page 17

63 4 0
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*


BISMILLAHI RAHMANI RAHIM

🅿 1⃣7⃣

Cikin mutu'kar farin ciki ta dawo ta zauna, tana duban sa da walwa akan fuskar ta tace" Alhamdulillahi, shi yasa nake ji da kai yaro na, yanzu ya ake ciki ?..."

Take an'nuri fuskar shi ya sauya zuwa damuwa, ya ciza lip's din shi na kasa kana yace" marainya ce!! bata da kowa a duniya da ya rage mata sai mutun d'aya,  Daddah kiyi duba da halin da take ciki a yanzu na rashin hankali, hakan bai sa ta manta sunan shi ba, sabida tsananin soyayyar da take mai yasa take kira na da Kawu!,  a yanda na samu labarin ta shi kad'ai ne gatan ta, shine uwa a wajen ta shine uba, marik'iyar ta kuwa ta gallaza mata iya kar iyawar ta,  a takaice dai Daddah shi da kan shi ya kore ta a gidan sa ta dalilin matar sa, amma a yanda aka ce min yanzu yana neman ta ido rufe, ko wajen aikin sa yaki komawa kullum yawon neman ta yake.

Daddah ko  Auta ta dawo gidan nan bana so ta san wannan sirin namu ko kad'an ka da a nuna mata Aysha ko a bari ta ganta, in baki manta ba na gaya miki kawaye ne su, dazarar ta ganta zata shedata kuma na san Auta bakin ta baya shiru tass zata kwashe ta gayawa Ayshan asali kin ga kenan yarinyar zata sake komawa ainahin rayuwar ta ta baya, ina so ta samu sauyi ko yaya ne Daddah!!.."

Har yanzu murmushi take cike da karfafa mai gwiwa tace" insha Allah Big man, MUNIIBAT baza ta sake komawa ainahin rayuwar ta ba, zata ci gaba da zama damu ko dako ace ta dawo hankalin ta, zan rik'e ta tamkar yar ciki na, kai ma kayi min alk'awari bazaka cutar  da marainiyar Allah ba?.."

" Nayi Alk'awari in Allah ya yarda banzan tab'a cutar da ita ba, zan Bata farin ciki iya kar iyawa ta, Alk'awari nayi ma kai na duk abinda take so shi zan mata ko da ko ni zan rasa nawa farin ciki, ina jin ta sosai a raina Daddah ban san me yasa haka take faruwa dani ba komai nata birge ni yake duk da tana cikin wani hali.."

Cike da jin dadi kalaman sa ta d'ago ta dube shi kana tace" Allah ya baka ikon aikatawa a aikace, Amma kar manta kabi k'aidar yanda kayi tun farko kar a samu matsala, kayi wa mahaifiyar ka biyayya kaji.."

" Insha Allah.."

D'aga haka suka koma wata hira can daban...

" Hello my mom..."

Cikin jin dadi ta gyara zaman ta game da cewa"   My Son, ina fatan kana cikin koshin lafiya?.."

Kamar yanda yake yana nan bai sauya ba, cikin murya sa me kama da ta jin baci yace " I missing u , ni gaskiya zan dawo gida a cikin satin nan, gaba d'aya bana jin dadin zama na a k'asar nan, gashi har yanzu na kasa mantawa da..."

" Shiiittt!!! bana so bana k'auna ko da wasa ka sake tuna min da wannan abun, wai me yasa yanzu baka jin magana ta ne AN'NUWAR!? nace ka manta da ita³ ha'a! ya kuke so nayi ne? shi want can ya koma wajen su ya tare, kai da kake nisa ka d'auki damuwar wasu banzaye ka azama rayuwar ka, to ka kiyayye ni AN'NUWAR tun kan mu had'u!!..." a masifance tayi maganar, amma fa ta nan yanda take tun farko...

" Mommy ba fa haka nake nufi ba, ki fahimce ni please, ina so na fad'a miki abinda ke damu na ne.." yayi maganar cike da damuwa...

A sanyaye tace" Ok ina jin ka?.."

" tun daga ranar dana zo k'asar nan kawo in yanzu kullum sai nayi mafarki wata yarinya, tana kuka tana mik'o min hannu akan na taimake ta, gashi ni bana iya motsi  ba iya ganin fuskar ta amma kukan ta yana ratsa min kai da jijiyo, sai nake gani kamar a gaske ne domin ko na farka ina jimawa da abin kafin ya barni, ina so na dawo kusa dake mommy!!.." ya k'arke maganar cikin narkewar murya kamar zai fasa kuka...

Shiru Mommy tayi jiki a sanyaye, cikin jimami tace" ba damuwa duk sanda ka shirya zaka iya taho wa, amma ka d'age da addu'a nima zan taya ka..." ai bata bari ya amsa ba ta kashe wayar...

Ina ƙwance sai k'unk'uni nake ni kad'ai, gaba d'aya haushin wanda yayi min tsawa d'azu ya cika min raina,  Anti ta shigo d'akin yafi sau biyar tana min magana akan na tashi nak'i, gajiya tayi ta rabu dani ta kama sabgar gaban ta...

Haka kawai na fashe da wani irin kuka me ƙ'arfin gaske, duk wani mahaluki dake cikin gidan nan sai da yaji kururuwa ta, Anti dake bayi a gigice ta hau saka kayan ta ko kumfar jikin ta bata dauraye  ba, Daddah da Big man suma da gudu suka taho shashin ANTY dan duba lafiya ta, Mommy dake tunanin da ta  tsoro ya kama ta, cikin sauri ta shige ɗaki haɗi da mmitar anje an ɗauko musu jaraba an kawo musu..

Kusan a tare suka shigo ɗakin, ina zaune akan  bed din hannuwa na bisa ka na, na wage murya iya ƙarfi na ina kumbuɗa ihu, cikin mutuƙar tausayi na Haidar  yazo kusa dani cikin taushin murya yace" Baby na!! menene? me akayi miki?.."

Ko sauraron sa banyi ba na ci gaba da kuka na, babu wanda baiyi magana a cikin su akan nayi shiru ba, ko na faɗi abinda nake so amma shiru wallahi na kasa magana, sai kuka nake cikin damuwa da tashin hankali, Daddah tace" wai  ba yau ne ranar komawar ku gani doctor ba?.." 

Cikin ladabi Hajiya Nusaiba tace" Eh hajiyar mu, Kiran da nayi ma Big kenan kuma taki yarda mu tafi shine na bari zuwa gobe maje.."

"Au dama sai ta yarda sannan zaku tafi? ki wuce kije ki wanke wannan kumfar ta jikin ki kuzo maza muje..."

Da sauri Nusaiba ta wuce, inda Haidar ya cigaba da rarashi na, amma kiri-kiri naki nayi shiru,  a hankali ya kamo hannu na cikin tautausan lafazi yace" Sanyi idaniya ta!!!.."

Diff kuka na ya ɗauke, sai hawaye kawai da yake zubo min, na kure shi da idanu ko kifftawa banayi, ya sakar min ƙaisaitacen murmushi kanaya ɗaura da cewa" kina so Kawun ki yayi fushi dake? bana san wannan rigimar, kina ji bana na so na ringa ganinki cikin damuwa, kina so nima nayi kuka ne?.." ya faɗa yana sauya fuskar sa zuwa damuwa...

A hankali nayi murmshi har yanzu hawaye nake kuma ban dai na kallon shi ba, so nake na tuna wani abu amma na gaza iya tuna komai,  kawai sai na mayar dashi TV...

Cikin yanayi farin ciki na samun nasara yace" yanzu me kike so?.."

A hankali na ware ɗaya hannu nawa, ina nuna mai cikin shirme na nuna shi da manuniya ta, yace" ni kike so?.." da kai na amsa mai dan ban san me yake nufi ba, nace eh...

Daddah tayi dariya cikin jin dadi tace" to ka sako mata hijabin ta muje, kafin ta cigaba..." tana gama faɗar gaka ta wuce..

Shirme na ta zuba mai, yana biye min  har sai da Anty tazo tace mu fito sannan ya kamo ni, mu kayo waje...

tana tsaye a wajen kamar jiran fitowar mu take, cike da jin haushi ganin yanda na cukukuye mata ɗa yasa tace" kai!!! ina kuma zaka je da yamma nan?.."

Cikin biyayya ya janye ni ɗaga jikin sa, zai isa gare ta nayi sauri ƙanƙame shi ina noke kafaɗa alamar bazan sake shi ba, Babu wanda bai ga abinda ya faru ba, gudun kada nayi kuka yasa shi jana a haka har zuwa gaban ta, cikin taushin murya yace" Mommy bata jin dadi ne shine zamu kai ta asibiti, Kum...

" Ke!!!.. ta daga min tsawa, cikin masifa da zazare idanuwa tace" sake shi dan ubanki!!.."

Na tsorata fiyya na dana farko, cikin sauri na shige bayan sa ina kara ƙanƙame shi, a hankali na leƙo idanuna ta tsakan-kanin hammatar sa ina hararar ta...

Ta haɗi rai sosai a hasale tayo kai na!!..

Kuyi haƙuri 'na fara gyarawa naji ban iyawa

Comments

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now