_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 5⃣0⃣
Abinda na fahimta yanzu ANTY bata cika zama muyi hira tare da ita ba, ko da yaushe tana d'akin ta, maganar komawar ta gidan Kawu na, ban gaya mata yanda mukayi dashi ba amma maman ta ta san komai itace ta hanani gaya mata, shirye-shirye muke tayi a tsakanin mu tamkar za'ayi bikin wata budurwa, kullum mune yawan cin kasuwa...
B'angare MAN kuwa ya shiga damuwa sosai rashi na a tare dasu, haka ma Mama na kullum sune kirana a waya sai mu bata lokaci muna abu d'aya dasu, abun mamaki wai har Dady cewa yake na dawo gida sunyi kewa ta, in muna waya dasu na kan shiga nishadi sosai babu wanda bana tambayar lafiyar sa a cikin a halin su, wannan karamamci nawa yake sake d'aga darajata a idanun kowa na gidan su MAN, kamar yanda muka saba yau ma waya muke dasu da yake a amsakowa suke sakani kowa yaji abinda zan fad'i, Mommy na zaune cikin izzar ta da isar ta gaba d'aya haushin su take ji ganin yanda suka wani zagaye waya guda kamar wata jinin su...
Bayan mun gaisa da kowa nayi kasa da murya cikin yanayin tausayi nace" please my family ku gaida mun da Mommy sosai dan Allah, ina me sake bata hak'uri a karo na babu adadi, tabbas ni me lefice a gareta na amince da wannan amma dan Allah ta amsheni a matsayin ya ko da na rana d'aya ne a rayuwa ta, ina buk'atar kulawar ta itama Ina so naga tana min murmushi tamkar yanda take ma Auta! dan Allah ku tayani bata hak'uri!..."
Shiru! wajen ya dauka sai numfashin su dake tashi a hankali, ko wa kallon Mommy yake ganin me za tace a hankali ta mike tamkar zata aikata wani abu, har inda suke tazo wayar ta dauka tana kallon kowa daya d'aya kana ta kashe wayar gaba d'aya cikin bacin rai tace" har abada bazata zamo wani shashi na cikin zuri'ata ba, ko muryar ta bana son jin bare kallon fuskar ta, amma da yake doluwace murmushi na take buk'ata, aikin banza!!!.." ta saki wayar a k'asa tayi gaba abinta...
Babu wanda ya tanka mata har ta fice a falon, takaici yasa Dady lumshe idanun sa...
Nikam jin an kashe wayar ban kawo komai a raina ba, na mike duk da zuciya bata min dadi tunanin d'aya ya za'ayi yanzu Mommy ta soni ita kadaice ta rage min a yanzu!..
Washe gari MAN ya matsa min da waya dole ta sa nayi masa kwatancen inda nake yazo, abun mamaki shima har da kayan sa wai sai ranar da zan koma shima zai tafi, ANTY ta amshe shi hannu bibiyu tunda zuwa yanzu ta san matsayin da yake dashi a wajena...
Muna shirin komawar ANTY ga soyayya muna zuwa ba tamkar bazaa mutu ba, gaskiya MAN dan soyayya ne na k'arshe, nima baa barni a baya ba wajan nuna mai k'auna soyayya ce me tsafata da daraja juna...
Cikin sati biyu akayi komai aka gama, matan Kawu sunyi mutu'kar mamaki ganin dawowar ANTY ko wace ta shiga taitayin ta, Kawu na ya dawo tamkar wani basarake ko wace na nuna mai iyakar k'aunar sun shagwab'a min Kawu na sosai, duk da haka yana bamu lokaci nida MAN dinna da muka zama tamkar tagwayen juna, yanzu har kaya iri d'aya muke sakawa abun gwanin ban sha'awa...
Duk wani iskaci da shashanci sai da ANTY RABI ta sauke shi, shima ta sanadiya ta domin sai da na matsa mata iya matsawa, ya zamana itace take shakar fitowa bamu ba, Kawu na ya goya min baya dari bisa dari...
Zaune nake a gaba ANTY kamar yanda ta buk'ata cikin biyayya nace" ANTY gani!.."
Kallo tai idanun ta cike da k'walla tace" ban san ta yanda zaki amshi magana ta ba Muni tabbas na zalinceki, na cutar dake sosai amma a yanzu zuciya ta cike take tsantsar ladama danasani, akwai wata alfarma danake nema guda d'aya a wajenki duk na san abune me mutu'kar wahala na sameta..."
Ta zame kasa bisa gwiwoyin ta cikin zubar da hawaya tace" sautari Kawunki yana min hangan wannan ranar, amma tushewar basira yasa na kasa fahimtar abinda yake nufi, DAN ALLAH DAN ANNABIN RAHAM, IN KINAYI WA IYAYENKI DAN GIRMAN ZATTI MUNIBBAT KI YAFE MIN DAN GIRMAN ALLAH!?..." cikin kuka sosai take maganar..
Mamaki da alajab'i ya hanani magana ba abinda nake face zazare ido Ina kallon ikon Allah, kukan da take har cikin raina nake jin sa, nima wata k'walla me zafi tazo bu min koba komai ANTY ta ri'keni kuma tayi min gata ta wani bangaren, a yanzu bana ganin lefin ta sam...
Gani har yanzu bance komai ba yasa ANTY mikewa tsaye cikin kuka tace" ni dama na sani abune me wuya kiyi yafe min abinda na aikata miki, amma ki sani zuciya ta bazata taba samun salama ba har sai ranar da kikace kin yafe mata, bazan sake farin ciki ba har sai ranar da kika shirya amsa ta a matsayin uwa MUNI, kiyi hak'uri na saki tuno abinda ya wuce!.."
Tana rufe bakin ta tai waje da sauri, ni gaba daya tausayin ta ne ya hanani magana ba wai wani abu ba, ina ji ina gani har ta fice ban iya tsayar da ita ba...
Bishira ta karasa shigowa d'akin itama tana kuka tace" ANTY MUNI tabbas mamana ta aikata miki babban lefi wanda zaiyi wuya ki iya mantawa dashi cikin sauki, tun kan nayi wayo na fahimci wacece ke a cikin gidan mu, amma hakan bai sa na rainaki ba nima ina me rokar wa mahaifiyar mu alfharma d'aya Dan Allah kiyi hak'uri ki yafe mata ko muma ma samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan nan, hakin kine yake shafar mu ANTY dan Allah ki yafe mata ba dan halin mu?...
Nima cikin muryar kuka nace" me yasa kuke rokona ne? ban tab'a ganin abinda ANTY take min ba a matsayin mugun abu, har kullum ina gani tamkar gyara take min a rayuwa ta, ta sanadin ta na samu mahafiya ta, niko me zance mata da ya wuce Allah ya biya ta, ban tab'a rike ANTY a zuciya ta ba dai-dai da rana d'aya, kullum burina shine nima naga tana kula dani tamkar yanda take muku, Alhamdulillahi na samu cikar burina a wajen ta, me kuma tai min yanzu? sam ni ban riketa a zuciya ta ba..."
" Duk mun fahimci haka ANTY burinmu a yanzu shine ki furta da bakin ki!.."
" Furtawa ta kawai kuke da bukata?.."
" Eh!.."
Tunda mukayi haka da ANTY ta shige daki, shiru taki fitowa gashi yamma har ta doso kai, ko abinci safe bata ciba wanda na ajiye mata ma yana wajen baa taba shi ba, na shiga damuwa sosai amma sai na d'aure na dauka ko barci take, ranar girkin ta ne mu mukayi komai har Kawu na ya dawo ANTY bata fito ba, babu irin bugun da baayi mata ba amma shiru babu amsa, tuni cikin mu ya gama kulewa tun Kawu na d'aukar abin wasa har yazo ya zarce tunanin sa, duk wata dabara anayi amma shiru Anty taki bude k'ofar room din ta, a ranar kowa haka ya kwana da tararabi a zuciyar sa amma shiru babu alamar zata bude sabida tashin hankali gaba d'aya a falon muka kwana, cikin dare kuwa muka daura da buga kofar ko Allah zaisa ta bude MAN ne yayi mana k'ok'ari wajen kirana masu irin wannan harkar aka zo aka bude k'ofar, sama bata cikin dakin mamaki da alajab'i ya kama jama'a da dama, kowa yana jimammi kamar ance na tura bayin ta, Ina turawa naji kofar tarike gam na sake turawa da k'arfi a hankali ta bude amma mutun bazai iya shiga ba, MAN ne ya taimaka min har muka bude gaba d'aya kwance take a wajen cikin mutu'kar galabaita fuskar ta ya yamushe, da dukan alama cikin ruwa ta shiga domin gashi nan jikin ta ya nuna hakan, na makyale a waje daya cikin azabar razana idanuna a waje...
Kawu ya matso da sauri ganin yanda muke mane a jikin bango dan tsoro, bai ce mana kalla ba illa daukar matarsa da yayi ya fice a bayin, sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya game da firta "" ANTY!..." Hankalina a tashe...
Kafar ta ya shiga murzawa a gagauce, ganin abinda yake nima na kama hannun ta ina hawaye ina murzawa, Bishira ta rik'e d'aya hannun inda fiddusi ta kama k'afa daya, dan danan hannuwan mu suka dauke zafi, bango ne kwato MAN ya dauko ya shinfida mata shi a jikin ta, gaba d'aya waje muka fito Kawu ya cire mata kayan dake jikin ta ya saka mata wani masu nauyin, kafin mu shiga doctor yazo tare da kayan aikin sa, d'aga shi sai Kawu a d'aki aka bari basu dauki lokaci me tsaho ba doctor ya fito ya wuce abin sa, zaune muka tarar da Kawu ya daura hannu a kan ga ANTY dake kwance a gefe tamkar mataciya, cikin sauri na Isa gaban shi har rigi rigin tambayar sa muke " ABBA me doctor yace!.??..."
Yana dagowa na hangin wasu hawaye masu mutu'kar gigita tunani na shirin zubo mai, nayi saurin yin kasa da kaina gaba na yana tsanenta fad'uwa, a hankali ya mik'e game da cewa" a yanzu addu'ar ku take buk'ata ba kuka ba yarana!..." Gaba d'aya kallon shi muke cikin hautsinewar tunani...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce

YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.