Chapter 5

58 6 0
                                    

_WAYE ZAƁIN  MUNIBAAT_?
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM

🅿 5⃣

Alhaji Abdulazizi nera, shine inkiyar sa kaf garin kano babu wanda bai san da shi ba, mutum ne mai kuɗin gaske, ya kasance mutumin kirki da son jama'a kekkyawa dattijon asali, domin shi kuɗin sa basu rufe masa ido ba,  kowa na shine baya kyamar talaka ko kaɗan,  shi ɗan asalin garin  kano ne a wani ƙauye da ake kira  rangaza, a nan kakaninsa suke da zama, yana da mata biyu.

Babbar matarsa ita ce Hajiya Ameena, tana da yara huɗu maza uku mace ɗaya, Hajiya Ameena macece me tsanani da nuna isa da iko, a duniyar ta ta tsani talaka ya raɓe ta ko ƴaƴanta, shi yasa duk wanda take hulɗa dashi to fa sai ya taka matsayi me girma a cikin masu kud'in ma, ita yar asalin rangaza ce, zamu iya cewa auren zumuci ne tsakanin ta da  mijinta, suna da rufin asirin su daidai gwargwado, ta auri Alhaji tun bai dashi har Allah ya hore mai ya zama  wani a duniya.

Alhaji ko kaɗan baya ƙaunar wannan halin Ameena na tsanar talaka da take yi, sau tari ya sha zaunar da ita yayi mata nasiha, amma da ya bar wajen shikenan ta manta da abin da ya ce mata, kaf cikin yaranta babu wanda ya ɗauki muguwar ɗabi'arta, sai dai ɗanta na biyu mai suna AN'NUWAR ya bi sahun nata yaƙi jinin talaka sosai a rayuwarsa, shi har yaso ya fi  Hajiayar tasu ma, bashi da abokai talakawa abokansa duk ƴaƴan masu ƙuɗi ne, gashi mayen mata, amma duk ƙaunar sa ga mace in ba ƴar masu ƙuɗi bace to shi kallon namiji yake mata, bai taɓa aikata Zina ba, domin a kullum Mommy tana mai huɗuban hatsari zina ga rayuwar ɗan adam sosai, ya yi karatun addini da boko sosai inda ya karanci fannin kimiya da fasaha wato computer science, tun kammala karatunsa yaƙi aikin gwamnati acewar sa tunda Daddy ya tara musu dukiya ba sai ya nema aiki ba.

Babban ɗan Alhaji shine Aliyu haidar, sunan babban yayan Alhaji ne wanda Allah yayi masa rasuwa kafin haihuwarsa, bayan yasamu ɗansa na farko sai ya mayar da sunan  kan Haidar wanda suke kira da BIG man, gaba d'aya Aliyu halin shi irin na mahaifinsa ne, babu inda ya baro shi, kyakykyawa ne na bugawa a jarida, duk abin da ake nema a wajen namiji Haidar  ya haɗa shi, ƴan mata kam da kan su suke kawo kan su gare shi, shi wani irin mutum ne  wanda mata sam basa gaban shi, bashi da burin da ya wuce yayi karatu me tsayi, Alhamdulillahi burin sa ya ciki ya samu duk wani matsayi da kuka sani na fanni ilimi yayi isilamiya yayi boko,tashin farko baiyi shawara da kowa ya nemi aikin  koyarwa, shima ba a ko ina ba sai a government school, lokacin da hajiyarsa taji labari ba ƙaramin hauka tayi masa a kan bai isa ba, dole ne ya ajiye wannan aikin shima ya zauna kamar yanda d'an uwan sa yayi, magana tayi girma in da har sai da aka je gaban Hajiya Nafeesa uwa ga Alhaji kenan, a nan ne ita ma ta nuna ikon ta akan jikan nata da ɗanta, dole Mommy taja bakin ta d'inke, domin Hajiya ta fita bala'i, dalilin haka ne ya sa Hajiya dawowa gidan da zama, a cewar ta Amina zata lalata mata jikoki, Daddy kuma ya goya mata baya...

Abu na farko da Hajiya ta fara a gidan shi ne, gaba d'aya gidan zasu hallara a babban falon ta, cikin Isa da  ƙasaitacciyar hajiya tayi gyaran murya ta ce "to Alhamdulillahi naji daɗi sosai yan da naga kun samu nutsuwa daga zuwa na, abin da nake so da kai Abdulazizi ranar Monday in Allah ya kai mu da rai da lafiya, ina son takorata a mayar da ita government skul, shi kuma Bashir dake ƙasar waje ina so ya dawo gida najeriya ya ci gaba da karatun na sa a nan, ina fatan ka fahimceni ni?.." ta fad'a tana mai wani irin kallo na ka kiyaye ni...

Cikin biyayya ya ce " insha Allah Hajiya yan da  kika ce haka za'ayi, muddin hakan zai saki farin ciki.." ya fad'a cikin girmamawa...

Hajiya ta saki murmushin k'asaita tana aikawa da Mommy banzan kallo, murya can k'asan mak'oshi tace" Amina ko kina da abin cewa?."

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now