Chapter 41

42 2 2
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿4⃣1⃣

" Eh nayi ƙusƙure na amince ni nayi ƙusƙure, amma me yasa zai mun haka? dama duk karya ce?..." A haka ANTY ta same ni, har zuciyata tanaji tausayi na kamar bala'i, amma ta ɗaure cikin ɗaure fuska tace" MUNIBBAT me kikeyi a nan ke kaɗai, tashi ki koma ciki..."

" A'A ba inda zani! sai kin gaya mun gaskia kema ba so na kike ba ko?..."

Harɗe hannuwan ta tayi a ƙirjin  tana kallo na, fuska ta babu alamar wasa..

Nace" Eh ya faɗa mun ni mayya ce da gaske ni din mayya ce ANTY?  ni nayi komai ne domin aminiya ta, amma me saya baza ku fahimceni ba?  bashi kaɗai  ba nima ina haukar san shi amma ANNU ya gaya min duk   *baso bane cuta ce*  sau biyu kenan a gaba ki ana cewa ni matsiya ce babu abinda kikayi a  kai! yace bai taɓ'a so na ba, ya tsane ni baya ƙ'aunar gani na, me yasa kuka rabani da Kawu na?  MAN a gaban ku yace ya rabu dani kuma kun san karya yake amma bakuce komai ba, kema kin ɗaina kulani kin ɗaina mun dariya, na rabu da ganin ki na wani lokaci, to wai me na tsare muku ne? na yarda na amince a yanzu ni *banyi dace ba* eh zan komai inda na fito na gaji!..."

" Kin gama? shikenan abinda ke bakin ki? dan dai ƴar wanna maganar? tsaya ma kafin shi ya furta waya fara furtawa? gara shi ɗan uwan sa ya barwa ba kamar ke da kika raina soyayya sa ba kika bawa ƙawarki!  duk abinda zaki ce kin jima baki ce ba, wawuyar yarinyar kawai..."  tana ida zance ta wuce abin ta...

" Na shiga uku, ya zanyi ne wai? ina zan kama ne?..."

Na sake faɗuwa a wajen ina kuka, da sauri ANTY ta karasa barin falon gudun kar zuciyar ta karaya...

Shi kuwa ANNU cikin mutuƙar farin ciki ya bar falon, kai tsaye gidan su Hafsat ya nufa...

ANTY tana shiga daki ANNU ta fara kira, kamar zata tashi sama amma a banza yaƙi ɗauka,  gajiya tayi ta haƙura...

Shi kam yana kallon Kiran ta yaƙi ɗagawa, ƙarshe ma ya ƙashe wayar gaba ɗ'aya...

Nima na ƙauracewa kowa, bana hira da kowa tsakani da su sai gaisuwa, abinci ma sai naji yunwa zata ƙasheni nake ci...

To matsala kam tsakani na da ANNU kullum cikin jifana yake da kalamai masu zafi da ƙaushi, in nayi magana na sha mari...

MAN gaba ɗaya ya ɓace a gidan, tunda aka sallamo sa ya rabu da zaman gida, kullum yana yawo wuraran shaƙatawa ko hankalin sa zai ƙwanta, baya bari mu haɗu dashi ko kaɗ'ai, amma duk ƙwanan duniya sai ya gani hankalin sa yake kwanciya, video call suke da ANTY cikin wayo da dabara take haskeni ya gani ta kashe wayar ta...


To yau iskacin sa yafi na kullum, ya mayar dani wata ƴar aiki komai yake so sai yace ni, cikin gadara yace na haɗo mai coffee, ban kawo komai a raina ba na miƙe, ko da na haɗa sai na tafi ɗaki na, gaba ɗaya sai na sha'afa da abinda ya sani, sai zuwa can na tuno yama gama hucewa,  cikin sauri na ɗauka jikina yana rawa na taho falon, coffee na gani a hannun sa yana sha, gabana ya faɗ'i na ɗaure, nace" yallaɓ'e gashi!.." kamar yanda ya ingaya min kar nake ce masa Yaya domin yafi ƙarfi na...

Ajiye na hannun sa yayi, da yake dan bala'i ne sai yace" matso dashi to!..."

Jikina har rawa yake wajen miƙo mai, ƙ'arewa coffee din kallo yayi yaga yana ta turiri, hankalin sa ƙwance yace" me kike tsayayi har kawo wannan lokacin?..."

" Kayi haƙ'uri mantawa nayi!.." cikin rawar murya nayi maganar domin har ga Allah yanzu tsoran sa nake kamar raina...

" Daga yau bazan sake sakaki aiki ki manta ba..."

Na dago da sauri, lokacin MAN ya kawo kai zai shigo, Daddah ta fito kallo ita ma, ANNUWAR ya daga cop din tae din dake turiri ya watsa mun a fuska, wani irin zugi da radadi ne ya ratsani na saki wata kara me hawa kai..."

Daddah ta zaro ido waje, cikin mutuƙar razani, MAN yayi wata muguwar sufa cikin kaɗ'uwa, ya damƙeni a jikin sa baiyi wani jinkiri ba, wajen cire rigar sa ya shiga goge mun fuska, hankali a tashe...

ANNUWAR ko a jikin sa, sai ma wani yauki yake yana kara batsewa...

Gaba ɗ'aya MAN ya gama haukacewa, yama rasa wanna irin taimako zai bani,  ruwa me sanyi Daddah ta miƙo me aiko ya shiga danna min a fuska ta, yana ta jera mun sannu, jina da nayi a jikin sa hakan ba ƙaramin daɗi yayi min ba, zuciya tayi sanyi na nemin ciwon narasa, sai kukan shagwaɓa da nake fitarwa a hankali, ga wani ruwan sanyi da yake danna mun a face din ya haɗ'u ya sake bada wata ma'ana daban...

A hankali ya furta""" _MUNIBBAT! bude idon ki na gani! kalle ni nan! ya ɗaina mike zafi! kalle ni Mana._.." cikin wani salo yake maganar..

Aiko na sake narƙewa, cikin kuka da turo baki na nuna gefen fuska ta ina kuka kasa-kasa...

Yana taɓawa nayi saurin cewa" Ashe!!.." alamar zafi, shima yamutsa fuska cike da tausayi na, ji yake tamkar ya cire ciwon ya dawo kan shi, wani irin so mukewa junan mu me ma'ana, wata irin soyayyatace take fuzgar sa, a hankali ya miƙ'e zai wuce nayi saurin riƙo hannun sa, ya juyo a fusce, na buɗe ido na a hankali da sukayi jajir nace" _ILOVE YOU SO MUCH HUBBY..._"

DA SAURI YA KAWAR DA KAN SHI GEFE...

COMMENTS

AND

SHARED

PLEASE

MRS ABUBAKAR CE

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum