sabida baby! gaban su yaje ya tsaya cikin nutsuwa yace" kuyi haƙuri na san duk nine silar komai, amma ina da hanyar da baby zata cigaba da zama daku, zama na har abada amincewar ki nake nema Daddah, ya kamo hannun ta ya daura dacewa _a gaban ku zan nemi auren ta a wajen mahaifin ta! fatana ta tashi lafiya..."_
A mutuƙar razane kowa yake duban sa, MAN ya dafe bango da sauri yana fitar da wani nishi marar sauti, Kawu ya kura mai ido zuciyar sa cike da zilumi, ANTY dake sauraron komai take wani bakin ciki ya mamaye mata zuciya cike da tsiwa tace" uban wa ma zai baka auren ta ɗ'aga ganin ka haka sama ta kai! tun ba yau ba mun riga da muyi mata miji, sai dai ka nema a gaba..."
Gaba ɗaya kuma sai kallo ya koma kan ta, shi dai Kawu na bai ce komai ba...
A haka doctor ya fito ya same su kowa yayi jigum-jigum, cikin farin ciki ya mikawa MAN hannu haɗe da cewa" congratulations Aboki na, a yanzu komai ya dawo normal kamar yanda na sha gaya maka, sai mu jira tashin ta mu gani kuma, Allah ya kara lafiya ..." jikin MAN a sabule ya amsa da amin...
Dadi kamar ya kashe Kawu na, ai bai jira cewar kowa ba ya faɗ'a ɗakin zuciyar sa kamar zata faso ƙirjin sa saboda dadi, MAN ya rintse idanun sa shikenan ta kubuce mai a karo na farko...
Daddah ta dafo shi cikin muryar ta na manyan taka tace" bana so ka karaya Haidar, har yanzu muna da sauran lokaci..."
" No Daddah komai ya ƙare min yanzu! shikenan ta tafi kenan!..."Wani kallon tara saura ƙwata ANTY na tayi musu sannan ta biyo bayan Kawu na cikin ɗ'akin da nake, yana zaune jikin gadon da nake ƙwance sai aikin kallo na yake hannu shi cikin nawa, na jima sosai ina barci sabida allurar da akayi min, su MAN ko da wasa babu wanda yayi gigin shigowa ɗakin, suna ɗaga waje amma suna iya gano komai a haka...
Kawu na, ya fito jikin sa sanyayye yace" kuyi haƙ'uri zan so kuzo kuma..." yayi maganar yana nuna musu cikin d'akin kana ya daura da cewa" tana buƙatar ku ita ma..." a hankali ya kamo hannun MAN tunda shi ya fara sani, har gaban gadon ya kawo shi sannan ya juya wajen su Daddah cikin girmamawa yace" Hajiya ban san da wannan irin baki zanyi miki godiya ba na riƙe min marainiyar Allah da kikayi, kin tallafe ta a lokacin da take buƙ'atar taimako, ki mayar da ita mutun a lokacin da take shirin yanke tsammani, kin gatata ki ɗaga darajar ta, a lokacin da take zaton baza ta sake samun wani gata ba, na biyewa sharin zuciya dana shedan na aika babban ƙuskure, na kore ta ɗaga gidana a lokacin da take mutuƙar buƙatar taimako na, na ci amanar yar uwa ta da ta bani amanar ta, nine gatan ta Amma na manta wannan, nafi kowa sanin me zata iya aika tawa amma rashin bincike yasa na rufe idanuna na aika ta babban kusƙure, yanzu da ba dan Allah yasa ta faɗa hannu na gari ba, da ya rayuwar ta zata ƙasance? tun daga ranar da ta bar gabana ƙwanciyar hankalin tayi ƙaura a waje na, kullum burina shine na ganta, kullum zuciya tana begen ta, sai gashi ina zaune an kawo mini ita cikin mutunci har gida, wannan shine karamci kun ƙauna CE ta duk da baku san ko ita WACECE ba, kun nuna mata gata wanda bata taɓa samu a wajen mu ba, niko da me zan saka muku kuji dadi?..."
Cikin sauri Hajiya Nusaiba tace" bama buƙatar komai ɗ'aga gare ka face ka bar mana baby ta zauna wajen mu. ta zab'e a gaban sa muryar ta a rauna ne tace" ka dube girman Allah, kamar yanda Allah ya taimaka ya baka zuri'a lafiya, ilimi, kaji tausayin mu nida yara na ka bar mana baby nayi maka alƙ'awari zan kula maka ita har ƙ'arshe numfashin na!! tabbas na san abu ne me wuya ƙyautar da suƙutunda guda haka, musammma irin baby, na san irin soyayya dake tsakani ka ita na San irin shaƙ'uwar dake tsakanin ku, ba dan ni ba badan halina ba da soyayyar da fiyyen halitta, karka rabani da ita..."" cikin hawaye yanzu take maganar...
Cikin sauri MAN ya ɗago ta ransa a bace yace" me kikeyi haka ne ANTY!!? kina tunanin zai iya baki kyautar MUNIBBAT cikin sauki haka? Daddah ki faɗa mata ta cire ta a ranta, ba gamu ba? mu bamu isheki ba ne ANTY? muma muna ƙaunar ki ko duk wannan bai miki ba? ki ɗaina in da rabon MUNIBBAT ta sake zama tare da ke zata dawo SON...!" a hankali ta rungume MAN cikin kuka tace" zanyi ƙewar ta sosai MAN! Ina jin ta tamkar yar ciki na!!.."
Shima hannun sa ya saka yana share ƙwallar idanun sa cikin juriya yace" nima ina ƙaunar ta ANTY amma ba yanda za muyi, yanzu zata ga abun da mu kayi mata tamkar a mafarki ne, gaba ɗaya mu zamuyi ƙewar ta ne!..." ji yake kamar ya kurma ihu amma sabida ANTY ta ɗai na kuka sai ya daure!!...
Daddah ta kamo hannun AN'NUWAR har gaban Kawu, cikin taushi tace" ka gafarce mu aka abinda jikana yayi muku na bige muku yarinyar cikin gaganci?.." ta faɗa tana haɗ'e hannuwan ta waje guda...
AN'NUWAR yace" kayi haƙuri tsutsayi na da ƙaddara amma nima ba haka na so ba, ka gafarce ni!!.." ya faɗa cikin ladabi..."
Gaba ɗ'aya ji yayi kan shi yayi mai girma, ganin manya mutane suna neman yafiyar sa akan MUNIBBAT ga tsananin soyayyar ta da yake hango wa a cikin tsakiyar idanun su, cikin tausayawa ya ɗago AN'NUWAR fuskar sa a sake yace" Allah ya yafe mana baki ɗaya, ni ya kama ta nayi godiya ba ku ba, na gode sosai Allah ya bar zumunci..."
A hankali suka amsa da ameen...
To abunda basu kula dashi ba, shine tun farkon shigowar su na farka, duk wannan koke-koken da suke akan idanuna su kayi sa, naji komai da ya faru dani kallo ɗaya nayi ma AN'NUWAR da Hajiya na tuno inda na san su, malan Haidar kuma bai juyo ba bare na sheda shi, amma naji murya sa inta kokon to...
Cikin sanyin jiki Daddah ta saka su a gaba akan su tafi gida, har sun kai ƙofa jiki na na rawa nace" Hajiya!!!..."
Gaba ɗayan su juyo wa sukayi kamar ance su rugo inda nake, musamma hajiya nusaiba cikin soyayya ta sunbaci goshi na idanun ta cike da hawaye tana wani shafa min fuska, tace" BABY NA!!! kin gane ni? Nice nice!!.." kuka kan da take ya hana abunda take son faɗa fitowa
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce☺
أنت تقرأ
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
القصة القصيرةlabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.