_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 1⃣1⃣
Gaba na ne yayi wata irin faɗuwa cikin kaɗuwa nace" Anty zan wuce?.."
Sheƙeƙe ta dube ni, cikin isa tace" yau a'i ba ranar makaranta bace, ki wuce kije abinda kika saba hutun ya isa haka.."
Cikin rashin fahimta nace" Anty me kenan? ai babu wani hutu da nayi.."
Cikin sanyi nayi maganar.." ehh lallai, abunda kika saba shi zakiyi, yau bazaki je makaranta ba maza shige ki cire kayan nan..." ta ƙarke maganar da turani ɗaki da ƙarfi, har sai da na faɗi cikin hawaye na ƙwaɓe kayan zuciya na tafasa, a haka har na kamala domin 'in ban manta ba alƙawari nayi mata lokacin da nake jin yunwa, zan cika ka mata shi daga rana irin ta yau ko zata ƙasheni bazan sake zuwa ba...
Jikina a sanya ye na fito bance mata ƙazaba na fice a gidan sai aiko min da harara take, wallahi sai na rasa inda zan nufa, tanuni na ya tsaya cak yanzu ta ina zan fara ne?...
*****
" Asalama alaikum Hajiya barka da hutawa.." cewar Hajiya Nusaiba wace ta kai sati yanzu da dawo cikin gidan...
Cikin farin ciki Hajiya Daddah ta musƙuta tace" yauwa ƴar nan, kin fito ? ya jikin naki?.."
Cike da jin ƙunya tace" da sauki Hajiya, na ma fasa zuwa asibiti ace ma AN'NUWAR ya barshi kawai na gode..."
" Haba dai wannan irin ya barshi a zaune kalau? ko haushi kika ji dan ya nuna bai ƙaunar kaiki? to kwantar da hankalin ki muddin ina cikin gidan nan babu me takaki ya zauna lafiya bari yazo dole zaki je, sabida shi ai bazaki fasa fita ba..." ta faɗa cikin masifa..
To gani hajiya ta mayar da abun babba, sai Nusaiba ta sake risinawa cikin girmamawa tace" ba haka bane hajiya, wallahi babu abinda naji a gani na shi ƙaramin yaro ne har yanzu bai gama hada hankalin sa ba, ni kuma naji sauki ne yanzu babu abinda ke damu na, shi yasa nace na fasa amma ba da wata manufa na faɗi haka ba..."
" To naji amma fa zuwa ne sai kinyi ko kinji sauki ne kuwa sai kinje..." ta faɗa cikin isa da izza..
" Muddin zakiyi farin ciki da hakan zanje Hajiyar mu..." ta faɗa cikin farin ciki dan yanda Hajiya take nuna mata ƙ'auna abin yana mata dadi...
" Sosai zanji dadi, abinda nake so dake yanzu shine, in kinje gani doctor ki zage kiyi mai bayani komai ko da wasa karki boye abinda ke damunki, insha Allah za'a dace kema da yarda Allah nan gaba kaɗai haka zaki shigo min da yan yaranki dagwai-dagwai suna min ƙiriniya..." ta faɗa har cikin zuciyar ta tana jin dadi da san kasancewar wannan ranar...
Nusaiba ta sunna kai ƙasa cikin jin nauyin ta fuskarta ƙunshe da murmushi, nan suka suka shiga hirar duniya...
" Mommy ni gaskiya ba zanje ba, fisabililahi duk cikar gidan nan a rasa me kaita asibitin sai ni ɗaya, to gaskiya ina da abunyi yanzu haka..."
" AN'NUWAR inda na isa da kai kaje ka kaita, wai meyasa baka da aiki ne sai na jawo mun magana? so kake kullum aita gani laifina ko? tsaya ma ka manta ita baƙuwace ba ko ina ta sani ba? ko so kake hajiya ta zageni tsaf a gaban ta?.." cikin muryar nan tata tayi maganar kamar bata so a haka wai faɗa take, gashi tana zaune ko gezau bata motsa ba...
VOUS LISEZ
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Nouvelleslabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.