Chapter 2

80 8 0
                                    

_WAYE ZABIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*
        
      

*A gaskiya nayi mamaki na kuma ji dadi ganin yanda kuka nuna min k'auna akan wannan book din, naga ruwan comments har inda banyi tsammani ba, na gode k'ware da gaske, Allah yasa ku d'ure a haka..*

🅿 2⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR   RAHIM

Washe gari da sasafe, sai ga Aysha ta shigo gidan mu fuskar ta cike murmushi, lokaci ina d'urk'ushe a gidin murho ina fama da itace yak'i kamawa, cikin murna na taso hannun ta na kama na jata zuwa bakin zauren gida mu, murya ta k'asa-k'asa nace" lafiya Aysha na ganki a irin wannan lokacin?.." na fad'a ina waigawa baya na tamkar b'arauniya..

Har yanzu murmushin ta bai gushe a kan fuskar ta ba, tace" matsoraciya kawai, zuwa nayi nayi miki albushir Monday in Allah ya kai mu tare zamu koma makaran ta, yanzu nan Mama ta gama gaya min yanda sukayi da Baban mu, yace zaizo ya same Abban ki in anjima.."

Dam gaba na yayi wata irin mumunar fad'uwar, cikin sark'ewar murya nace" me kike ce Aysha? ni dai dan Allah kije kiyi ma Mama bayani muddin Abba ya samu labarin nan wallahi k'ashi na ya bushe a wajen Anty, domin ko bata kasheni ba  zan sha bak'ar azaba, ni dai kawai a maidani makaranta ta ba lallai sai an gaya mai ba, tunda nima ya biya min ita ta hana kud'in har aka gaji aka k'oroni, kin fa san komai Aysha dan Allah kije kiyi musu bayani bana so na sake shiga matsala a yanzu, Abba ko sati bazai k'ara a cikin garin nan ba zai wuce zata iya komai inta ga babu idon sa..." na kai k'arshen zance hawaye na bin k'uncina...

Aysha ta b'ata fuska tana turo baki gaba kamar yanda muka saba tace" kin gani ko? ni matsala ta dake kenan d'an k'aramin abu sai ki kama mai kuka, kwantar da hankalin ki haka ma baza ta faru, na san Baba sare zanyi mai bayani da kai na kuma zai fuskace ni, amma dole Mama zata zo tayi ma Anty wayo kin ji.." ta fad'a tana share min k'wallar...

A haka muka rabu da ita zuciyoyin mu cike da murna, b'angare d'aya kuma cike da tsoron Anty, wajen aiki na na koma cikin sa'a kuma sai naga wutar ta kama,  d'akin mu na wuce na fara tashin yaran d'aga barci mu hud'u ne d'aya ne na miji a cikin mu, kuma yaro ne sosai dan ko  shekara biyar bai gama rufawa ba, cikin sa'a na fara da Bishira kayan ta na tub'e mata duk tana ta magagin barci a haka na fito da ita tsakar gidan lokacin ruwan yayi zafi, wanka nayi mata cikin sauri sabida sanyi da ake, ina gamawa da ita sai ga fiddusi ta fito, tana ta turo baki kamar dole a kai na ta tsaya cikin rashin d'a'a tace" malama ni kiyi sauri sanyi nake ji.."

Niko bani da lokacin magana a yanzu dan haka, kamar yanda tace sama-sama nayi mata wanka ta wuce ita abin ta, a haka sai da na wanke su tas sannan nima na d'auki nawa ruwa na shige bayi, bayan na fito na koma ciki, a zaune na same su babu wanda ya shafa mai a cikin su, baya babu wace bazata iya shirya kan ta ba, har ta taimaki dan uwanta, cikin jin haushin su nace" Bishira ke dai kinji kuny'a wallahi yanzu ki shafa man ne bazaki iya ba  har sai kun jira ni nazo wato ga baiwar ku ko?..." na fad'a ina cigaba da aika masu harara, babu wace ta tanka min a cikin su dan sun san bugu zasu sha...

**************

" Yaya wallahi da gaske nake abinda na fad'a maka, d'azu da sasafe naje gidan kuma nayi  sa'a ita kad'ai na samu a waje, shine take fad'a min yanzu taimakon ka nake nema ta yanda Baba zan fahimce ni.." ta fad'a cikin marairaice wa...

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now