_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)**BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
🅿 2⃣8⃣
A hankali Dadda ta ɗago ta zuwa jikin ta, cikin nutsuwa tace" shitt!! ya isa haka!!.."
Ƙare musu kallo nayi tass, sannan 'na kalle Kawu na, haɗi da sakar mai tausasan murmushi, a hankali nace" ina san ka sanyin idaniyata!.."
Shi ma martanin murmushi ya mayar min, daga bisa ni yace" Hajiya 'in babu damuwa ina son magana dake?.."
" BISMILLAH!.." cewar Daddah.. Waje suka fita ni kuma aka barni da jama'a ta har yanzu MAN bai waigo ba, tunda na kalle ANNUWAR sau ɗaya ban sake gigin kallon sa ba, hankali na gaba d'aya yana wajen Hajiya Nusaiba, da take ta ƙoƙari ganin na tuna su...
(Kun dai san manta komai nata tayi, ba wai haukacewa tayi ba, duk abinda kayi mata zata iya rikewa, haka zata iya tunawa ko da memory dinta ya samu lafiya, musamma ita tunda tana da kayefin tunanin, zata na ganine tamkar a mafarki tayi wata rayuwar daban...)
Cikin gajiyawa nace" Kiyi haƙuri Hajiya, nima yau na fara ganin ku!.."
Maganar ce ta daki zuciyar ANTY cikin sauri tayi baya, MAN yayi saurin tare ta, haushi ya kama ANNUWAR...
" HAJIYA zan so na bar muku ita a hannun ku, ni kai na sai zuciyata sai tafi nutsuwa da hakan, amma ina jin tsoro sosai da yanayi da take ciki, ki ƙwantar musu da hankali insha Allah nan ba da jimawa ba zan dawo muku da ita, zanyi ƙoƙari sosai na ganin bata manta da ku ba, kuyi haƙ'uri dan Allah ku bar min ita nima na samu nutsuwa, zata dawo muku cikin sauki..."
Kallo mutuntawa Hajiya Daddah tayi masa cikin jin dadi da tausayi sa tace" haƙiƙa naji dadi furicin ka sosai, Allah ya saka da alhairi, amma abinda nake so da kai shine, karka taƙura kan ka abinda bakayi niyya ba, na san yanda kake ƙaunar ƴarka, ita ma tana ƙ'aunar mahaifin ta, muna san muga MUNIBBAT a cikin farin ciki, me ɗaurewa kullum ƙwanan duniya addu'ar da muke mata kenan, Allah ya amsa kuma mun gode masa, duk cikin mu babu wanda zai so ya raba ta da abinda take so, a yanzu babu wanda tafi ƙaunar gani da san zama dashi sama da kai! kana tunanin zamu so wannan farin cikin nata ya rushe? a'a baza mu zama masu san kan mu ba gaskiya, zan so ka bar ta a wajen ka duk lokacin da ta bukaci ganin mu, insha Allah zata gan mu, kamar yanda muke kula da ita a wajen mu, baza mu canza ba insha Allah mun gode sosai Allah ya bar zumuci, ka ci gaba da riƙe amana tabbas zakaga ribar hakan, Allah ya tsare gaba mun gode..."
Jikin sa yayi mutukar yin sanyi, ko magana ma ya gagara...
Har yanzu ban ga fuskar mal Haidar ba, a haka ya fice da Anty tana kallo na hawaye na bin kuncin ta, ANNUWAR na bin bayan su, a waje suka tarar da Daddah daga nan su kayi sallama da Kawu suka fice a asibitin gaba ɗaya...
Gaskiya na yarda ni ƴar gata ce a wajen Kawu na, duk inda na motsa sai ya tambaye lafiya ta, abun gwanin ban sha'awa zuwa dare aka sallame mu muka dawo gida, babu wanda baiyi mamaki ba gani a gyara gidan fas dashi, musamma ɗaki na a zuba mun wasa manya kayan ɗaki masu bala'in kyau da tsari, tamkar ba gidan mu ba, gaskiya ana ƙawata abun sosai, dadi ya kamani sai tsalle nake ina murna, cikin jin dadi nace" Kawu duk wannan nawa ne ni kaɗ'ai?.."
Shima murmushi ƙarfin hali yayi min haɗi da cewa" eh mana yar gidan Kawu, duk dan kiyi farin ciki ne ai..."
Ko da na bude cikin siff din kaya ne masu yawan gaske da tsada, komai ana zuba min a ciki ina can ina shirme na na jin dadi, Kawu na ya ɗauki wata farar takarda da aka ɗ'anne ta da ƙwalin wata danƙ'areriyar waya, bai bari na gani ba yayi saurin ficewa a ɗ'akin...
ŞİMDİ OKUDUĞUN
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Kısa Hikayelabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.